Elizabeth Afoley Quaye

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Elizabeth Afoley Quaye
Member of the 7th Parliament of the 4th Republic of Ghana (en) Fassara

7 ga Janairu, 2017 -
District: Krowor Constituency (en) Fassara
Election: 2016 Ghanaian general election (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Nungua, 1 Nuwamba, 1970 (53 shekaru)
ƙasa Ghana
Karatu
Makaranta University of Ghana diploma (en) Fassara
Central University (en) Fassara Digiri a kimiyya : agribusiness (en) Fassara
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa, minista da Manoma
Imani
Addini Kiristanci
Jam'iyar siyasa New Patriotic Party

Elizabeth Afoley Quaye (an haife ta a shekara ta 1970), a halin yanzu ita ce ƴar majalisa mai wakiltar mazaɓar Krowor a yankin Greater Accra Ghana. Ita ce kuma ministar kiwon kifi.[1]

Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

Elizabeth tana da Digiri na ɗaya a fannin, Agribusiness daga Central University College. Ta samu takardar shaidar kammala aikin noma ta ƙasa a Jami'ar Ghana, sannan ta samu satifiket na shaidar aikin gona daga Kwalejin Aikin Noma ta Kwadaso.[2]

Sana'a[gyara sashe | gyara masomin]

Elizabeth ta yi aiki tare da Ma'aikatar Abinci da Noma a matsayin babbar Jami'ar Samar da Abinci na tsawon shekaru 20. Ita ce ƴar majalisa mai wakiltar mazaɓar Krowor, kuma ita minista ce a fannin kiwo da kamun kifi.[2]

Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Afoley Quaye ta tsaya takara kuma ta lashe zaɓen majalisar dokoki mai wakilta mazaɓar Krowor a ƙarƙashin jam'iyar New Patriotic Party a cikin yankin, Greater Accra a shekara ta 2015. A kuma lokacin babban zaɓen Ghana na 2016, ta lashe wannan kujera ta majalisar dokoki ta zama ƴar majalisa mai wakiltar mazaɓar Krowor. Ta fafata da wasu ƴan takara su uku, wato Agnes Naa Momo Lartey na National Democratic Congress, Hugo Kofi Huppenbauer na jam'iyyar Progressive People's Party da Amartey Fanny na jam'iyyar Convention People's Party . Afoley Quaye ta samu nasarar lashe zaɓen ne da ƙuri'u 32,463 daga cikin kuri'u 63,555 da aka kaɗa, wanda ta ke wakiltar kashi 51.08 na jimillar kuri'un da aka kaɗa.[3]

Rashin nasara[gyara sashe | gyara masomin]

Ta fafata ne a babban zaɓen Ghana na 2020 a matsayin ƴar takarar majalisar dokoki ta jam'iyyar, New Patriotic Party kuma ta sha kashi a hannun, Agnes Naa Momo Lartey ta jam'iyyar, National Democratic Congress wacce ita ma ta fuskanta a zaɓen 2016 (NDC).[4]

Rayuwa ta sirri[gyara sashe | gyara masomin]

Ta yi aure ta na da ƴaƴa huɗu. An bayyana ta a matsayin Kirista.[5]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Mensah, Kent. "PROFILES: Akufo-Addo reveals names of 11 more ministers". starrfmonline. STARRFMONLINE. Archived from the original on 15 January 2017. Retrieved 15 January 2017.
  2. 2.0 2.1 Segbefia, Lawrence (12 January 2017). "Elizabeth Quaye nominated for Ministry of Fisheries & Aquaculture". Citifmonline. citifmonline. Retrieved 15 January 2017.
  3. FM, Peace. "Ghana Election 2016 Results - Krowor Constituency". Ghana Elections - Peace FM. Retrieved 2019-03-09.
  4. "Fisheries Minister, Elizabeth Afoley Quaye loses Krowor seat". Graphic Online (in Turanci). Retrieved 2020-12-10.
  5. "Ghana MPs - MP Details - Afoley, Quaye Elizabath". ghanamps.com. Retrieved 2019-03-09.