Jump to content

Emmanuel Osodeke

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Emmanuel Osodeke
Ɗan Adam
Bayanai
Jinsi namiji
Ƙasar asali Najeriya
Wurin haihuwa Delta
Harsuna Turanci da Pidgin na Najeriya
Sana'a researcher (en) Fassara da university teacher (en) Fassara
Mai aiki Jami'ar Jihar Delta, Abraka da Jami'ar Calabar
Ilimi a Jami'ar jihar Riba s, Jami'ar Ibadan da Michael Okpara University of Agriculture
Academic major (en) Fassara soil science (en) Fassara
Hair color (en) Fassara black hair (en) Fassara
Mamba na Haɗakar Ƙungiyoyin Ma'aikatun Jami'o'i
Personal pronoun (en) Fassara L485

Emmanuel Victor Osodeke Farfesa ne na Kimiyyar Ƙasa na Najeriya a Jami'ar Aikin Noma ta Michael Okpara, Umudike,[1] wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar malaman jami'o'i ta ƙasa.[2][3] Ya taɓa zama mataimakin shugaban ƙungiyar a wa'adin da ya gabata.[2]

Rayuwar farko da ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Osodeke a Kokori, ƙaramar hukumar Ethiope ta gabas ta jihar Delta. Ya yi karatun BSc a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Ribas a cikin shekarar 1987, sannan kuma ya yi digirin digirgir a Jami’ar Ibadan a cikin shekarar 1989. Ya samu Diploma a fannin Agro-meteorology a Cibiyar Nazarin Yanayin Ƙasa ta Isra’ila a shekarar 1994, sannan a shekarar 2002, ya samu PhD a Jami’ar Aikin Gona ta Michael Okpara da ke Umudike.[4]

Sana'a[gyara sashe | gyara masomin]

Osodeke malami ne a Jami’ar Jihar Delta, Abraka, ya kuma kasance shugaban ƙungiyar malaman jami’o’i a Jami’ar noma ta Michael Okpara, Umudike. Shi malami ne mai ziyara a Jami'ar Calabar da Jami'ar Cape Cost, Ghana.[4] A ranar 30 ga watan Mayun 2021 an zaɓe shi shugaban ƙungiyar malaman jami'o'i ta ƙasa.[5][6]

Rayuwa ta sirri[gyara sashe | gyara masomin]

Osodeke ya auri Onome Osodeke kuma suna da ƴaƴa huɗu.[4]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://thenationonlineng.net/emmanuel-osodeke-in-the-eye-of-the-storm/
  2. 2.0 2.1 "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-04-01. Retrieved 2023-04-01.
  3. https://punchng.com/osodeke-emerges-new-asuu-president/
  4. 4.0 4.1 4.2 https://www.bbc.com/pidgin/tori-57306285
  5. https://www.premiumtimesng.com/news/headlines/464669-breaking-asuu-elects-new-president.html?tztc=1
  6. https://www.vanguardngr.com/2021/05/breaking-as-biodun-ogunyemi-bows-out-emmanuel-osodeke-emerges-new-asuu-president/