Jump to content

Chimaobi Ebisike

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Chimaobi Ebisike
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

21 ga Afirilu, 2021 -
District: Aba North/Aba South 60
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

Rayuwa
Haihuwa Jihar Abiya, 9 Mayu 1978 (46 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƙabila Tarihin Mutanen Ibo
Harshen uwa Harshen, Ibo
Karatu
Harsuna Turanci
Harshen, Ibo
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Chimaobi Ebisike ɗan siyasan Najeriya ne, kuma ɗan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazaɓar Aba North/Aba ta Kudu a jihar Abia. [1] [2]

Aikin siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Ebisike ya kasance kwamishinan ayyuka na musamman a gwamnatin Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abia daga shekarun 2019 zuwa 2021. [3] Ya tsaya takarar ne a mazaɓar tarayya ta Aba North/Aba ta kudu a kan tikitin jam'iyyar People's Democratic Party, PDP bayan rasuwar Ossy Prestige ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar a shekarar 2021. Ebisike ya samu kuri’u 10,322 inda ya doke ‘yan takarar APC, Mascot Uzor Kalu wanda ya samu 3,674 da All Progressives Grand Alliance, APGA, Akaraka Destiny Nwagwu wanda ya samu kuri’u 1,554. [4]

Ebisike ya tsaya takarar tikitin komawa majalisar wakilai ta 10 a zaɓen da aka yi ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 a jam’iyyar PDP amma ya sha kaye. Ɗan takarar jam’iyyar Labour Party, LP Emeka Nnamani ya samu kuri’u 35,502 [5] yayin da Ebisike mai ci ya samu kuri’u 13,388 inda ya samu matsayi na uku a bayan ɗan takarar All Progressives Grand Alliance, APGA Alex Ikwecheghi wanda ya samu kuri’u 22,465 ya zo na biyu a zaɓen. [6]

  1. Ibe, Sam Obinna (2022-10-24). "I'm in politics to alleviate my constituents' suffering – Abia Reps member". Blueprint Newspapers (in Turanci). Retrieved 2023-05-01.
  2. Emeruwa, Chijindu (2021-03-31). "Abia re-run: PDP's Chimaobi Ebisike receives Certificate of Return". Daily Post Nigeria (in Turanci). Retrieved 2023-05-01.
  3. www.premiumtimesng.com https://www.premiumtimesng.com/regional/ssouth-east/358044-abia-gov-inaugurates-23-commissioners.html?tztc=1. Retrieved 2023-05-01. Missing or empty |title= (help)
  4. Ogbolu, George Oshogwe (2021-03-28). "Aba Bye-Election: PDP Defeats Orji Uzor Kalu's Brother". Naija News (in Turanci). Retrieved 2023-05-01.
  5. gloriaabiakam (2023-03-23). "2023 Elections: Labour Party Wave hits Abia, as Party takes Political Structure from PDP in the State". Federal Ministry of Information and Culture (in Turanci). Retrieved 2023-05-01.
  6. Umuahia, Linus Effiong (2021-03-28). "REPORTER'S DIARY: INEC Officials Sleeping On Duty, Over 480,000 Missing Voters and other tales from Aba". Daily Trust (in Turanci). Retrieved 2023-05-01.