Maulidi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Infotaula d'esdevenimentMaulidi
Maulidur Rasul (8413657269).jpg
Iri Islamic holidays (en) Fassara
public holidays in Tunisia (en) Fassara
religious festival (en) Fassara
Rana 12 Rabi' al-awwal (en) Fassara
hotan bana na ranar Maulidi a Dar es Salaam, Tanzania

Maulidi asali dai kalmar larabci ce mai asali da kalmar “Milad”, aka arota daga Larabci zuwa Hausa, kalmar na nufin Haihuwa ko kuma Murnar Haihuwa, Maulidi wani biki ne da Musulmai mabiya darikun Sufiyya da kuma yan Shi’a ke yi duk shekara don tunawa da haihuwar Manzo Allah Annabi Muhammad(saw). Ana yin Maulidi ne a duk 12 ga watan Rabi' al-awwal ta shekarar Hijira. Musulmi a fadin duniya ne ke bikin maulidin kuma suna fitowa domin bayyana farin cikinsu.[1][2]

Wasu kasashen musulmi da suke bayar da hutu don bikin murnar Maulidi sun hada da:

Banbancin Fahimta[gyara sashe | Gyara masomin]

Amman wasu daga cikin Musulmi sun ce basu yarda da Maulidi ba, kasancewar yadda suke ganin cewar bikin kirkirarre ne, kuma baida asali daga Manzon Allah SAW, kasan cewar bai aikata ba, kuma a ganinsu ba shi da asali a cikin Addinin Musulunci. Daga cikin malamai masu irin wannan fahimta akwai:

Wasu daga mabiya Ahlus-Sunnah wal-Jama'ah bangaren Salafiyya basa bin tsarin yin Maulidi.daga ciki harda kasar Saudi Arebiya, inda aka Haifi Manzon Allah, a kasar Najeriya akwai kungiya mai zaman kanta mai suna Izalatul bidi'a wa'ikamatus sunna, kungiyace dake wa'azi akan kawar da bidi'o'i da kuma tsaida sunna wacce Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ya kirkira. suna da reshe a Kaduna.

A mahangar Sufaye da Yan shi'a[gyara sashe | Gyara masomin]

Sai dai mabiya darikun sufaye da suka hada da Qadiriyya, Tijjaniyya da kuma mabiya Shi’a da suke danganta kansu ga Imamu Ali suna bikin Maulidin. Ana karatun Al’kur’ani da kuma jawabai na tarihi da fadakarwa ne a guraren taron; hade da shagulgulan walima da wakokin yabo ga Manzon Allah (s.a.w) don bayyana farin ciki.

Wasu malaman da suke ganin dacewar bikin Maulidin sun hada da:

.[6][7][8][9][10][11][12][13][10][14][15][16][10][17][18][19][20][21]

Akwai kuma malamai da suke ganin bikin Maulidi ya danganta da niyyar mai yi ne. Idan aka saka abubuwan da shari’a ta hana to bikin ya haramta. Amma idan aka yi shi don farin ciki da Manzon Allah (saw) to wannan za a samu ldan niyya. Daga cikin masu wannan mahanga akwai:

• Sheikh Ahmad Ibn Taimiyya [22]

• Sheikh Usman Danfodiyo

• Sheikh Abdallah bn Bayyah [23]

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

 1. Schimmel, Annemarie (1974). A history of Indian literature: Modern Indo-Aryan literatures, part II. Sindhi literature, Part 1. Harrassowitz Verlag. p. 7. ISBN 978-3-447-01560-8.
 2. Sperl, Stefan; C. Shackle (1996). Qasida Poetry in Islamic Asia and Africa: Classical traditions and modern meanings. BRILL. p. 361. ISBN 978-90-04-10295-8.
 3. https://www.dailytrust.com.ng/fg-declares-monday-public-holiday-for-eid-el-maulud.html
 4. https://www.trtworld.com/life/heres-how-nine-countries-celebrated-prophet-muhammads-birthday-250772
 5. http://www.islamicacademy.org/html/Articles/English/Milad.htm
 6. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named IS
 7. Al-Bahith, Yahya (February 27, 2012). "What is the meaning of Bida'a? Is using modern technology in Dawah considered as Bida'a?". Islam Q & A. Retrieved 26 June 2015. Innovation and discoveries related to our daily life is encouraged in Islam, as long as it does not contradict Islamic teachings and principles. Using modern technology in Dawah is required as means to convoy the message of Islam.
 8. Fat-hul Baari by Ibn Hajar al-Asqalani (vol.2, page 443)
 9. Bin Ramzaan Al Haajiree, Muhammad (2013). The Guidance of the Companions With Regards To The People Of Innovation (Salafi). MPUBS. p. 8. Retrieved 3 September 2015.
 10. 10.0 10.1 10.2 from: "Concept of Bidah in Islam". Alahazrat.net. INTERNATIONAL ISLAMIC WEBSITE. Archived from the original on 11 April 2018. Retrieved 31 August 2015.
 11. (Fathul Bari chap on Taravi by Hafidhh Asqalani)
 12. Ibn Qayyim al-Jawziyya wrote: 'The one who denies the punishment of the grave is an innovater'.
 13. Qadi Shawkani Nayl-ul-Autaar, chapter Salaah Al Taravee
 14. Tahzeeb al-Asma wal-Lughat, word Bid’ah by Imam Nawawi
 15. Tahzeeb al Asma wal lughaat word Bid’ah by Imam Nawawi
 16. (Hafidhh Asqalani, Fathul Bari, chapter on Taravi)
 17. (Hafidhh ibn Rajjab, Jaami' Al Uloom Al Hukkam, p 252)
 18. [Tirmizi chapter Il
 19. Abu Nu'aym in al-Hilyah (7/26) and Ibn Battah (no.444)
 20. Abu Shaamah (no. 39)
 21. Al-Ghazali, Book of Knowledge, p.206
 22. Iqtida' Al Sirat Al Mustaqeem (Cairo, al-Fiqqi 1950 edition, pages 294 and 297)
 23. http://binbayyah.net/english/on-celebrating-the-prophet’s-birthday/