Aminu Abdullahi Shagali
Aminu Abdullahi Shagali | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 13 ga Faburairu, 1980 (44 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Ahmadu Bello |
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Imani | |
Jam'iyar siyasa | All Progressives Congress |
Aminu Abdullahi Shagali shi ne kakakin majalisar wakilan Jihar Kaduna, Najeriya. Ya kasance shahararren dan kasuwa ne shi.
Farkon Rayuwa Da Karatu
[gyara sashe | gyara masomin]Aminu Abdullahi Shagali, an kuma haife shi ne a ranar 13 ga watan Fabrairun shekara ta alif 1980, shi ne yaro na biyar (5) a wurin mahaifinsa Alhaji Abdullahi Shagali kuma daga wurin mahaifiyarsa Hajiya Zulaihat Shagali. Ya yi karatun firamare a Bako Zuntu Nursery and Primary School, da ke Zariya a shekara ta alif (1986–1993), ya yi sakandare a Federal Government College, Daura a jihar Katsina a shekara ta alif (1993–1999), da kuma Kaduna State Polytechnic, Zariya (a yanzu ita ce Nuhu Bamalli Polytechnic) inda ya yi jarabawar Interim Joint Matriculation Board examamination a 2000. Shagali ya karanta Political Science a Jami'ar Usmanu Danfodiyo, da ke Sokoto, da yin master's degree a bangaren public administration a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria a shekara ta 2008. Ya kuma kasance dan kasuwa ne shi gabanin tsundumarsa fagen siyasa a shekarar 2010. Bayan haka kuma ya yi karatun digiri na uku wato (PhD) a bangaren rural development a Jami'ar Bakhtalruda, da ke Sudan.