Jump to content

Al-Shifa' bint Abdullah

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Al-Shifa' bint 'Abd Allāh ( Larabci: الشفاء بنت عبد الله‎ ), wanda aka ba sunanta Laylā, sahabi ne na annabin musulunci Muhammad .

Tarihin Rayuwarta

[gyara sashe | gyara masomin]

Ita ce 'yar Abdullahi bn Abdulshams da Fatima bint Wahb [1] kuma 'yar gidan Adi ta Kuraishawa ce a Makka . [2] Ta auri Abu Hathma bn Huzaifa, suka haifi ‘ya’ya biyu, Sulaiman da Masruq. [1]

Ta yi suna a matsayin mace mai hankali. Sunanta Al-Shifaa yana nufin "Mai warkarwa," yana nuna cewa ta yiwa jama'a maganin damuwa da dama. [3] A daidai lokacin da mutane ashirin a Makka suke iya karanta-rubutunta, Al-Shifaa ita ce mace ta farko da ta samu wannan fasahar. [2] Ta koya wa wasu da yawa, [4] ciki har da, danginta, Hafsa bint Umar, da wasu mata biyu sun kasance abokai. [5]

Al-Shifaa ta musulunta a Makka kuma tana cikin wanda suka fara yin hijira zuwa Madina . [1] [6] Anan ta sami gida tsakanin masallaci da kasuwar madina. [7] Muhammad ya ziyarce ta a can kuma a wasu lokuta yana tuntubar ta game da mafi kyawun ayyuka a cikin harkokin kasuwancinta. [3]

An ruwaito cewa, lokacin da Umar ya zama khalifa, wani lokaci yakan yi shawara da ita kan wasu al’amura na kasuwanci. Amma wannan ruwayar ba ta tabbata daga ingantattun madogara ba. [3] Ta tuno da shi: “Lokacin da Umar ya yi magana sai ya yi surutu, idan yana tafiya sai ya yi sauri, idan ya buge sai ya ji ciwo. [8] Shima yakan kai mata ziyara a gidanta. [6] A wani lokaci ya tambayi dalilin da ya sa danta Sulaiman ya bace daga sallar asuba; Ta amsa da cewa Sulaiman ya kwana yana sallah, ya bar barci da safe. [7]

Daga cikin hadisin da ta ruwaito akwai asalin sunan Umar, Amirul Muminina [6] da kuma maganganun Muhammad: “’Misalin jarumin jihadi a tafarkin Allah, kamar wanda ya yi azumi, ya yi sallah, batareda wata tsoro ko shakkah ba. Akan kar adaina azumi ko sallah har sai jarumin jihadi ya dawo”. [9]

Danta Masruq ya zama sarki . [1] Danta sulaiman ya haifi yara biyu Abubakar da Uthman, wadanda suma maruwaitan hadisi ne. [7] [3]

  1. 1.0 1.1 1.2 1.3 Muhammad ibn Saad. Kitab al-Tabaqat al-Kabir vol. 8. Translated by Bewley, A. (1995). The Women of Madina, p. 188. London: Ta-Ha Publishers.
  2. 2.0 2.1 Ahmed ibn Jabir al-Baladhuri. Kitab Futuh al-Buldan. Translated by Murgotten, F. C. (1924). The Origins of the Islamic State Volume II, p. 271. New York: Longmans, Green & Co., & London: P. S. King & Son.
  3. 3.0 3.1 3.2 3.3 Ahmad ibn Hajar al-Asqalani. Al-Isaba fi Tamyiz al-Sahaba vol. 7 #11373.
  4. Kazan, H., Dünden bugüne hanım hattatlar, [Women Calligraphers: Past and Present], İstanbul Büyükşehir Belediyesi, 2010, Chapter 5
  5. Abu Dawud 28:3878.
  6. 6.0 6.1 6.2 Bukhari, Al-Adab Al-Mufrad 42:1023.
  7. 7.0 7.1 7.2 Malik ibn Anas. Al-Muwatta 8:7.
  8. Muhammad ibn Jarir al-Tabari. Tarikh al-Rusul wa'l-Muluk. Translated by Smith, G. R. (1994). Volume 14: The Conquest of Iran, p. 120. Albany: State University of New York Press.
  9. Tirmidhi 3:20:1619.