Dahiru Mangal
| Rayuwa | |
|---|---|
| Haihuwa | Jahar Katsina, 1957 (68/69 shekaru) |
| ƙasa | Najeriya |
| Sana'a | |
| Sana'a | ɗan kasuwa |
Dahiru Barau Mangal (an haife shi ne a ranar uku (3) ga watan Agustan, shekara ta alif dubu daya da dari tara da hamsin da bakwai 1957A.c) dan kasuwa ne a Najeriya. Shi ne ya kafa kamfanin jiragen sama na Max Air a shekara ta 2008.[1]
Rayuwar farko.
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Dahiru Barau Mangal a cikin jihar Katsina ga dangin Alhaji Barau Mangal. Ya girma tare da 'yan'uwansa Alhaji Bashir Barau Mangal, Alhaji Hamza Barau Mangal, Hajiya Zulai Barau Mangal, Hajiya Yar Goje da Mahaifiyarsa Hajiya Murjanatu Barau Mangal a Katsina. Ya fara kasuwancinsa a matsayin direban babbar mota kuma daga baya ya cigaba da sayen motoci domin haya.
Ayyuka.
[gyara sashe | gyara masomin]Mangal shi ne wanda ya kafa kamfanin jiragen sama na Max Air, wanda yake jagorantar kamfanin jirgin sama na cikin gida, yanki da kuma na kasashen duniya. Sauran bangarorin da ya sa hannun jari sun hada da sufuri, mai da gas da kuma gini. Ya kasance Babban Daraktan Kamfanin MRS Oil Nigeria Plc wanda ya yi murabus a ranar 17 ga watan Nuwamban, shekara ta 2017.[2]
Shi babban mai hannun jari ne a kamfanin na Oando Plc inda ya samu sabani da shugabannin kamfanin wanda ya kai ga dakatar da kasuwancin Oando a kasuwar kasuwannin hada-hadar hannayen jari ta Legas da ta Johannesburg. Rikicin ya samo asali ne a shekara ta dubu biyu da Sha bakwai (2017) lokacin da Mangal Yana tare da wani kamfanin mai suna Gabriel Volpi da ke sarrafa harsashi suka rubuta takardar koke ga hukumar musayar hannayen jari ta Najeriya kan zargin almubazzaranci da kudi da shugabannin Oando suka yi, wanda hakan ya sa hukumar ta binciki lamarin har da yiwuwar cinikin mai ciki. An warware rikicin ne ta hanyar sa hannun Mai Martaba Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi a watan Janairun Shekara ta 2018.
Ɗahiru Mangal, fitaccen ɗan kasuwa kuma Attajirin mai dukiya da ta kai biliyoyin daloli kuma ɗaya daga cikin Attajiran masu kuɗi 10 a Najeriya, mun haɗa muku abubuwan da ya dace ku sani game da shi. Dahiru Barau Mangal, fitaccen ɗan kasuwa ne ɗan asalin Najeriya, ya kafa kamfanin sufurin jiragen sama na Max Air a shekarar 2008, kamar yadda Newwire ta tattaro. Mangal, mamallakin Max Air, kamfanin sufurin jiragen sama da ke jan ragamar sufuri a cikin gida da ƙasa da ƙasa, ya zuba hannun jari a wasu wuraren da suka haɗa da tafiye-tafiye, Mai da Gas, da gine-gine. [3]
Matar aure da 'ya'ya Kasancewarsa Musulmi, Mangal yana da aure kuma Allah ya albarkace shi da samun ƴaƴa da dama. A shekarar 2010 an zargi Attajirin da haihuwa kafin shafa fatiha. [4]
Kyauta
[gyara sashe | gyara masomin]Mangal sanannen dan agaji ne wanda ke ba da taimako da tallafi ga dalibai, mutanen da ke da nakasa da kuma ’yan gudun hijirar da ke cikin gida da rikici ya shafa a Nijeriya. Haka nan yana raba abinci a yankin Arewacin Najeriya da suka hada da Katsina, Kano, Kaduna da kauyuka a kowace rana.Dahiru ya kasance daya daga cikin masu arzikin da ke kiyayewa wurin bayar da zakka a lokacin Satan ramadana
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]