Abubakar Gumi
![]() | |
---|---|
![]() | |
Rayuwa | |
Haihuwa | Gumi, 5 Nuwamba, 1922 |
ƙasa | Najeriya |
Harshen uwa | Hausa |
Mutuwa | Landan, 11 Satumba 1992 |
Yanayin mutuwa | (sankaran bargo) |
Ƴan uwa | |
Yara |
view
|
Karatu | |
Harsuna |
Turanci Hausa Larabci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a |
qadi (en) ![]() |
Kyaututtuka | |
Imani | |
Addini | Mabiya Sunnah |


Sheikh Abubakar Mahmud Gumi (O dañaama ñalaande 5re lewru 9ɓru hitaande(
1922) miladiy ndenaboo O maayi ñalaande 11re lewru 9ɓru hitaandeyu(1992)haa a Landan)[1][2] o laati mallumjo diina alsilaamaku anndaaɗo nden boo kiitoowo hiitotoɓe (Grand kadi) mo woyla lesdi Naajeeriya. O laati baaba, malla daɲragal nden ɗaɗol tiggunde Izala e Salaf haa Najeriya.[3]
Karatu[gyara sashe | gyara masomin]
Ya yi karatu da rubuce-rubuce a kan addinin musulunci sosai, ya fassara Qur'ani zuwa harshen Hausa, kuma shine mutum na farko daya rubuta tarjama wato fassarar dai-daikun ayoyin dake Alkur'ani.[4] Hakan ne ya sa ya samu nasarar samun kyautan Sarki Faisal(King Faisal Award) daga kasar saudiya. Malamin dai ya kasance babban aboki kuma mai ba wa Firimiya Ahmadu Bello sardaunan Sakkwato shawara. Shi ne mahaifin Dakta Shaykh Ahmad Gumi.
Shahara[gyara sashe | gyara masomin]
Gumi ya shahara tun lokacin mulkin mallakar turawa a matsayin mai fada a ji, yana sukar salon Mulkin Turawa cewa ya karya lagon sarakunan Musulmi kuma hakan yana kara karfafa al'adun Turai a kasashen musulunci. A farkon shekara ta 1960s an samu barkewar rikici tsakanin shi da malaman sufaye wanda daga baya rikicin ya koma muhawara a gidajen rediyo da talabijin a shekarun 1970 zuwa shekara ta 1980.[5] Ya riƙa amfani da ranakun Juma'a a matsayin lokutan yada akidunsa a babban masallacin juma'a na Kaduna mai suna Masallacin Sultan Bello.
Dangi[gyara sashe | gyara masomin]
Abubakar Gumi ba a san takamaiman yawan yayansa ba, amma mafi shahara a cikinsu shi ne Dr. Ahmad Gumi Wanda shi ne ya gaji Mahaifinsa a matsayin mai gabatar da wa'azi a masallacin na Sultan Bello dake Kaduna. Dr Ahmad Gumi kwararren likita ne daga Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Kuma tsohon jami'in sojin Najeriya ne, ya bar aikin soja inda ya tafi zuwa Saudiyya domin karanta ilimin fikihu, a jami'ar Ummul Quraa da ke birnin Makka inda ya samu shaidar digirin digir-gir.[6]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]
- ↑ The Independent: "Obituary: Sheikh Abubakar Mahmud Gumi" by Karl Maier 16 September 1992
- ↑ John O. Hunwick; Rex Séan O'Fahey (1994). Arabic Literature of Africa: The writings of central Sudanic Africa Vol.2. Volume 13. BRILL. p. 551. ISBN 90-04-10494-1.
- ↑ Hunwick, John O.; O'Fahey, Rex Séan (1994). Arabic Literature of Africa: The writings of central Sudanic Africa Vol.2. Volume 13. BRILL. ISBN 978-90-04-10494-5.
- ↑ John N. Paden, Muslim Civic Cultures and Conflict Resolution: the challenge of democratic federalism in Nigeria, Brookings Institution Press, 2005. p 60. ISBN 0-8157-6817-6
- ↑ The Independent: "Obituary: Sheikh Abubakar Mahmud Gumi" by Karl Maier 16 September 1992
- ↑ John Owen Hunwick. Religion and National Integration in Africa: Islam, Christianity and Politics in the Sudan, Northwestern University Press, 1992. p 551. ISBN 0-8101-1037-7