Umar Ibn Al-Khattab

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Simpleicons Interface user-outline.svg Umar Ibn Al-Khattab
Abu bakr2.jpg
Khalifofi shiryayyu

22 ga Augusta, 634 - 3 Nuwamba, 644
Sayyadina Abubakar - Sayyadina Usman dan Affan
Rayuwa
Haihuwa Makkah, 585 (Gregorian)
ƙasa Khulafa'hur-Rashidun
ƙungiyar ƙabila Larabawa
Mutuwa Madinah, 3 Nuwamba, 644
Makwanci Masallacin Annabi
Yanayin mutuwa kisan kai (stab wound (en) Fassara)
Killed by Abu Lu'lu'a Firuz (en) Fassara
Yan'uwa
Mahaifi Khattab Ibn. Nufayl
Mahaifiya Hàntama bint Hixam
Abokiyar zama Umm Kulthum bint Ali ibn Abi Talib (en) Fassara
Atika bint Zayd (en) Fassara
Umm Kulthum bint Asim (en) Fassara
Yara
Siblings Zayd ibn al-Khattab (en) Fassara da Fatimah bint al-Khattab (en) Fassara
Karatu
Harsuna Larabci
Sana'a
Sana'a statesperson (en) Fassara, caliph (en) Fassara, Liman, shugaban addini da Sahabi
Aikin soja
Ya faɗaci Badar
Yaƙin Uhudu
Yaƙin gwalalo
Yaƙin Khaybar
Imani
Addini Musulunci
Signature Believed To Be Of ʿUmar B. Al-Khaṭṭāb.png

Umar, ko kuma Omar a Larabci kuma عمربن الخطاب Umar dan Al'Khattab hausa Umaru dan Kaddabi Allah ya kara yarda da shi.

Daya ne daga cikin manyan Sahabban Annabi Muhammad (s.a.w), kuma shine na biyu cikin halifofin Musulunci. Yana daya daga cikin Halifofinnan guda Hudu na Halifancin Annabta, sannan kuma yana daya daga cikin sahabbai goman da Annabi yayima bushara da Aljanna tun suna Duniya. Umar ya kasan ce mai taka tsantsan tare da gudun duniya, kasancewar sa mutumin da yayi kaurin suna kwarai wajen rarrabewa tsakanin gaskiya da karya ne yasa akayi masa lakabi da Al'faruk, ma'ana mai raba karya da gaskiya. Umar ya kasance babban jagora, kuma dukkannin hadisai ruwayar shi ana kallonsu a matsayin hadisai ingantattu.

Farkon rayuwar sa[gyara sashe | Gyara masomin]

An haifi Sayyiduna Umar a birnin Makka daga kabilar Banu Adiy. Mahaifinsa Al'Kattab ibn Nufayl mahaifiyar sa itace Hantama bintu Hisham, yar kabilar Banu Makhzun. A lokacin kuruciyar sa, Umar ya kasance yana taya mahaifin sa kula da rakuman sa.

Tun a lokacin kuruciyar sa Sayyiduna Umar ya kasance mai sha'awar koyon rubutu da karatu. Hakane yasa ya samu kwarewa wajen iya rubutu da karatu, harma ya zama gagara-badau wajen iya rubuta wake-wake kamar yadda larabawa suka shahara wajen rubuce-rubuce na wake-wake a zamanin kafin zuwan Musulunci. Ana danganta Basirar Umar da gado daga wajen Mahaifin sa watau Wanda ya haifeshi.

Hakanan dai a zamanin kuruciyar Sayyadina Umar, ya zama babban dan kaauwa inda yake zuwa kasashen Romaniya da Farisa fatauci. Sai dai harkar kasuwancin bata karbe shiba sosai kamar sauran takwarorin sa.

