Jump to content

Asisat Oshoala

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Asisat Oshoala
Rayuwa
Haihuwa Ikorodu, 9 Oktoba 1994 (30 shekaru)
ƙasa Najeriya
Mazauni Barcelona Province (en) Fassara
Karatu
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Yarbanci
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
FC Robo (en) Fassara2009-2013
  Nigeria women's national under-20 football team (en) Fassara2012-2014137
  Kungiyar kwallon kafa ta mata ta Najeriya2013-1711
Rivers Angels F.C. (en) Fassara2013-20156
Liverpool F.C. Women (en) Fassara2015-2015123
Arsenal W.F.C. (en) Fassara2016-2016112
Dalian Quanjian F.C. (en) Fassara2017-20182023
FC Barcelona Femení (en) Fassara2019-20243233
Bay FC (en) Fassara2024-
 
Muƙami ko ƙwarewa Ataka
Tsayi 172 cm
Kyaututtuka
Imani
Addini Musulunci
asisat a rigar training
asisat a Barcelona Fc
Asisat Oshoala a 2019
asisat in uefa women champion league
asisat Oshoala a training
asisat tareda mai hura wasa
asisat Oshoala in action

Asisat Lamina Oshoala MON (an haife tane a ranar 9 ga watan Oktoba a shekarar 1994) Yar'Najeriya ce, kuma ƙwararriyar yar'wasan ƙwallon ƙafa wacce take buga wasa a ƙungiyar kwallon kafa na FC Barcelona Femení a ƙasar Spaniya a Primera División amatsayin yar'wasan gaba.[1] Tazama year wasa mafi yawan cin ƙwallaye a gasar cin kofin duniya na mata yan kasa da shekaru 20 2014 FIFA U-20 Kofin Duniya na mata kuma itace yar'wasa mafi ƙayatarwa. Ta sake zama yar'wasa mafi ƙayatarwa kuma nabiyu a yawan cin ƙwallaye da ƙungiyar Super Falcons wanda suka lashe gasar 2014 African Women's Championship.

Matakin Kulub

[gyara sashe | gyara masomin]

A ranar 23 ga watan Janairun shekara ta 2015, Oshoala ta koma Liverpool Ladies. Maikula da ƙungiyar Liverpool, Matt Beard ta bayyana ta amatsayin "ɗaya daga cikin mafiya ƙayatarwan yan'wasa matasa na duniya".[2] Dukda cewa ansamu jita-jita a lokacin na zata koma ne wasu ƙungiyoyin, amma tace taji ɗadin data koma Liverpool.[3]

Asisat Oshoala tayi rashin buga wasanni biyu na A kakar shekarar 2015 sakamakon raunin gwiwa data samu, amatsayin Liverpool waɗanda suke rike da kofin gasar amma sun ƙare amatsayi na bakwai ne cikin ƙungiyoyi takwas.[4] A watan Janairu na shekarar 2016 Liverpool ta fidda wani rehoton cewan Arsenal Ladies sun fara tattaunawa akan sayan Oshoala sannan kuma ita yar'wasan tana tattaunawa da kulub ɗin na London.[5][6]

A ranar 10 ga watan Febrerun shekarar 2017, ƙungiyar ƙasar Sin Dalian Quanjian F.C. sun sayi Oshoala.[7]

Amma kuma a ranar 31 Janairun shekarar 2019, ƙungiyar kasar Spaniya, FC Barcelona Femení sun sayi Oshoala akan aro na zuwa karshen ahekara.[8]

Asisat Oshoala takasance tayi matuƙar ɓata wa mahaifanta rai sanda tabar makaranta ta koma buga wasan ƙwallon ƙafa.[9] Oshoala takasance Musulma ce, Dan kuwa iyayen ta dukkaninsu mabiya addinin musulunci ne.[10]

  1. "Oshoala off to China". SuperSport. 11 February 2017. Retrieved 11 February 2017.
  2. "Asisat Oshoala: Liverpool Ladies sign Nigerian prospect". BBC Sport.
  3. Kessel, Anna (21 March 2015). "Happiness lies with Liverpool for Nigerian superstar Asisat Oshoala". The Guardian.
  4. Currie, Jo (13 October 2015). "Liverpool Ladies: Injuries 'impacted' on season, says Beard". BBC Sport.
  5. "Nigerian striker Oshoala to hold talks with Arsenal". Liverpool L.F.C. 26 January 2016. Archived from the original on 3 July 2018. Retrieved 26 January 2016.
  6. "Liverpool Ladies Accept Arsenal's Bid For Asisat Oshoala | Wolexis Sports Blog". www.wolexis.com.
  7. 权健女足引进强力外援 二人均来自欧洲联赛. sina weibo (in Harshen Sinanci). Dalian Quanjian Official Weibo. 10 February 2017.
  8. https://www.vanguardngr.com/2019/01/asisat-oshoala-joins-barcelona-from-dalian-quanjian/amp/
  9. Taylor, Louise (5 June 2015). "Women's World Cup 2015: 10 players to watch". The Guardian. Retrieved 5 June 2015.
  10. Wejinya, Sammy (25 October 2014). "Q & A with Asisat Oshoala". SuperSport. Retrieved 15 November 2014.