Cutar huhu
Respiratory disease | |
---|---|
Micrograph of an emphysematous lung; emphysema is a common respiratory disease, strongly associated with smoking. H&E stain. | |
Specialty | Pulmonology |
Cututtukan numfashi, ko cututtukan huhu,[1] Cututtuka ne da ke shafar gabobi da tsoka - tissue wanda ke haifar da wahalar numfashi ga dabbobi masu shakar iska. Sun hada da yanayi na cututtukan hanyoyin numfashi ciki har da trachea, bronchi, bronchioles, alveoli, pleurae, pleural cavity, jijiyoyi da gabobin numfashi. Cututtukan na numfashi sun hada da masu sauki ko wanda za'a iya shawo kansu cikin sauki, irin su mura, majina da tari, da kuma pharyngitis zuwa cututtuka masu barazana ga rayuwar dan-Adam irin su asthma da sankarar huhu, tarin fuka, asma mai tsanani, ciwon huhu,[2] da cututtuka masu tsanani na numfashi kamar COVID-19.[3] Ana iya rarraba cututtuka na numfashi ta hanyoyi daban-daban, kamar dangane da gabobin jiki ko nama da ke kamuwa da cutar, t ko kuma ta alamomin da dalilan cutar.
Ana kiran karatun nazarin cututtukan da suka shafi numfashi da pulmonology. Likitan da ya kware akan cututtukan numfashi ana kiran shi da likitan huhu pulmonologist, ƙwararren likitan ƙirji, ƙwararrun likitancin numfashi, likitan numfashi ko ƙwararren likitancin thoracic.
Cututtukan da ke toshe huhu
[gyara sashe | gyara masomin]Asthma, Chronic bronchitis, Cutar huhu na yau da kullun (COPD), dukkanninsu cututtuka ne da ke hana numfashi ta hanyar toshe hanyoyin iska. Wannan suna iyakance iskar da ke shiga gabar alveoli saboda toshewar hanyar iska (bronchial tree) a dalilin kumburi. Ana iya gano cututtukan da ke toshe huhu ta hanyar alamomin cutar da kuma awo na auna cutar huhu irinsu spirometry. Ana iya magance mafi yawancin wadannan cututtuka ta hanyar rage cudanya da abubuwan da ke tayar da su (kamar kwayoyin kura da Shan taba), da kuma alamomi irinsu bronchodilators, da kuma kore kumburi (kamar ta hanyar corticosteroids) a lokacin da cutar yayi tsanani.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Lung diseases". MeSH.nlm.nih.gov. Retrieved 14 August 2019.
- ↑ Sengupta N, Sahidullah M, Saha G (August 2016). "Lung sound classification using cepstral-based statistical features". Computers in Biology and Medicine. 75 (1): 118–29. doi:10.1016/j.compbiomed.2016.05.013. PMID 27286184.
- ↑ "COVID-19 and vascular disease". EBioMedicine. 58: 102966. August 2020. doi:10.1016/j.ebiom.2020.102966. PMC 7438984. PMID 32829782.