Zamanin Annabi Muhammad (s.a.w)[gyara sashe | Gyara masomin]

Takobin Sayyadina Umar

Kafin Musuluntar sa[gyara sashe | Gyara masomin]

A shekara ta 601M. Annabi Muhammad (s.a.w) ya fara kira zuwa ga musulunci, kamar sauran mutanen makkah shima Umar bai bayar da gaskiya ga Annabi ba da farko. Harma ya kasance babban mai adawa da Annabi (s.a.w). Sakamakon takurawar da Umar da sauran kafiran makkah na lokacin sukema Annabi da wadanda suka musulunta ne yasa Annabi (s.a.w) ya umarci wasu daga cikin musulmai da suyi hijirah daga makkah zuwa kasar Sham. Lokacin da sahabbai sukabi Umarnin Annabi (s.a.w) ne sai ganin haka ya kara tayar da hankalin Sayyadina Umar harma ya fara shirye shiryan kashe Annabi Muhammad (s.a.w).

Musuluntar Sayyadina Umar[gyara sashe | Gyara masomin]

Umar ya shiga musulunci ne a shekarar 616 Miladiya. wato shekara daya kenan bayan hijirar Musulmai zuwa Sham. Ibn Ishak, yayi rubutu a lattafin sirar shi game da Musuluntar Sayyadina Umar.

Ga tarihin Daga gidan ‘yan- uwansa, yasame shi ta matarsa suna karatun Alqurani, sai yaji da kunnebsa alhali baisan sun muslumta ba, sai yayi fushi mai tsanani har yakaiga ya bugi dan uwan nasa, matar dan uwan nasa tace Ashhadu an laa ilaha illallahu wa anna Muhammadan Rasulullahi, sai jikin yayi sanyi, sai umar ya umurceta da bashi pallen kuranin yagani, sai ta bashi ya karanta ayoyin qurani, sai yace don wannan Kuraishu suke azabtar da mutane? kai tsaye ya wuce zuwa Darul-Arqam da ke karqashin dutsen Safa wanda kuma nan Manzon Allah (s.a.w) ya samu mafaka. Da isar Sayyadina Umar (r.a) wannan gida sai ya kwankwasa kofa. “ Sai mai gadin Gidan yace Wanene yake kwanKwasa kofar?” Sayyadina Umar ya amsa da “Umar ne”. . Da mai gadin ya leko ya gan shi da takobi zare, sai ya yi shakkar bude kofar. . Sai Sayyadina Hamza (r.a) ya ce da shi, “Bude masa idan da alheri ya zo muna maraba da shi idan kuma da akasin haka ya zo ai sarkin yawa ya fi sarkin karfi”. . Aka bude masa ya shiga, Da shigarsa sai Sayyadina Hamza (r.a) ya dakume shi ya ce da shi “Umar, me ke tafe da kai?” . Sauran Musulmi kuma suka zazzare takubbansu suka yi masa kawanya (suka zagayeshi) da zimmar ko da zai tada jijiyar wuya sai su cimmasa. . Da jin wannan hayaniya sai Manzon Allah (s.a.w) ya fito daga dakinsa ya ce da Sayyadina Hamza (r.a) “kyale shi ya karaso gare ni”. . Da Sayyadina Umar (r.a) ya kusanci Manzon Allah (s.a.w) sai Manzan Allah (s.a.w) ya ce da shi “Wane irin lokaci za ka dauka kana fada da Musulunci? Har yanzu lokacin da za ka karbi Addinin gaskiya bai yi ba?” , Sai Sayyadina Umar (r.a) ya ce: “Hakika lokacin da zan karbi Addinin gaskiya ya yi. Na zo ne na yi imani”. . Sai Manzan Allah (s.a.w) ya mikar da hannunsa shi kuma Sayyadina Umar (r.a) ya dora nasa a kan Na Manzan Allah (s.a.w) cikin ladabi sannan ya ce “Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Muhammadu Manzon Allah ne”.

Da jin haka sai Musulmi suka ce “Allahu Akbar” cikin jin dadi. Sai Manzan Allah (s.a.w) ya rungume shi, sannan sauran Musulmi ma suka rika rugumarsa daya bayan daya.

