Enioluwa Adeoluwa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Enioluwa Adeoluwa (an haifeshi ranar 6 ga watan Yuli 1999), ɗan Najeriya ne kuma daraktan fina-finai,[1] mai magana da yawun jama'a, marubuci kuma ƙwararren kakaki.[2][3] Akan kira shi a matsayin darakta mai karancin shekaru a Najeriya, bayan an ba shi kyautar 'fitaccen darakta' da aka bashi a taron bikin Nigerian Universities Theatre Arts Festival, 2019.[1]

Kuruciya da Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Adeoluwa a ranar 6 ga watan Yulin, a shekarar 1999, a Akure, Jihar Ondo, Najeriya, ga iyalin mutum 3 na Farfesa Femi da Bola.[1] Ya yi karatunsa na firamare a makarantar firamare ta Cabataf, sannan ya yi makarantar Preston international ya samu shaidan kammala karatun sakandire sannan ya kammala digirinsa a jami’ar jihar Ekiti.[1]

Sana'a[gyara sashe | gyara masomin]

Adeola ƙwararre ne a fannin magana, marubuci, ƙwararren mai shirya kwalliya da ado don bikin aure ko harkokin finafinai, kuma ƙwararren a ɓangaren sadarwa, kuma ƙwararren daraktan fina-finai kuma mai tasirin kyan gani a Najeriya.[4] Shi ne mai watsa shiri na Late Night Show Tare da Eni.[3]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 1.2 1.3 "Enioluwa Adeoluwa". IMDb. Retrieved 2022-06-15.
  2. "Enioluwa Adeoluwa Biography, Age, Net Worth, Girlfriend, Parents, Wiki & University". Thenaijafame Blog. Retrieved 2022-06-15.
  3. 3.0 3.1 "'Lipgloss Boy' Enioluwa Adeoluwa Brings Beauty to Nigeria". PAPER. 2022-03-08. Retrieved 2022-06-15.
  4. "How Beauty Boy, Enioluwa Adeoluwa, Is Shattering the Expectations of Masculinity In Nigeria". OkayAfrica. 2021-10-19. Retrieved 2022-06-15.