Aminu Ala
Lua error a mw.lua, layi na 656: invalid value (nil) at index 1 in table for 'concat'. | |
| Rayuwa | |
| Haihuwa | Kano, 11 ga Faburairu, 1973 (53 shekaru) |
| ƙasa | Najeriya |
| Karatu | |
| Harsuna | Hausa |
| Sana'a | |
| Sana'a | mawaƙi |
Aminu Ladan Abubakar, wanda aka fi sani da Alan Waƙa (an haife shi a ranar 11 ga watan Fabrairu, shekara ta 1973), mawaƙin Hausa ne kuma Mawallafin littattafai daga Jihar Kano ta Arewacin Najeriya.[1][2][3]
Fitaccen mawakin Hausa, Aminu Abubakar, wanda aka fi sani da Aminu Ala ya ce hukumar tace fina-finan jihar Kano ba ta da hurumin tace waƙoƙin yabon Annabi. Aminu Ala ya shaida wa BBC Hausa cewa yin hakan daidai yake da "matse tunanin" mawaƙa saboda "ba a tace fasaha". An hana wakokin yabon Annabi a Kano sai da izinin gwamnati[4]
Ridda a Kano: An yanke wa mawaƙi hukuncin kisa bisa yin ɓatanci ga Annabi[5]
A kwanakin baya ne, hukumar tace fina-fanai ta Kano ta ce babu wani sha'iri da zai ƙara fitar da waƙa a jihar, sai ta ba shi lasisi. Shugaban hukumar Isma'il Muhammad Na'abba wanda aka fi sani da Afakallah ne ya bayyana hakan a wata hira da BBC.[6]
Rayuwar farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]Aminu Ala ya kammala karatunsa na firamare a makarantar firamare ta Tudun Murtala tsakanin shekara ta 1980 zuwa 1986, sannan kuma ya wuce GSS Kawaji Secondary School a Dakata Kano daga 1987 zuwa 1992 a 2004. Ya ci gaba da karatunsa a Makarantar Fasaha a Kano inda ya samu difloma a shekarar 2007.[7]
Littattafai
[gyara sashe | gyara masomin]An fara sanin Ala a fagen rubutun harshen Hausa kafin a san shi a fagen waka. Ala ya rubuta littattafai kusan tara ciki har da:[8]
• Cin Zarafi
• Bakar Aniya
• Sawaba
• Cin Fuska
• Jirwaye
• Tarzoma
• Diwanin Ala
Waƙa
[gyara sashe | gyara masomin]Ala ya fara waƙa tun yana ɗalibi a makarantar Islamiyya a lokacin da ake koya musu addini da ilimi ta hanyar waka, ta yadda za su iya fahimta da tsarawa cikin sauki. A lokacin ne aka koya musu waƙoƙin yabo ga Annabi Muhammad, duk lokacin da watan Maulidi ya faɗi, Ala na cikin waɗanda suka hau mimbari a addinin musulunci, don karanta waƙoƙi. Ta haka ne ya cusa wa Ala sha’awar kiɗa.[9][10]
Bayan Ala ya girma sai ya fara ƙoƙarin rubuta waka.[11]
Jigogin Waƙoƙinsa
[gyara sashe | gyara masomin]Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALAn Waƙa) sun kasance ɗauke da jigogi daban-daban. A cikinsu akwai masu:
- Jigon siyasa
- Jigon addini
- Jigon nishaɗi
- Jigon faɗakarwa
- Jigon baƙar addu'a[12]
Wasu Daga Cikin Waƙoƙinsa
[gyara sashe | gyara masomin]Aminu Ladan Abubakar (ALAn Waƙa) ya yi waƙoƙi masu tarin yawa. Misalansu sun haɗa da:
- Jami'a Gidan Ban Kashi
- Rayuwa A Duniya Tana Ban Tsoro
- Murnar Salla Ta Gani
- Ɗanjarida
- Allah Kaɗa Guguwar Sauyi
- Baubawan Burmi
- Makomar Arewa
- Hasbunallahu Wa Ni'imal Wakilu
- Momi Ummina
- Shahara
- Bara a Kufai
- Hikima Taguwa[13]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Hukumar fina-finan Kano ba ta da hurumin tace waƙoƙi - Aminu Ala". BBC News Hausa. 2020-08-19. Retrieved 2021-04-05.
- ↑ "...Daga Bakin Mai Ita tare da Alan Waƙa". BBC News Hausa. 2020-12-17. Retrieved 2021-04-05.
- ↑ "Aminu Ladan Abubakar, Alan Waka: Gwarzonmu Na Mako". Leadership Hausa Newspapers (in Turanci). 2020-09-17. Retrieved 2021-08-06.
- ↑ k
- ↑ k
- ↑ G
- ↑ "Kida da Al'adu - Tattaunawa da Alan Waka a Kano". RFI. 2014-03-09. Retrieved 2021-08-06.
- ↑ "Cikakken Tarihin Aminu Alan Waka" (in english). Retrieved 2021-04-05.CS1 maint: unrecognized language (link)
- ↑ Sani, Abu-Ubaida (2018-09-15). "Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) Na Salisu Ahmad YAKASAI Da Abu-Ubaida SANI". Medium (in Turanci). Retrieved 2021-04-05.
- ↑ Welle (www.dw.com), Deutsche. "Tarihin mawaƙi Abubakar Ladan Zariya | DW | 02.08.2010". DW.COM. Retrieved 2021-04-05.
- ↑ "Wakokin Aminu Ladan Abubakar, Alan Waka, Su Na Yin Kasuwa Sosai". VOA. Retrieved 2021-08-06.
- ↑ https://www.amsoshi.com/2024/03/kunshiyar-diwanin-wakokin-aminu-ladan.html
- ↑ Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19472234