Sayyadina Umar (r.a) shi ne na arba’in (40) a shiga Musulunci. A wannan ranar da Sayyadina Umar ya Musulunta har Mala’ika Jibrilu (a.s) sai da ya taya Manzan Allah (s.a.w) murna saboda musuluntar sayyadina Umar (r.a). Ya ce da shi, “Ya Manzan Allah jama’ar Aljanna suna murna da musuluntar Umar (r.a) kuma suna mika sakon taya murna gareka”.

Sayyadina Umar (r.a) Saboda tsananin jin dadin musuluntar da ya yi saida ya rika bi kwararo-kwararosako-sako a Makkah yana shelanta Musuluntar sa.

Hijirar Sayyadina Umar[gyara sashe | Gyara masomin]

Sakamakon tsanani yayi yawa daga wajen kafiran Makkah ne sai Annabi Muhammad(s.a.w) ya umarci sahabbai da suyi hijira zuwa birnin da ake kira Yathriba a wancan lokacin wanda daga bisani aka mayar dashi Madinah. Sai sahabbai suka runka bin dare suna sulalewa daga garin Makkah saboda gudun cutarwa daga kafiran Makka na wancan lokacin. Amma shi Sayyadina Umar a fili kuma da rana tsaka yayi tasa hijirar har ma yana fadin Ina wanda yake son matar sa ta zama bazawara ko yayansa su zama marayu? to ya zo ya hana ni Umar yai hijirar sa tare da rakiyar dan dan'uwan sa da kuma dan'uwansa Sa'id dan Zaidu

Rayuwar sa a Madina[gyara sashe | Gyara masomin]

A Madinah kuwa, Umar (R.A) na daya daga cikin zaratan mayaka wadanda su kayi ruwa da tsaki wajen kare martabar Addinin Musulunci da ruguza abokan gaba wato Kafirai. Ya kusanci Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama har ya kai matsayin wazirinsa na biyu. A shekara ta uku bayan hijira sai Allah ya karrama shi da surukuta da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama inda Manzo ya nemi auren 'yarsa Hafsah, aka ba shi ita, aka daura aure, sai ta zama ita ce ta uku daga cikin matansa bayan rasuwar uwargidansa Khadijah. A wurare da dama Umar (R.A) ya dace da hukuncin Alkur'ani kafin saukarsa. Misali, Umar ne ya ba da shawarar kada Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya halarci sallar jana'iza a kan munafukai, kuma sai AlKur'ani ya sauka da aya da tai daidai da wannan hukuncin. Haka kuma Umar (R.A) ya bai wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama shawarar ya hana mutane shiga gidansa, kuma Allah ya saukar da wahayi a kan haka. Shi ne kuma ya nemi a shamakance mata daga maza ta hanyar amfani da hijabi, sai Allah ya saukar da wahayi a kan haka. Ya bada shawarar a kashe fursunonin yaqin Badar, Allah ya karfafi ra'ayinsa a Suratul Ali Imran. Wadannan duka suna nuna irin kaifin basirarsa da kusancinsa ga Allah da sanin abin da Allah yake so da wanda ba ya so.

Khalifancin Sayyadina Umar (r.a)[gyara sashe | Gyara masomin]

Taswirar daular Musulunci a zamanin Kalifancin Sayyadina Umar R.A

Sayyadina Abubakar (R.A) say ya ayyana wa Musulmi Umar a matsayin wanda zai gaje shi bisa ga shawararsu. Don haka da Abubakar ya cika nan take mutane su kayi masa mubaya'a kuma ya kama aiki. Wani muhimmin abinda ya kamata a sani game da khalifancin Umar (R.A) shi ne kwarjinin da yake da shi matuka a idon jama'a. Amma kuma duk da haka talakawa sun more a lokacin khalifancinsa, domin kuwa ya kasance yana kula da al'amuransu ta ko wane fanni. Bayan dai kulawarsa da tsayuwar addini. Umar (R.A) yana kulawa da jin dadin rayuwar jama'a da inganta lafiyarsu da gyaruwar tattalin arzikinsu da samun kwanciyar hankali da zaman lafiya a tsakaninsu.

