Jump to content

Arbeloa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Arbeloa
Rayuwa
Cikakken suna Álvaro Arbeloa Coca
Haihuwa Salamanca (en) Fassara, 17 ga Janairu, 1983 (41 shekaru)
ƙasa Ispaniya
Mazauni Madrid
Harshen uwa Yaren Sifen
Karatu
Harsuna Yaren Sifen
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
Real Zaragoza (en) Fassara1991-200298
  Spain national under-19 football team (en) Fassara2001-200140
  Spain national under-17 football team (en) Fassara2001-200110
Real Madrid C (en) Fassara2002-2003160
Real Madrid Castilla (en) Fassara2003-2006840
Real Madrid CF2004-200620
  Spain national under-21 association football team (en) Fassara2005-200510
  Deportivo de La Coruña (en) Fassara2006-2007200
Liverpool F.C.2007-2009662
  Spain national association football team (en) Fassara2008-2013560
Real Madrid CF2009-20161533
West Ham United F.C. (en) Fassara31 ga Augusta, 2016-ga Yuni, 201730
 
Muƙami ko ƙwarewa fullback (en) Fassara
Nauyi 78 kg
Tsayi 184 cm
IMDb nm3972635
Álvaro Arbeloa


Álvaro Arbeloa Coca (an haifeshi a ranar 17 Junairu 1983), dan wasa ne da ya aje taka leda a harkar kwallon kafa, sai dai ya kasance mai bada horo a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid CF Juneil A. Ya kasance dan wasan baya na gefen dama ko kuma gefen hagu wata sa'i.[1][2]

Ya fara doka wasa a matsayin kwararren dan wasa a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, sai dai mafi yawanci yana zama a matsayin dan jira. A shekara ta alif dubu biyu da shida 2006 ya koma kungiyar kwallon kafa ta Diportivo daga bisani kuma ya koma kungiyar kwallon kafa ta Liverpool bayan daukar rabin shekara kacal da yayi a kungiyar Diportivo. A kungiyar Liverpool, ya buga wasanni har guda 98 inda ya shafe shekaru 3 cir a kungiyar. A shekarar dubu biyu da tara 2009, ya sake komawa kungiyar ta Real Madrid da yarjejeniyar kudi kimanin £5m. Dan wasan ya shafe shekaru masu yawa a kungiyar inda ya shafe shekaru bakwai tare da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid din inda ya samu nasarar lashe kofuna har guda takwas 8 daga ciki harda gasar Laliga ta shekarar 2011-12 da kuma kofin gasar zakarun nahiyar Turai inda ya lashe gasar har sau biyu 2.

A fannin kasa kuma, dan wasan ya kasance dan kasar sifaniya inda ya wakilci kasar tashi ta sifaniya har sau 56. Dan wasan ya wakilci kasar sifaniya a gasar kofin duniya na shekarar dubu biyu da goma 2010, Euro 2008 da kuma Euro 2012 inda ya lashe dukkanin wadannan gasanni guda 3.

Rayuwar kwallo

[gyara sashe | gyara masomin]

Real Madrid

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Arbeloa a samalanca, castle,da leon daga baya suka koma zaragoza su duka hada iyalanshi a lokacin da yake dan shekara 4. Ya fara taka leda ne a kungiyar kwallon kafa ta Real Zaragoza daga bisani kuma ya koma kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid amma ta samari lokacin yana dan shekara goma sha takwas 18.[3]

Dan wasan ya shafe shekaru 3 cir da Real Madrid castilla inda ya bada gudummawar buga wasanni 38 har ya samu nasarar jefa kwallo daya a raga. Ya fara buga wasan Laliga na farko inda aka sakoahi daga baya a wasan da akayi kunnen doki da kungiyar kwallon kafa ta Real betis 1-1.[4]

A ranar 24 ga watan Juli 2006 Arbeloa yasa hannun kwantiragi da kungiyar ta Diportivo La Kuruna inda kwallon kafa ta Real Madrid ta shigo cikin sayayyar da kaso hamsin da ta zuba har na tsawon shekaru 3.[5] Dan wasan yakan ce wannan kadara tace na buga wasanni a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid har na tsawon shekaru 5 a wani irin yanayi na lokaci inda akwai wadatattun yan wasan baya har guda shidda. Saboda haka wani abu dole ya shigo.[6]

