Jump to content

Amba Bongo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Amba Bongo
Rayuwa
Haihuwa 21 ga Afirilu, 1962 (62 shekaru)
ƙasa Jamhuriyar dimokuradiyya Kwango
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a marubuci

Amba Bongo (an haife ta a ranar 21 ga Afrilu, 1962) marubuciya ce kuma mai ba da shawara ga 'yan gudun hijira daga Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo-Kinshasa wurin da ta yi karatun Turanci da Al'adun Afirka a l'Institut Supérieur Pédagogique da ke Gombe. Ta kuma yi karatun Ilimin halayyar dan adam a Jami'ar Warocqué da ke Mons, Belgium. [1][2]

Tun daga shekara ta 1994 ta yi aiki a tsakanin tsarin shari'ar Burtaniya kuma ta yi aiki a matsayin darektan furojet na Mata masu aiki, wata kungiya ta 'yan gudun hijira da ke tallafawa mata 'yan gudun hijira da ke magana da Faransanci da Masu neman mafaka da ke neman wurin zama a Ingila. Amba ta rubuta litattafai, waƙoƙi da gajerun labarai kuma a halin yanzu tana zaune a birnin Landan.[1][2]

Littafinta na farko Une femme en exil ( ) an buga shi a shekara ta 2000 kuma L"Harmattan, Paris ce ta wallafa shi. [2]  Labarin game da Anna ne, wacce ta sami aiki a matsayin mai ba da shawara kan ilimi a Jami'ar Kinshasa, amma mambobin jami'an tsaro na jihar sun dauke ta inda ta juri wahalhalu, wulakanci da azabtarwa kafin a kore ta daga kasar London.[1]

Haɗin waje

[gyara sashe | gyara masomin]

Bayanan da aka ambata

[gyara sashe | gyara masomin]
  1. 1.0 1.1 1.2 "Amba Bongo". aflit.arts.uwa.edu.au. Retrieved 2024-03-25. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":0" defined multiple times with different content
  2. 2.0 2.1 2.2 "Amba Bongo | exiled". www.exiledwriters.co.uk (in Turanci). Retrieved 2024-03-25. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":1" defined multiple times with different content