Quraiba bint Abi Umayya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Quraiba bint Abi Umayya
Rayuwa
Haihuwa Hijaz
ƙasa Makkah
Ƴan uwa
Mahaifi Abu Umayya ibn Al-Mughira
Abokiyar zama Sayyadina Umar  628)
Abdul-Rahman dan Abu Bakr
Mu'awiya  (630 -
Ahali Q12223444 Fassara, Q106926120 Fassara, Q106927513 Fassara, Q106881635 Fassara, Ummu Salama da Al-Muhajir ibn Abi Umayya (en) Fassara
Yare Banu Makhzum (en) Fassara
Sana'a
Imani
Addini Musulunci

Quraiba "Ƙarama" bint Abi Umayya, sahabiyar Annabi Muhammad, (S A W) kuma ta kasance, matar khalifa Umar na biyu daga baya kuma khalifa Umayyawa na farko wato Mu'awiya.

Tarihin Rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Iyali[gyara sashe | gyara masomin]

Babanta, Abu Umayya ibn al-Mughira, [1] :184shi ne sarkin Makka a farkon karni na bakwai. [2] Mahaifiyarta ita ce Atika bint Utba, 'yar gidan Abdshams ta Kuraishawa. Don haka Hind bint Utba ta kasance kanwar mahaifiyarta [1] :165,184yayin da Ummu Salama ta kasance kanwar mahaifinta. [3]

Auren farko[gyara sashe | gyara masomin]

Ta auri Umar kafin shekara ta 616. :510[4] :92A lokaci guda Umar ya auri Zainab bint Maz'un da Ummu Kulthum bint Jarwal, wadda ta haifi 'ya'ya biyar a tsakanin su, alhali kuwa Quraiba ba ta haihu ba. :203–204

Umar ya musulunta a shekara ta 616. :207Dukan iyali sun yi hijira zuwa Madina a shekara ta 622, :218duk da cewa Ummu Kulthum da Kuraiba sun kasance mushrikai. :510[5] An ambaci Quarayba a taqaice a Madina a wani waki’a da ta taimaka wajen kula da jaririn ‘yar uwarta Ummu Salama. :66

Ba da dadewa ba bayan yarjejeniyar Hudabiya a shekara ta 628, Annabi Muhammad ( صلى الله عليه و سلم ) ya ba da sanarwar wahayi cewa an umurci musulmi da cewa kada su riqe igiyoyin mata mushrikai. Don haka sai Umar ya saki Ummu Kulthum da Quraiba, kuma dukkansu suka koma Makka.

Aure Na Biyu[gyara sashe | gyara masomin]

Sai Kuraiba ta auri dan uwanta Mu'awiya bn Abi Sufyan " alhalin su biyun suna mushrikai " wato kafin Janairu 630. [5] [4] :92Sai dai kuma Mu'awiya na sake ta. Amma Quraiba ta haifi 'ya'ya mata 3 tare da Mu'awiya, Ummu Hakim, Ummu Sa'id da Ummu Habib.

Aure na uku[gyara sashe | gyara masomin]

Daga baya kuma Abdulrahman bn Abi Bakr ya aure ta. Aisha ta yi sulhu da yayanta, dangin Makhzum suka amince da wasan. [6] Abd al-Rahman da Qurayba sun haifi 'ya'ya uku: Abd Allah, Umm Hakim, Asma, Muhammad da Hafsa.

Abd al-Rahman ya yi kaurin suna da “wajen tsaurarawa” mata, kuma dangin Makhzum sun nuna rashin amincewarsu da mu’amalarsa da Quraiba. Sun yi iƙirarin cewa sun ba da ta ne kawai saboda Nana Aisha Allah ya ƙara yarda da ita, wacce ta daidaita su da ɗan'uwanta. Watarana Quraiba ta ce: “An gargaɗe ni game da kai! sai Abdurrahman ya amsa da cewa: "Ni zan sake ki in kina so." Sai ta canza ra’ayinta ta ce: “Ba zan fifita kowa a kan ɗan Abubakar Allah ya ƙara yarda da shi ba. Suka zauna tare. [6] [1] :184

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 1.2 Muhammad ibn Saad. Kitab al-Tabaqat al-Kabir vol. 8. Translated by Bewley, A. (1995). The Women of Madina. London: Ta-Ha Publications.
  2. Guillaume, A. (1960). New Light on the Life of Muhammad, p. 24. Manchester: Manchester University Press.
  3. Muhammad ibn Jarir al-Tabari. Tarikh al-Rusul wa'l-Muluk. Translated by Landau-Tasseron, E. (1998). Volume 39: Biographies of the Prophet's Companions and Their Successors, pp. 80, 175. Albany: State University of New York Press.
  4. 4.0 4.1 Muhammad ibn Jarir al-Tabari. Tarikh al-Rusul wa'l-Muluk. Translated by Fishbein, M. (1997). Volume 8: The Victory of Islam. Albany: State University of New York Press.
  5. 5.0 5.1 Bukhari 3:50:891.
  6. 6.0 6.1 Malik ibn Anas. Al-Muwatta 29:14.