Kusan wata shidda da ya shafe da kungiya daga galacia. Dan wasan ya fito cikin wasanni guda ashirin da daya kuma ya fito cikin gasar lig sau goma sha takwas 18.[7][8]

Dan wasan ya kulla yarjejeniya da kungiyar ta premier league wato Liverpool a ranar 31 ga watan Junairu 2007 inda ya buga wasa a karkashin mai horaswa Rafael Benitez.[9][10] Ya fara buga wasa a premier league a ranar 10 ga watan Fabrairu inda ya canji dan wasa mai suna Jamaine pennant inda ya shigo wasan cikin mintina 15 kafin a tashi wasan a wasan da suka buga da kungiyar kwallon kafa ta Newcastle inda suka samu rashin nasara daci biyu da daya 2-1 aw wasan waje da aka buga.[11]

Dan wasan ya buga wasan shi na farko tare da jajayen a wasan da ya buga da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona a shekarar 2006-2007 a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai inda ya wakilci kungiyar a matsayin mai tsaron baya na gefen hagu a filin wasa na camp nou. Saboda kafarsa ta dama zata iya tare Lionel Messi dan kwallon da yake da yanke a kafarsa kuma dan wasa mai basira daya gagari manyan yan bayan duniya. Sannan shi Lionel Messi dan kwallo ne mai hanzari sosai da kuma basira. Arbeloa ya samu damar tare gwarzon dan wasan inda kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta samu nasara akan kungiyar Lionel Messi din daci biyu da daya 2-1. Wasan ya kare ne daci biyu da biyu 2-2 inda dan wasan ya buga mintina casa'in kuma ya haska sosai kuma yayi kokari a wasan.

Dan wasan ya zura kwallo ta farko a kungiyar Liverpool inda suka fafata da kungiyar kwallon kafa ta Reading wasan da aka buga a ranar bakwai bakwai 7 ga watan Aprilu shekara ta 2007-08. Ya canji steve finnan a minti na karshe a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai inda suka fafata da kungiyar kwallon kafa ta Ac milan a wasan da suka samu rashin nasara daci biyu da daya 2-1.

Dan wasan ya koma sanya lamba 2 a kungiyar saboda wani dalili nashi kuma ya buga wasanni guda arba'in da daya inda kungiyar tashi ta kare a mataki na hudu a gasar premier league. Inda ta samu lasisin buga gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai.

Dawowa Real Madrid

[gyara sashe | gyara masomin]

A ranar 29 ga watan Juli 2009, an wallafa cewa kungiyar kwallon kafa ta Liverpool sun cima matsaya da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Wajan daukar dan wasan akan jumillar kudi £5m da kwantiragi na tsawon shekaru 5. Bayan zamani michael solgado da kuma Miguel Torres Kungiyar ta Real Madrid taba dan wasan lamba 2 a matsayin lambar goyo. Dan wasan ya shafe shekara yana buga gefen dama a gefen baya inda ya zura kwallo ta farko a ranar 13 ga watan Fabrairu 2010 a wasan waje da suka fita suka samu nasara daci ukku da nema 3-0 inda suka fafata da kungiyar kwallon kafa ta xerez CD. Wasa na biyu daya jefa kwallo wasane na yan gari daya anacema wasan madrid derby wanda aka buga a ranar ashirin da takwas 28 ga watan Match inda yayi amfani da kafarsa ta dama ya makalama Degea ita yakaishi makaifa a wasan da suka buga da kungiyar Atletico Madrid inda suka samu nasara daci ukku da biyu 3-2 karkashin mai bada horo wato babban koci mai suna Jose Morinho.

Yayi murnar bayyana da yayi sau goma a cikin kofin zakarun nahiyar Turai da kwallonsa ta farko a gasar inda ya jefa kwallon daga wajen layi na daga kai sai mai tsaron raga. Kuma sun samu nasara inda suka jefa kwallaye hudu a raga ba tareda an jefa musu kwallo ko daya a raga ba awasan da suka fafata da kungiyar kwallon kafa ta Ajax a wasan rukuni na kofin zakarun nahiyar Turai.

