Jump to content

Andrew Jonathan Nok

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Andrew Jonathan Nok
Rayuwa
Haihuwa Jihar Kaduna, 11 ga Faburairu, 1962
ƙasa Najeriya
Mutuwa 21 Nuwamba, 2017
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a chemist (en) Fassara da biochemist (en) Fassara
Muhimman ayyuka Genome and proteome screening of Onchocerca volvulus reveal putative vaccine candidates (en) Fassara
Kyaututtuka
Mamba Makarantar Kimiyya ta Najeriya

Andrew Jonathan Nok, NNOM (An haife shi a ranar 11 ga watan Fabrairu, 1962 - ya mutu ranar 21 ga watan Nuwamba, 2017) Farfesa ne a Nijeriya a fannin Biochemistry kuma sakataren hulda da jama'a na kwalejin kimiyya ta Nijeriya.[1] A shekarar 2010 ya kasance wanda ya samu lambar yabo ta Nigeria National Order of Merit Award (NNOM), a fannin kimiyya kuma a shekarar 2013 ya lashe kyautar Alexander Humboldt. Ya rasu ne a ranar 21 ga watan Nuwamba, shekarar 2017 bayan gajeriyar rashin lafiya.

Farkon Rayuwa da Karatu

[gyara sashe | gyara masomin]

An haife shi a ranar 11 ga watan Fabarairu a shekara ta 1962, a Jihar Kaduna, a Arewacin Najeriya, Iyayensa sun kasance daga kauyen Nok a karamar hukumar Jaba ta Jihar Kaduna.[2] Ya halarci makarantar firamare ta LEA da ke Jihar Kaduna, ya cigaba da makarantar Sakandaren Gwamnati dake garin Kafancan in da ya samu shaidar kammala karatu ta West Africa School Certificate a shekarar 1979, a shekarar ya samu shiga Jami'ar Ahmadu Bello da ke garin Zaria Jihar Kaduna inda ya yi digirin farko a fannin Biochemistry a shekarar 1983, ya yi digiri na biyu a shekarar 1988, digiri na uku kuma a shekarar 1993. Ya auri Amina Nok kuma suna da diya guda Ukku Anita,Amanda da Nathan Nok.[3]

Nok ya shiga makarantar Firamare ta LEA Primary School Kafanchan, daga nan ya tafi Government Secondary School Kafachan inda ya kammala sakandare dinsa kuma ya karbi kwalin WASC dinsa a shekarar 1979, a shekarar aka dauke shi Jami'ar Ahmadu Bello dake garin Zariya inda ya karbi shaidar digirinsa na farko a bangaren Biochemisrty a shekarar 1983, sai digirinsa na biyu a shekarar 1988, sai digirinsa na ukku wato Doctorate a shekarar 1993.

An nada Nok a matsayin kwamishinan Lafiya da hidimar Al'umma daga gwamnan jihar kaduna Malan Nasiru El-rufa'i a ranar 29 ga watan yuli shekarar 2015.[4][5]

1. Mamba a, Nigerian Academy of Science 2. Mamba a, Alexander von Humboldt Foundation 3. Mamba a, Japan Society for the Promotion of Science Lady Davis Fellows 4. Mamba a, Nigerian Society of Biochemistry and Molecular Biology (NSBMB) 5. Mamba a, Nigerian Academy of Science (NAS)

  1. "Members of Council". Nigerian Academy of Science. Archived from the original on 7 July 2015. Retrieved 6 June 2015.
  2. "Members of Council". Nigerian Academy of Science. Archived from the original on 7 July 2015. Retrieved 6 June 2015
  3. Lawani Mikairu (1 December 2011). "Five professors win 2010/2011 Merit Award". Vanguard News. Retrieved 6 June 2015
  4. "Prof. Andrew Jonathan Nok (NNOM)". Nigerian National Order of Merit. Retrieved 6 June 2015
  5. "el-rufai-nominates-13-commissioners.html". Retrieved 29 July 2015.[permanent dead link]