Donald Etiebet

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Donald Etiebet
Gwamnan jihar Cross River

Oktoba 1983 - Disamba 1983
Clement Nyong Isong - Dan Archibong
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

Rayuwa
Cikakken suna Donald Dick Etiebet
Haihuwa Ikot Ekpene, 1934
ƙasa Najeriya
Mutuwa 21 ga Yuli, 2015
Karatu
Harsuna Turanci
Ibibio
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa All Nigeria Peoples Party

Cif Donald Dick Etiebet (1934 - 21 Yuli 2015) ɗan siyasan Najeriya ne wanda ya kasance sanata a jamhuriya ta biyu a Najeriya (1979 - 1983). Daga nan ne aka zabe shi gwamnan jihar Cross river tare da goyon bayan shugaban majalisar dattawa na lokacin Joseph Wayas da kuma Sanata Joseph Oqua Ansa duk sun kasance yan adawa da gwamna mai ci a lokacin Clement Isong, Fidelis Ikogo Nnang shi ne mataimakinsa, yana rike da wannan ofishin daga Oktoba zuwa Disamba 1983, lokacin da juyin mulkin soja ya kawo Janar [[Muhammadu Buhari ]kan karagar mulki.

Rayuwar farko da Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Etiebet a Ikot Ekpene a Jihar Akwa Ibom, Dan kabilar Annang. Ya auri Nike Maryam Agunbiade, daga Jihar Oyo a shekarar 1991, kuma suna da ‘ya’ya uku.[1] Kanensa Donatus ("Don") Obot Etiebet ya rike mukamin Ministan Makamashi a majalisar ministocin Ernest Shonekan na kankanin lokaci, inda ya ci gaba da rike mukamin bayan wancan, gwamnatin daJanar Sani Abacha ya tsigeshi, kuma daga baya ya zama dan takarar PDP na gwamnan jihar Akwa Ibom a shekarar 2007. [2]

Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan komawar dimokradiyya a 1999, Etiebet ya kasance shugaban jam'iyyar United Nigeria People's Party (UNPP), wacce daga baya ta hade da All People's Party (APP) wadda takoma jam'iyyar All Nigeria People's Party . (ANPP)An nada Etiebet Amatsayin mataimakin shugaban jam’iyyar ANPP ta Kudu. Daga baya Etiebet ya zama shugaban jam'iyyar ANPP na kasa bakidaya. Da yake magana da yawun jam’iyyar ANPP a watan Maris na shekarar 2003, Etiebet ya ce kamata ya yi a fitar da sakamakon zabe a rumfunan zabe kuma wakilan jam’iyyun siyasa su sanya hannu a kai a matsayin hanyar dakile tashe-tashen hankula a lokacin zabe. [3]

Shugaban majalisar koli[gyara sashe | gyara masomin]

A matsayinsa na shugaban majalisar koli ta dattawa a jihar Akwa Ibom, a watan Maris na shekarar 2004, Etiebet ya jagoranci tawagar shugabanni daga jihar Akwa Ibom domin ganawa da shugaba Olusegun Obasanjo, inda suka tattauna kan dokar kawar da tsarin bakin teku wadda take raba kudaden shigar man fetur.[4]

Mutuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Mista Etiebet,ya mutu ranar 21 ga watan Yuli, 2015, an yi jana’izar shi a gidan iyalansa da ke Oruk Anam, a karamar hukumar Oruk Anam ta jihar akwa ibom.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]