A shekara ta alif 2011-12 saboda raunin Cavalho ta sanya aka medo Sergio Ramos ya dawo mai tsaron baya ta santa wato lamba 5 da lamba 6. Hakan yaba dan wasan dama ta bugawa kullum a cikin jerin mutum hudu na baya. A watan Ogusta 2012, dan wasan ya tsawaita zamansa tare da kungiyar tashi ta Real Madrid har zuwa shekara ta alif 2016. A hankali kuma Arbeloa ya zama dan kwallon ado. A shekarar alif dubu biyu da goma sha biyar 2015 zuwa shekara ta alif dubu biyu da goma sha shida 2016 ya buga wasanni 9 kacal a duka gasanni da kungiyar ta buga a shekarar baki daya. Sai dai daga ciki wasa 9 din, ya buga gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai inda ya samu nasarar lashe gasar a karo na biyu cikin shekaru 3. A ranar 8 ga watan May 2016 yayi sanarwa cewa zai bar kungiyar ta Real Madrid a ranar talatin ga wata June

West ham

Daga bisani dan wasan ya dawo gasar Premier league inda ya shafe tsawon shekara daya a kungiyar kwallon kafa ta West ham United inda ya doka wasanshi na farko a ranar 29 ga watan September da kungiyar kwallon kafa ta Accrington stanley a wasan gida na West ham United inda suka samu nasara daci daya mai ban haushi 1-0. Daga baya kuma ya ajiye kwallo a shekarar alif dubu biyu da goma sha bakwai 2017.

Bada Horo

Arbeloa ya dawo kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid a watan September shekarar alif dubu biyu da ashirin 2020 inda aka bashi aikin bada horo ga yan kasa da shekaru goma sha hudu U14. Bayan shekara biyu kuma ya samu nasarar komawa Juvenil A.

  1. Sánchez-Flor, Ulises (15 October 2010). "Arbeloa es el jugador 'número 12'" [Arbeloa is player 'number 12']. Marca (in Sifaniyanci). Retrieved 19 June 2013.
  2. Rodrigálvarez, Eduardo (1 June 2012). "El comodín de la defensa" [The joker of defence]. El País (in Sifaniyanci). Retrieved 19 June 2013.
  3. Carrasco, Carlos (19 February 2012). "Álvaro Arbeloa, el espartano incansable" [Álvaro Arbeloa, the tireless spartan] (in Sifaniyanci). Defensa Central. Retrieved 19 June 2013.
  4. Artús, José Luis (17 October 2004). "Ni ambición" [No ambition]. Mundo Deportivo (in Sifaniyanci). Retrieved 19 June 2013.
  5. "El Real Madrid traspasa a Alvaro Arbeloa al Deportivo de La Coruña" [Real Madrid transfer Alvaro Arbeloa to Deportivo de La Coruña]. Diario AS (in Sifaniyanci). 24 July 2006. Retrieved 12 April 2020.
  6. "Alvaro Arbeloa se marcha al Depor" [Alvaro Arbeloa goes to Depor] (in Sifaniyanci). 86400. 25 July 2006. Retrieved 19 June 2013.
  7. "Arbeloa es el ex jugador del Castilla más utilizado" [Arbeloa is the most used former Castilla player]. Diario AS (in Sifaniyanci). 29 September 2006. Retrieved 2 May 2018.
  8. García González, Antía (21 February 2013). "Yo jugué en el Dépor: Álvaro Arbeloa" [I played for Dépor: Álvaro Arbeloa] (in Sifaniyanci). Vavel. Retrieved 2 May 2018.
  9. "Reds swoop for Spanish pair". Liverpool F.C. 31 January 2007. Retrieved 17 August 2014.
  10. "Arbeloa and Duran join Liverpool". BBC Sport. 31 January 2007. Retrieved 19 June 2013.
  11. Sinnott, John (10 February 2007). "Newcastle 2–1 Liverpool". BBC Sport. Retrieved 26 May 2017.