Jump to content

Bahr el Gazel (yankin Chadi)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Bahr el Gazel


Wuri
Map
 13°38′35″N 16°29′31″E / 13.6431°N 16.4919°E / 13.6431; 16.4919
Ƴantacciyar ƙasaCadi

Babban birni Moussoro
Yawan mutane
Faɗi 361,100 (2019)
• Yawan mutane 7.08 mazaunan/km²
Labarin ƙasa
Yawan fili 51,000 km²
Altitude (en) Fassara 286 m
Bayanan tarihi
Ƙirƙira 2008
Bayanan Tuntuɓa
Lamba ta ISO 3166-2 TD-BG

Barh El Gazel[1][2][3][4][5][6] ( Larabci: منطقة بحر الغزال‎ , French: Région du Barh El Gazel )[5] yana ɗaya daga cikin yankuna 23 na kasar Chadi. Hakanan ana iya rubuta sunan yankin a matsayin Barh El Gazal[7] ko Bahr el Gazel.[8] Babban birninsa shine garin Moussoro.[4] An ƙirƙiro yankin a shekara ta 2008 daga tsohon Sashen Barh El Gazel na Yankin Kanem.[9]

Bayanan ƙasa[gyara sashe | gyara masomin]

Yankin ya yi iyaka da yankin Borkou daga arewa, yankin Batha a gabas, yankin Hadjer-Lamis a kudu, da yankin Kanem a yamma. Yankin dai galibi ciyayi ne, wanda ya haɗe cikin hamadar sahara a arewa.

Garuruwa[gyara sashe | gyara masomin]

Moussoro ne babban birnin yankin; wasu manyan garuruwan yankin sun haɗa da Chadra, Dourgoulanga, Michemiré da Salal.[10]

Alkaluma[gyara sashe | gyara masomin]

Bisa ga ƙidayar jama'a a shekarar 2009, yawan mutanen yankin ya kai dubu 260,865, kashi 46.3% daga cikin su mata ne. Matsakaicin girman iyali kamar na 2009 shine 5.90: 5.90 a cikin gidajen karkara da 5.80 a cikin birane. Jumillar gidaje 43,478: 38,160 a yankunan karkara da 5,318 a birane. Adadin makiyaya a yankin ya kai 126,855, kashi 32.7% na yawan jama'a. Akwai mutane 257,804 da ke zaune a gidaje masu zaman kansu. Akwai 111,278 da suka haura shekaru 18: 56,407 maza da 54,871 mata. Akwai ma'aikata 134,010 masu zaman kansu, 1.20 na yawan jama'a.[11]

Manyan kungiyoyin ƙabilanci sune Dazaga Toubou da Kanembu.[12]

Tattalin Arziki[gyara sashe | gyara masomin]

Yankin ne babban wurin noma a duk faɗin ƙasar, yana samar da auduga da gyaɗa, manyan abubuwan biya mafiya kawo kuɗaɗe na ƙasar. Akwai amfanin gona iri-iri na gida kamar shinkafa da ake nomawa a yankin.[13]

Gudanarwa[gyara sashe | gyara masomin]

Makiyaya a yankin

A matsayin wani ɓangare na raba mulki a watan Fabrairun 2003, an raba ƙasar bisa tsarin mulki zuwa yankuna, sassa, gundumomi da al'ummomin karkara. Lardunan da tun asali 14 ne aka sake faɗaɗa su a cikin yankuna 17. Gwamnonin da shugaban ƙasa ya naɗa ne ke gudanar da yankunan. Hakimai, waɗanda tun farko ke riƙe da nauyin kananan hukumomi 14, har yanzu suna riƙe da muƙaman kuma su ne ke da alhakin gudanar da kananan hukumomi a kowane yanki. Ana zaɓen mambobin majalisun ƙananan hukumomi ne duk bayan shekaru shida, yayin da hukumomin zartaswa ke zaɓen, a duk bayan shekaru uku.[14] Ya zuwa shekarar 2016, akwai yankuna 23 a ƙasar Chadi, wadanda aka raba bisa la'akari da yawan jama'a da kuma saukaka harkokin mulki.[15]

