Bello Baƙo Ɗambatta
| mutum | |
|
| |
| Bayanai | |
| Jinsi | namiji |
| Ƙasar asali | Najeriya, jihar Kano da Afirka |
| Harsuna | Turanci da Hausa |
| Sana'a |
scientist (en) |
| Ilimi a |
University of Huddersfield (en) |
Bello Baƙo Ɗambatta, (an haife shi a ranar 15 ga watan Disamban shekarar 1950 a Kano, Jihar Kano, Nigeria)ɗan Najeriya ne masanin chemistry kuma mai kula da jami'a. Ya riƙe muƙamin shugaban jami’ar Bayero ta Kano daga shekara ta 1995 zuwa shekarar 1999.
Ilimi da aiki
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Ɗambatta a ranar 15 ga Disamban shekarar 1950 a cikin birnin Kano, Najeriya.[1] Ya fara karatunsa na gaba a Kaduna Polytechnic (1970-72), sannan ya koma Ingila, inda ya halarci Huddersfield Polytechnic (1972-74), Trent Polytechnic (1974-75), Jami'ar Bradford (1975-76), da Jami'ar Lancaster (1980-83).[1] Ya kammala digirinsa na uku a Jami'ar Lancaster, tare da rubutu mai taken Bincike game da polymerisations ɗin free-radical na tri-n-butyltin methacrylate da i-vinylimidazole.[2]
Ya zama malami a jami’ar Bayero ta Kano a shekarar 1978, kuma ya samu ƙarin girma, har ya kai cikakken farfesa a shekarar 1994.[1] Ya yi aiki a matsayin shugaban Sashen Chemistry daga 1991 zuwa 1995, kuma shi ne shugaban tsangayar kimiyya daga 1992 zuwa 1995.[1] Ya kasance mataimakin shugaban jami'ar Bayero daga shekarar 1995 zuwa 1999,[3] kuma shine farkon wanda malaman jami'ar suka zaɓa (gwamnatin tarayya ce ta naɗa mataimakan shugabannin da suka gabata).[4]
Ɗambatta ya zama fellow, wato babban mamba, na ƙungiyar sinadarai ta Najeriya a watan @Agustan shekarar 1996.[1]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 1.2 1.3 1.4 https://blerf.org/index.php/biography/dambatta-professor-bello-bako/
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-03-07. Retrieved 2023-03-07.
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-03-07. Retrieved 2023-03-07.
- ↑ https://web.archive.org/web/20170619095119/http://buk.edu.ng/sites/default/files/buktoday/bt_aug_2015.pdf