Jump to content

Aweng Ade-Chuol

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Aweng Ade-Chuol
Rayuwa
Haihuwa Kakuma (en) Fassara
ƙasa Sudan ta Kudu
Sana'a
Sana'a model (en) Fassara da jarumi
Kyaututtuka

Aweng Chuol 'yar ƙasar Sudan ta Kudu ce abin 'yar talla, jarumar wasan kwaikwayo, kuma mawakiya.

Kuruciya da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Chuol a sansanin 'yan gudun hijira na Kakuma a kasar Kenya, danginta sun gudo daga yakin basasar Sudan na biyu. Sun ƙaura zuwa Ostiraliya lokacin da Chuol tana da shekaru bakwai. Tana da ‘yan’uwa 11, wadanda ita ce babba a cikinsu. Mahaifinta karamin soja a yakin basasar Sudan na farko kuma ya yi yaki a karo na biyu, ya mutu sakamakon harbin bindiga da ya samu a shekarar 2013.

A shekara ta 2017, yayin da take aiki a McDonald's a Sydney a lokacin tana da shekaru 18, wani wakili daga Chadwick Model ya lura da Chuol, wanda ya tallafa mata ta yi aiki tare da su. Ta sanya hannu tare da kungiyar kuma ta fara aikinta a matsayin 'yar talla. Tun daga lokacin ta yi tallan samfuran Fenty, Vetements, da Pyer Moss, da sauransu. [1]

A cikin 2020, Chuol ta fito a cikin fim ɗin wakar Beyoncé da kundi na kallo wato Black Is King, kuma a cikin tallan hutu na Ralph Lauren tare da matarsa.

Chuol tana karatun shari'a da kimiyyar tunani a Jami'ar New England, daga inda za ta kammala karatunta a 2021. Tana fatan yin amfani da digirinta na shari'a don taimaka wa marasa galihu, kuma tana son samun cibiyar kula da masu tabin hankali a Sudan ta Kudu. Har wayau Chuol tana daukan darussan wasan kwaikwayo, kuma ana burin zama 'yar wasan kwaikwayo. Ta ambaci Lupita Nyong'o da Shonda Rhimes a matsayin abubuwan da suka jawo ra'ayinta ga sana'arta. [1]

An sanya Chuol a cikin jerin Mata 100 na OkayAfrica a shekara ta 2019.

Chuol ta hadu da matar ta Alexus a cikin watan Janairun 2019. Sun shafe watanni tara suna soyayya kafin su yi aure. Ma'auratan sun yi aure a watan Disamba a wannan shekarar a New York City Hall, kuma suna da ma'auni na "XII" a kan yatsunsu na zobe. Bayan aurensu, Chuol ta fuskanci cin zarafi na luwadi, musamman daga al'ummomin Sudan ta Kudu, wanda ta kai ga yunkurin kashe kanta bayan 'yan watanni. Ta yi kwana uku a sashen kula na gaggawa da kuma wasu kwanaki shida a cikin asibiti sakamakon haka. [2]

An nuna Chuol da Alex a bangon mujallar Elle a cikin 2020. Yi zuwa watan Satumban 2020 ma'auratan suna zaune a Landan.

Ma'auratan sun rabu a ƙarshen Disamba 2021.

  1. 1.0 1.1 Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named :0
  2. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named :2

Hanyoyin haɗi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]