Ayuba Dauda

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ayuba Dauda
Rayuwa
Haihuwa Mogadishu, 24 ga Faburairu, 1990 (33 shekaru)
ƙasa Somaliya
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  Juventus FC (en) Fassara2008-201310
F.C. Crotone (en) Fassara2009-2010110
F.C. Crotone (en) Fassara2009-2009110
  A.C. Lumezzane (en) Fassara2010-201141
A.S. Gubbio 1910 (en) Fassara2011-2011114
Cosenza Calcio (en) Fassara2011-2012142
  FC Sion (en) Fassara2011-2011
  Somalia national football team (en) Fassara2011-
FC Chiasso (en) Fassara2011-
A.S. Gubbio 1910 (en) Fassara2012-2012114
FC Chiasso (en) Fassara2013-201492
Budapest Honvéd FC (en) Fassara2013-2015167
Budapest Honvéd FC (en) Fassara2014-
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga tsakiya
Lamban wasa 9
Nauyi 65 kg
Tsayi 177 cm

Ayub Daud (Somali, Larabci: أيوب داود‎  ; an haife shi a ranar 24 ga watan Fabrairun shekara ta alif dubu ɗaya da dari tara da casa'in (1990)) Miladiyya. ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Somaliya wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan gaba ko mai kai hari ga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Somaliya.

Aikin kulob[gyara sashe | gyara masomin]

Dan Daud Hussein, tsohon memba ne na tawagar kasar Somaliya, [1] An haifi Daud a Somalia, kuma ya koma Cuneo, Italiya tare da iyalinsa yana da shekaru biyar.[2][3]

Ya shiga sashin matasa na Juventus a cikin shekarar 2000 kuma ya fara halarta tare da tawagar Primavera (ƙasa da 20) a cikin kakar 2007-2008. Daud yana cikin tawagar Juventus a shekarar 2009 Torneo di Viareggio, inda aka yaba masa a matsayin daya daga cikin mafi kyawun 'yan wasan kwallon kafa na gasar. Ya zura kwallaye 20, kuma shi ne ya fi zura kwallaye a gasar.[4]

A ranar 14 ga watan Maris ɗin shekarar 2009, ya buga wasansa na farko tare da Juventus, ya maye gurbin Sebastian Giovinco a cikin mintuna na ƙarshe na nasarar Seria A 4-1 akan Bologna. [5]

A ranar 6 ga watan Agustan 2009, Daud ya bar Juventus kuma ya koma Crotone a matsayin aro. Matashin ya sha wahala a kulob din kudancin Italiya, kuma daga baya ya koma Juventus a watan Janairu na shekara mai zuwa. Sai aka mai dashi aro zuwa Serie C1 club Lumezzane. A ranar 25 ga watan Janairun 2011 ya tafi Gubbio a kan aro. Daud ya bar Italiya a watan Agustan 2013 ya koma kungiyar Budapest Honvéd Hungary.

Ƙwallayen ƙasa da ƙasa[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Size doesn’t matter for Ayub – The Star
  2. "Daud si ripete, la Juve piega il Parma" (in Italian). La Gazzetta dello Sport. 12 February 2009. Retrieved 14 March 2009.CS1 maint: unrecognized language (link)
  3. "AYUB DAUD" (in Italian). Calciomercato.it. 6 March 2009. Archived from the original on 9 March 2009. Retrieved 14 March 2009.CS1 maint: unrecognized language (link)
  4. "TMW VIAREGGIO – Juventus, Daud: una freccia bianconera" (in Italian). Juventus FC. 11 February 2009. Retrieved 14 March 2009.CS1 maint: unrecognized language (link)
  5. "JUVE-BOLOGNA 4–1: RIPRESA TRAVOLGENTE E L'INTER E' A −4" (in Italian). Calciomercato.it. 14 March 2009. Archived from the original on 16 March 2009. Retrieved 14 March 2009.CS1 maint: unrecognized language (link)