Alia Sabur

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Alia Sabur
Rayuwa
Haihuwa New York, 22 ga Faburairu, 1989 (35 shekaru)
ƙasa Tarayyar Amurka
Karatu
Makaranta Drexel University (en) Fassara
Stony Brook University (en) Fassara
Sana'a
Sana'a masanin lissafi, injiniya da taekwondo athlete (en) Fassara
Employers Konkuk University (en) Fassara
Imani
Addini Musulunci

Alia Sabur (an haifeta ranar 22 ga watan Fabrairu, 1989) ƙwararriyar masaniniyar Materials science ce ƴar Amurka. Tana riƙe da tarihin wacce ta zama Farfesa mafi ƙanƙanta a duniya. [1]

Rayuwar farko da ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Sabur a birnin New York, New York. Mahaifiyarta, Julie Sabur (an haifi Kessler), ta yi aiki a matsayin mai kawo rahoto ga News12 Long Island har zuwa 1995. [2] Ta auri Mohammed Sabur, ɗan ƙasar Pakistan, a 1980. [2] Alia, an haifeta 22 ga watan Fabrairu, 1989, akwai alamun baiwa tattare da ita. Ta gwada "off the IQ scale," a cewar wani malami wanda ya gwada ta a matsayin 'yar aji ɗaya. [2] A matsayinta na 'yar aji hudu, ta bar makarantar gwamnati kuma an shigar da ita Jami'ar Stony Brook tana da shekaru 10, daga baya ta kammala karatun summa cum laude tana da shekaru 14. Ta kuma sami kyautar baƙar bel a Tae Kwon Do tana ƴar shekara 9.[3]

Bayan Stony Brook, Sabur ta halarci Jami'ar Drexel, inda ta sami digiri na biyu (M.S.) a shekarar 2006. Alia ta kasance mai karɓar haɗin gwiwar Dean na 2007 daga Jami'ar Drexel.[4] A cikin 2007 ta riƙe wani matsayi na ɗan lokaci a Jami'ar Southern University da ke New Orleans bayan Hurricane Katrina.[5]

Aikin lissafi[gyara sashe | gyara masomin]

A ranar 19 ga watan Fabrairu 2008, tana da shekaru 18 (kwana 3 kafin ranar 19 ga watan zagayowar ranar haihuwar ta), an naɗa ta a matsayin Farfesa ta ƙasa da ƙasa a fannin Cibiyar Bincike tare da Jami'ar Stony Brook ta Dept. of Advanced Technology Fusion a Jami'ar Konkuk a Seoul, South South . Koriya .[ana buƙatar hujja]Matsayin ne, kwangilar shekara guda wanda ta zaɓi ba zata sabunta ba bayan karewar wa'adin farko.[6][7] Littafin Guinness Book of Records ya sanya sunan Sabur a matsayin Farfesa mafi ƙarancin shekaru a duniya, inda ya maye gurbin Farfesa Colin Maclaurin na fannin lissafi a Jami'ar Aberdeen yana da shekaru 19.

Ta fara aiki a sashen (Department of Advanced Technology Fusion) a Jami'ar Konkuk a watan Yuni 2008 kuma ta koma garinsu na New York a farkon shekara ta 2009, ba tare da sabunta kwangilarta ba.[5][7][8]

Deepwater Horizon oil spill[gyara sashe | gyara masomin]

A watan Yuni 2010 Sabur ta bayyana a gidajen telebijin na; CNN da Fox News' Hannity don kwatanta ra'ayinta, wanda kamfanin mai na Birtaniya, BP ya ɗauka a matsayin wani zaɓi don taimakawa wajen rage zubar da man fetur na Deepwater Horizon a yankin Gulf of Mexico.[9][10][11]

Rigima a Graduate school[gyara sashe | gyara masomin]

A cikin shekara ta 2008, Sabur ta shigar da ƙara a kan Jami'ar Drexel, tana mai da'awar cewa jami'ar ta aikata zamba da cin mutunci game da neman digiri na uku da ta ke yi. A cikin ƙarar, Sabur ta tuhumi Yury Gogotsi, tsohuwar Ph.D. mai ba da shawara, ta yi amfani da bincikenta ba daidai ba don neman tallafi, kuma da gangan ta hana ta digiri. An fara shari'ar a ranar 9 ga watan Agusta, 2010.

“Amma a lokacin ne na ƙara ruguza duniyar kimiyya. Na ga munanan hali kuma na gane cewa wasu farfesoshi ba son cigaban kimiyya ne a gaban su ba. Na yi karo da mai ba da shawara wanda ke kula da digirin digir-gir (PhD) dina. Na yi imani mai ba ni shawara ya nemi tallafi da haƙƙin mallaka ta amfani da ra'ayoyina, kuma ya ɗauki bashi a gare su. Ya musanta haka kuma ya zarge ni da satar aikinsa. Duk da cewa jami'a ta wanke ni daga zargin sata, amma har yanzu ta ki ba ni digiri na.", in ji rahoton labarin mujjalar Financial Times.[6] (subscription required)

Wannan ita ce ƙara ta biyu da ta shafi dangin Sabur. A na baya bayan nan iyayen Alia Sabur sun kai ƙara a madadin ƴar su, inda suka yi zargin cewa hukumar ilimi ta Northport – East Northport, da ‘ya’yanta, da kuma gundumar makarantar sun kasa baiwa ƴar su ayyukan da suka dace da ilimi wanda ya saba wa ilimin nakasassu Aiki.[12] Shida daga cikin laifuka bakwai an yi watsi da su.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Youngest Professor - Guinness World Records
  2. 2.0 2.1 2.2 Newsday Long Island - March 9, 1999 - Real Genius: 10-year-old Alia Sabur of Northport tests 'off the IQ scale'[permanent dead link]
  3. Winerip, Michael (2003-01-22). "Reading at 8 Months? That Was Just the Start". The New York Times. Retrieved 2009-05-08.
  4. "MSE Well Represented at Honors Day Ceremony". Archived from the original on 2013-01-19. Retrieved 2013-05-23.
  5. 5.0 5.1 McNeill, David (2008-05-01). "University appoints world's youngest professor". The Independent. Archived from the original on 2008-05-12.
  6. 6.0 6.1 Duguid, Sarah (2010-10-01). "First Person: Alia Sabur". Financial Times Magazine. Archived from the original on 7 October 2010. Retrieved 2010-10-14.
  7. 7.0 7.1 Ahn Hai-ri; Lee Jong-chan; Choe Sun-uk; Lee Jeong-bong (2009-10-24). "Critics denounce expat college hires". Joongang Daily. Retrieved 2009-11-12.
  8. Considine, Bob (2008-04-24). "World's youngest professor can't legally drink". MSNBC. Archived from the original on 25 April 2008. Retrieved 2008-04-25.
  9. Template:Cite episode
  10. Rosenberg, Rebecca (2010-06-04). "LI brainiac offers oil giant a slick fix". New York Post. Retrieved 2010-06-08.
  11. Template:Cite episode[dead link]
  12. "Sabur vs Brosnan, US District Court for the Eastern District of New York, 203 F. Supp. 2d 292 (2002)". NY.Findacase. Archived from the original on 2019-06-20. Retrieved 2011-06-28.

Kara karantawa[gyara sashe | gyara masomin]

Hanyoyin haɗi na waje[gyara sashe | gyara masomin]