An raba yankin Barh El Gazel zuwa sassa biyu. kowane da aka jera tare da sunan babban birninsa ko babban garinsa ( shuga-lieu a Faransanci) da jerin ƙananan hukumomi ( sous-préfectures ).[4][5]

Duba kuma[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

 1. "Décret n° 1071/PR/PM/MAT/2010 du 13 décembre 2010". Présidence de la République du Tchad. 13 December 2010. Archived from the original on 18 December 2010.
 2. "Décret 11-530 2011-06-01 PR/PM/MCD/11: Décret fixant le nombre des conseillers municipaux des Communes chefs-leix des Régions et des Départements" [Decree fixing the number of municipal councilors of Chief towns of Regions and of Departments]. Légitchad (in French). Republique du Tchad [Republic of Chad]. 1 June 2011. Archived from the original on 1 September 2012.CS1 maint: unrecognized language (link)
 3. "List provisoire des candidats aux elections legislatives" [Provisional list of candidates for legislative elections] (PDF). JournalDuTchad.com (in French). Republique du Tchad - Commission Electorale Nationale Indépendante (CENI) [Republic of Chad - National Independent Electoral Commission]. Archived from the original (PDF) on 7 August 2012.CS1 maint: unrecognized language (link)
 4. 4.0 4.1 4.2 "Profil National du Tchad sur la gestion des produits chimiques, Troisieme Edition" [National Profile of Chad on Chemicals Management, Third Edition] (PDF). ESTIS.net (in French). Republique du Tchad - Ministere de l'Environnement et des Ressources Halieutiques [Republic of Chad - Ministry of Environment and Water Resources]. September 2009. Archived from the original on 1 March 2014.CS1 maint: unrecognized language (link)
 5. 5.0 5.1 5.2 "Décret 10-371 2010-04-02 PR/PM/2010: Décret portant désignation des Présidents des démembrements de la Commission Électorale Nationale Indépendante" [Decree appointing the presidents of branches of the Independent National Electoral Commission]. Légitchad (in French). Republique du Tchad [Republic of Chad]. 2 April 2010. Archived from the original on 24 February 2013.CS1 maint: unrecognized language (link)
 6. "Regions and departments of Chad (list and maps)". Office for the Coordination of Humanitarian Affairs (OCHA), United Nations. Retrieved 31 August 2012.
 7. "Deuxieme Recensement General de la Population et de l'Habititat (RGPH2, 2009)" [Second General Census of Population and Housing] (in French). Republique du Tchad - Institut national de la statistique, des études économiques et démographiques (INSEED). September 2009. Archived from the original (PDF) on 1 September 2012.CS1 maint: unrecognized language (link)
 8. "ISO 3166-2 Newsletter No. II-2" (PDF). ISO. 30 June 2010.
 9. "Ordonnance n° 002/PR/08 portant restructuration de certaines collectivités territoriales décentralisées" [Ordinance No. 002/PR/08 on restructuring of certain decentralized local authorities]. Government of Chad. 19 February 2008. Archived from the original on January 20, 2012.
 10. "Tchad : Région du Bahr-El-Gazal - Juin 2010" (PDF). UNOCHA. Retrieved 4 October 2019.
 11. "Census of Chad". National Institute of Statistical, Economic and Demographic Studies, Chad. 2009. Archived from the original on 21 November 2016. Retrieved 17 November 2016.
 12. "Languages of Chad". Ethnologue. Retrieved 27 September 2019.
 13. Hilling, David (2004). "Chad - Physical and Social Geography". Africa South of the Sahara 2004. Psychology Press. p. 218. ISBN 9781857431834.
 14. Republic of Chad Public Administration and Country profile (PDF) (Report). Department of Economic and Social Affairs (DESA), United Nations. 2004. p. 9. Archived from the original (PDF) on 14 June 2007. Retrieved 17 November 2016.
 15. Chad district map (PDF) (Report). Department of Field Support,Cartographic Section, United Nations. Retrieved 20 November 2016.