Jump to content

Alakar Najeriya da Rasha

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Alakar Najeriya da Rasha
alakar kasashen biyu
Bayanai
Ƙasa Rasha da Najeriya
Lokacin farawa 25 Nuwamba, 1960
Wuri

Samfuri:Infobox Bilateral relationsAlaƙar Najeriya-Rasha ( Russian: Российско-нигерийские отношения ) shine dangantakar kasashen waje da ke tsakanin kasashen guda biyu, Najeriya da Rasha . Rasha tana da kuma ofishin jakadancinta a Birnin Legas da ofishin wakilci a Birnin Abuja, kuma Najeriya na da ofishin jakadancinta a Moscow. Jakadan Rasha a Najeriya na yanzu shi ne Alexey Shebarshin.

Dmitry Medvedev a Najeriya a shekara ta 2009.

An kafa dangantakar diflomasiyya tsakanin Najeriya da Tarayyar Soviet a ranar 25 ga Nuwamban shekara ta 1960. A lokacin yakin basasar Najeriya tsakanin 1967 zuwa 1970, USSR ta baiwa gwamnatin Najeriya taimakon siyasa da soja. Najeriya da sabuwar Tarayyar Rasha sun kafa dangantakar diflomasiyya a shekara ta 1991.[ana buƙatar hujja] A watan Maris na 2001, Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya ziyarci Moscow. A lokacin wannan ziyarar Vladimir Putin, da Olusegun Obasanjo sun sanya hannu kan sanarwar "Kan Ka'idodin Hulda da Abokai da Kawance Tsakanin Tarayyar Rasha da Tarayyar Najeriya", da kuma shirin hadin gwiwa a tsarin kasashen biyu da na duniya tsakanin Rasha da Najeriya. A ranar 24 ga Yunin, shekara ta 2009 Shugaban Rasha Dmitry Medvedev ya kawo ziyarar aiki a Nijeriya a wani bangare na rangadin wasu kasashe guda 3 na Afirka . Ita ce ziyarar farko da wani shugaban Rasha ya kawo Najeriya. [1] [2]

A shekara ta 2017, Rasha da Najeriya sun sanya hannu kan wata yarjejeniya kan hadin gwiwar sojoji. Najeriya na sha'awar sayen kayan aikin sojan Rasha. Najeriya ta riga ta sanya hannu kan yarjejeniyar sayen jirage masu saukar ungulu samfurin Mi-35, wadanda tuni aka kawo shida daga cikinsu.

A watan Disamba na 2023, Rasha da Nijar za su rattaba hannu kan takardar fahimtar juna a wani bangare na karfafa hadin gwiwar soja tsakanin Jamhuriyar Nijar da Tarayyar Rasha.[3]

  • Jerin jakadun Rasha a Najeriya.

Hanyoyin haɗin waje

[gyara sashe | gyara masomin]