Dunni Olanrewaju
Dunni Olanrewaju | |
---|---|
Haihuwa |
December 2, 1960 Akinyele, Oyo State, Nigeria |
Wasu sunaye | Opelope Anointing |
Dan kasan | Nigerian |
Aiki |
|
Shekaran tashe | 1998–present |
Dunni Olanrewaju an haife shi a watan (Disamba 2, 1960), wanda aka fi sani da Opelope Anointing mawaƙin bishara ne na Najeriya, marubuci kuma mai wa’azu a gidan telebijin. [1] [2] [3]
Rayuwar farko
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Opelope Anointing a ranar 2 ga watan Disamba shekara ta 1960 a Akinyele, karamar hukumar a jihar Oyo, kudu maso yammacin Najeriya a cikin dangin Kirista na marigayi Ishaya da Deaconess Elizabeth Olaniyi.[4]
Ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]Dunni ta fara karatun firamare a wani kauye mai suna Sannu kafin daga bisani ta wuce makarantar sakandaren zamani ta Elekuro da ke Ibadan amma ta bar makarantar Ejigbo da ke jihar Legas, inda a karshe ta bar karatun ta na mai da hankali kan wakar bishara. [5]
Sana'a
[gyara sashe | gyara masomin]Album dinta na farko mai suna Adun-Igbeyawo ya fito ne a shekara ta 1998 amma ta shahara da taken albam din Opolope Anointing, wakar da ta rubuta kuma ta nada a rana daya. [6] Ta sami daukakarta, "Opelope Anointing" daga wannan kundin. [7] Ta kaddamar da albam din ta na 20 a ranar 26 ga watan Oktoba, shekara ta 2014 kuma a wurin taron akwai mashahuran mawakan bisharar Najeriya, Joseph Adebayo Adelakun, Tope Alabi, Bola Are da Funmi Aragbaye . [8] A cikin shekara ta 2010, ta kafa "Opelope Anointing Foundation (OPAF), ƙungiyoyin agaji, Ƙungiyoyi masu zaman kansu. [9]
Rayuwa ta sirri
[gyara sashe | gyara masomin]A watan Mayun na shekara ta 2013, 'yarta Ibironke ta auri Olawunmi kuma an yi bikin aure a Isolo a jihar Legas . [10] Bakin da suka halarta sun hada da Bola Are, Funmi Aragbaye da kuma Mega 99 wadanda suka taka rawa a wurin taron. [11]
Hotuna
[gyara sashe | gyara masomin]- Opelope Anointing (1998)
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]- List of Nigerian gospel musicians
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ A. "Opelope Anointing Set For Ado-Odo :: P.M. News Nigeria". Africanewshub.com. Archived from the original on February 8, 2016. Retrieved February 7, 2016.
- ↑ "Musician Opelope Anointing Unveils 20th Album". P.M. NEWS Nigeria. October 17, 2014. Retrieved February 7, 2016.
- ↑ "Ayewa, Opelope Anointing, Foluke Awoleye to grace CAC Transfiguration Zone 26 years anniversary". Archived from the original on April 2, 2015. Retrieved March 15, 2015.
- ↑ "Day Obesere performed with me in London - Dunni-Opelope Anointing". Archived from the original on April 2, 2015. Retrieved March 15, 2015.
- ↑ "Amazing story of God's greatness in my life – Opelope Anointing | Newswatch Times". Mynewswatchtimesng.com. Archived from the original on February 8, 2016. Retrieved February 7, 2016.
- ↑ "I wrote and recorded Opelope Anointing in one day". M.thenigerianvoice.com. March 1, 2005. Retrieved February 7, 2016.
- ↑ "Habila Home for Fidelity Creative Writing Workshop, Articles". Thisday Live. July 16, 2010. Archived from the original on April 2, 2015. Retrieved February 7, 2016.
- ↑ "Opelope Anointing shines in 3-In-1 event". Archived from the original on March 15, 2015. Retrieved March 15, 2015.
- ↑ "Amosun, Fashola, storm Ogun State for Opelope Anointing". The Sun News. Archived from the original on April 2, 2015. Retrieved March 15, 2015.
- ↑ "Celebrities Regroup at Opelope Anointing Daughter's wedding – YouNewsng". Younewsng.com. June 1, 2013. Archived from the original on October 5, 2018. Retrieved February 7, 2016.
- ↑ "Mega 99 shows class at Opelope Anointing bash – the Punch – Nigeria's Most Widely Read Newspaper". Archived from the original on 2013-06-08.