Irin kwarjinin da Umar (R.A) yake da shi a zukatan jama'a ya sanya wata mata ta yi barin cikinta a lokacin da ta samu labarin an kai kararta ga Sarkin Musulmi Umar. Wannan ya sanya Umar ya tara jama'a ya nemi shawararsu a kan wannan abinda ya faru don sanin ko diyya ta wajaba a kansa. Ya kuma yi aiki da ra'ayin Sayyadina Ali (R.A) na biyan diyyar jinjirin da aka rasa. Ba za mu yi mamakin wannan mata ba idan muka san cewa, manyan Sahabbai irin su Zubairu dan Awwam da Sa'adu dan Abu Waqqas sukan tafi wajen Umar da nufin gaya masa wata magana ko gabatar da wata bukata, amma su je su dawo ba su samu damar yin haka ba saboda kwarjininsa da ya cika masu fuska. Ibnu Abbas ma duk da irin kusancin da yake da shi ga Umar amma ya yi shekara daya yana son ya tambaye shi game da wata aya bai samu damar haka ba saboda kwarjininsa.

Wani wanzami kuma ya saki iska saboda tsoro a lokacin da Sarkin Musulmi Umar ya yi tari shi kuma yana yi masa aski. Umar (R.A) da kansa ya kan damu wani lokaci da yadda jama'a suke fargabarsa, har ma ya kan ce, Ya Allah! Ka san na fi tsoronka fiye da yadda su ke tsorona.

A game da kulawarsa da talakawa kuwa, Umar (R.A) ya shahara da ziyarar sa ido wadda yake yi a cikin dare yana sintiri a tsakanin hanyoyi da gidaje don sanin halin da kasarsa ta ke ciki. A cikin irin wannan ziyarar ne yake gano idan akwai barayi ko wasu miyagu ko mabarnata masu fakewa a cikin duhun dare su yi aikin assha watau aikin masha'a, ko kuma bako wanda bai samu masauki ba.

Kisan Sayyadina Umar (r.a)[gyara sashe | Gyara masomin]

Makwancin Kalifa Umar a masallacin Annabi (s.a.w) Madina. Tagar farko daga dama tana nuna Kabarin Sa

A shekarar 144M. ne wani bawa bafarenshe maisuna Abu Lu'u lu'ul majusi ya kai hari kan Sayyaduna Umar (r.a). Dama ansha shirya kashe Umar watanni kafin aiwatar da kisan. Adaidai lokacin da Sayyaduna Umar yake jagorancin sallar Asuba ne maharin yazo da wuka ya daddabawa Sayyaduna Umar (r.a) har sau shida nakarshe ne ya daba masa ita a makogwaron sa. A kokarin sauran mutanen na ganin aun kama maharin Lu'u Lu'u ne sai da ya raunata mutum goma sha biyu(12) . Daga baya shida ko tara na mutanen Allah ya karbi rayuwar su dalilin wannan raunin. Shima Lulu daga bisani kashe kansa. Sayyadina Umar ya rasu sakamakon raunukan da maharin wato Lu'u Lu'u (l.a) yayi masa bayan kwana uku. Wato ranar Laraba ta 26 ga watan Dhul Hijja shekara ta 23 bayan hijira. Da Umarnin Aisha ne aka binne mahaifin ta wato Sayyaduna Umar bin khatdab a cikin dakinta gefe kadan da Makwancin Annabi Muhammad (s.a.w) da kuma na Sayyadina Abubakar(r.a).

Iyalin Sayyadina Umar (r.a)[gyara sashe | Gyara masomin]

Sayyadina Umar(A.S) Ya auri mata Tara ne a iya rayuwar sa. Yana da yaya goma sha hudu, goma maza hudu mata.