Bulugh al-Maram
Bulugh al-Maram | |
---|---|
Asali | |
Mawallafi | Ibn Hajar al-Asqalani |
Asalin suna | بلوغ المرام من أدلة الأحكام |
Online Computer Library Center | 39014805 |
Characteristics | |
Harshe | Larabci |
Muhimmin darasi | Shafi`iyya da Fiƙihu |
Bulūgh al-Marām min Adillat al-Aḥkām, Fassara: Cimma Manufa bisa dalilan farillai na al-Hafiẓ ibn Ḥajar al-'Asqalānī (1372 – 1448) littafin hadisi ne wanda ya shafi fikihu musamman a mazhabar Imam Shafi'i. Ana kiran wannan littafin a harshen Larabci da Aḥādith al-Aḥkam.[1]
Game da
[gyara sashe | gyara masomin]Littafin Bulugh al-Marām ya ƙunshi jimlar hadisai 1358. [2] A ƙarshen kowane hadisin da aka ruwaito a cikin Bulugh al-Marām, al-Hafiẓ ibn Hajar ya ambaci wanda ya ruwaito hadisin a asali. Bulūgh al-Marām ya haɗa da hadisai da aka ciro daga tushe masu yawa kamar su Saḥīḥ al-Bukhari, Sahih Muslim, Sunan Abu Dawud, Jami’ at-Tirmidhi, Sunan al-Nasāʾī, Sunan ibn Majah, Musnad Ahmad ibn Hanbal da sauransu dai.
Yana da banbance-banbance sai dai kuma dukkan hadisan da aka tattara a cikin littafin sun kasance ginshiƙin duk wasu hukunce-hukunce daga Mazhabar Shafi’i. Baya ga ambaton asalin kowane hadisi a cikin Bulugh al-Marām, Ibn Hajar ya kuma haɗa da kwatancen fassarar hadisin da ya zo daga mabambanta daban-daban. Saboda irin abubuwan da littafin ya kebanta da su na inganci, har yanzu ya kasance littafin hadisan da aka fi amfani da shi ba tare da la’akari da mazhabar ba.[3]
Babi-babi da ke cikin Littafin
[gyara sashe | gyara masomin]Babi 15 ne a cikin littafin:
- Babin tsarki
- Babin Sallah
- Babin Jana'iza
- Babin Zakka
- Babin Azumi
- Babin Kasuwanci
- Babin Aure
- Babin Jinaya
- Babin Haddodi
- Babin Jihadi
- Babin Abinci
- Babin rantse-rantse da alwashi
- Babin hukunci
- Babin Ƴanci
- Babin da ya tattara abubuwa
Bayanai
[gyara sashe | gyara masomin]- Al-Badar al-Tamām na al-Husayn ibn Muhammad al-Maghribi
- Subul al-Salam na Muhammad ibn Isma'il al-Amir al-San'āni, al-Badr al-Tamām.
Fassara
[gyara sashe | gyara masomin]- Bulugh al-Maram: biyan buƙatu bisa ga Shaidar farillai, Darus-Salam; Bugu na ɗaya (1996), ASIN : B000FJJURU
- Kinyarwanda translation: Kugera ku ntego : hashingiwe kuri gihamya z'amategeko y'idini ya Islam : Bulugh al maram : min adilatil ah'kam, Kigali: Maktabat al-qalam; (2019)
Watsawa
[gyara sashe | gyara masomin]- Bulugh al-Maram
Maɓallin waje
[gyara sashe | gyara masomin]Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Bulugh Al-Maram". www.kalamullah.com. Retrieved Apr 30, 2019.
- ↑ "بلوغ المرام من أدلة الأحكام • الموقع الرسمي للمكتبة الشاملة". shamela.ws.
- ↑ "Bulugh Al-Maram". Retrieved Apr 30, 2019.