Baha'i

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Baha'i
Founded unknown value
Mai kafa gindi Bahá'u'lláh
Classification
Alamar Addinin Baha'i
Addinin Baha`i
gurin bautan mabiya Addinin BAHA`I

Baha'i,wani addini ne da ya fara a shekara ta 1800 daga wani mutum dan ƙasar Iran wanda ake kira Bahá'u'lláh wanda aka haifa a birnin Tehran na ƙasar ta Iran. Mabiya addinin Baha'i sunyi imani da Bahá'u'lláh a matsayin annabin Allah ne kuma yana koya wa mutane sanin Ubangiji da bauta masa.

Akidar mabiya Baha'i sun yarda da Ubangiji daya. Sun yarda Bahá'u'lláh yana dauko sakon Ubangiji zuwa ga halitta. Bahá'u'lláh yace bashine na farko ba wajen kawo sakon Ubangiji kuma bashi ne na karshe ba, yace shima kamar sauran Annabawa yake kamar Yesu, Muhammad, Ibrahim da Musa,sanann kuma shima kamar sauran jagiririn addinai yake irin su Krishna da Buddah. Yace yana kallon dukkannin su a matsayin Manzannin Ubangiji ne. An kuma haifi Bahá'u'lláh a gidan Musulmai ne kafin ya kafa nasa addinin mai kama da Musulunci. Mabiya Baha'i sun hakikance da babu wani Annabi bayan Bahá'u'lláh sai an samu shekaru 1000 bayan rasuwar sa.

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

Abdulbaha

An kafa addinin Baha'i ne a shekarar 1844 lokacin da wani mutum mai suna Bab yace yana samun sako daga Ubangiji. Yace lallai Ubangiji zai aikoshi da sako na addini ga Yan adan. Shidai bab asalinsa wani babban malamin Shi'a ne. Wannan ne ya fara addinin, mabiya wannan addini ana kiran su da Babi. Mutane da dama sun zamo Babi a ƙasar Iran, wadda ake kira da Farisa a wancan lokacin. Wannan kuma ya fusata Al'umar Musulmai dama hukumomin kasar ta Farisa. Suna kama Bab tare da kashe shi da mabiyansa da dama. Duk da faruwar wannan har yanzu akwai mabiya wannan addinin a kasar dama sauran kasashen duniya.

Bayan kashe Bab sai Bahá'u'lláh ya cigaba da tafiyar da jagorancin mabiyan su, daga bisani shima ya ayyana cewar yana samun sakon Ubangiji. Ya zamo sananne tsakanin mabiyan Baha'i. Bayan kashe Bab hukumomin Fasiya suka yi suma mabiyan baha'i sunyi kudirin kashe sarkin Farisa amma sai Bahá'u'lláh yace kada mabiyan suyi haka. A lokacin rayuwar sa a kurkuku Bahá'u'lláh yace yaga mala'ika yazo masa kuma ya fada masa cewa zaui zama mazo na Ubangiji, sannan kuma yayi masa bishara da Uabangiji zai kare shi kuma zai fitar dashi domin yaci gaba da aiwatar da wannnan addini. Kuma ba'a dade ba sai ya fita daga giadan yarin ammai sai gwamnatin ta Farisa ta kora shi inda ya koma birnin Bagadaza wanda a lokacin yan karkashin ikon daukar Usmaniyya ne.