Jump to content

Amir Khan

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Amir Khan
UNICEF Goodwill Ambassador (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa Mumbai, 14 ga Maris, 1965 (59 shekaru)
ƙasa Indiya
Ƴan uwa
Mahaifi Tahir Hussain
Abokiyar zama Reena Dutta (en) Fassara  (18 ga Afirilu, 1986 -  Disamba 2002)
Kiran Rao (en) Fassara  (28 Disamba 2005 -  2 ga Yuli, 2021)
Yara
Ahali Faisal Khan (en) Fassara, Nikhat Khan (en) Fassara da Farhat Datta (en) Fassara
Karatu
Makaranta Bombay Scottish School (en) Fassara
St. Anne's High School, Bandra (en) Fassara
Narsee Monjee College of Commerce and Economics (en) Fassara
Harsuna Harshen Hindu
Urdu
Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan wasan kwaikwayo, darakta, mai tsara fim, marubin wasannin kwaykwayo, mai gabatarwa a talabijin da producer (en) Fassara
Kyaututtuka
Wanda ya ja hankalinsa B. R. Ambedkar
Imani
Addini Musulunci
IMDb nm0451148

Mohammed Aamir Hussain Khan (an haifeshi a ranar 14 ga watan Maris shekarar 1965), jarumi ne a masana'antar finafinai ta kasar Indiya, kuma darakta, maishirya fim kuma sananne a gabatar da shirin talabijin. Ya kwashe sama da shekaru talatin a masana'antar Bollywood, Khan ya ayyana kansa a matsayin fitacce kuma babban jagora a masana'antar ta Bollywood.[1][2] Yana da masoya masu yawan gaske musamman ma a Indiya da Sin, kuma jaridar Newsweek ta aiyanashi da babban tauraro, [3][4] a duniya.[5][6][7] Amir Khan ya samu kyaututtuka da lambobin yabo masu dimbin yawa, daga ciki akwai Filmfare Awards, hudu, National Film Awards da AACTA Awards, harma ma ta Academy Award. Gwamnatin Indiya ta girmama shi da kyautar Padma Shri a shekarar 2003 da kuma Padma Bhushan a shekarar 2010,[8] sannan ya samu lambar girmamawa daga gwamnatin kasar Sin a shekarar 2017.[9]

Farko Amir Khan ya fara baiyana fuskar sa akwatin talabijin yana dan shekara takwas a cikin fim din kawun sa Nasir Hussain mai suna Yaadon Ki Baaraat a shekarar (1973). Fim din sa na farko bayan girmansa shine Holi a shekarar (1984), sannan ya fara fita a matsayin cikakken jarumi a fim din soyayya na Qayamat Se Qayamat Tak a shekarar (1988). Kwazon da ya nuna a fim din Raakh a shekarata (1989) ya saka shi ya samu kyautar National Film Award. Bayan karin samun karbuwar fina finan sa da kuma samun nasarorin da yayi a shekarun a shekarar 1990, sai Amir Khan ya aiyana kansa da daya daga cikin na gaba gaba na masana'antar finafinai ta Indiya. Hakan yafarune bayan samun karbuwar fina finan sa kamar DilWanda akayi a shekarar (1990) da Raja Hindustani shekarar (1996) da kuma Sarfarosh a shekarar (1999).[10]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Readers' Picks: Top Bollywood Actors". Rediff. 17 August 2006. Retrieved 26 January 2010.
  2. "Powerlist: Top Bollywood Actors". Rediff. 8 August 2006. Retrieved 26 January 2010.
  3. "Whoa! Aamir Khan Is 'World's Biggest Superstar'!". 13 March 2018.
  4. "Aamir Khan Is The Worlds Biggest Superstar Says A Trade Analyst!". 29 March 2018.
  5. "Aamir Khan is the biggest movie star on the planet—and a woke feminist, too". Newsweek. 19 October 2017.
  6. "Success By 'Secret Superstar' Could Give Aamir Khan The Title Of The World's Biggest Movie Star". Forbes. 3 October 2017.
  7. "Why Aamir Khan Is Arguably The World's Biggest Movie Star, Part 2". Forbes. 5 October 2017.
  8. "Padma Awards" (PDF). Ministry of Home Affairs, Government of India. 2015. Archived from the original (PDF) on 19 October 2017. Retrieved 21 July 2015.
  9. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named afternoondc
  10. Press Trust India (30 November 2000). "I become the audience". Rediff. Retrieved 26 January 2010.