Fadar Shugaban Ƙasa ta Haramain

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Fadar Shugaban Ƙasa ta Haramain
Bayanai
Ƙasa Saudi Arebiya
Shafin yanar gizo gph.gov.sa

Babban Fadar Shugaban Kasa ta Haramain ( Larabci: الرئاسة العامة لشؤون المسجد الحرام و المسجد النبوي‎ ) Hukuma ce ta gwamnatin Saudiyya da ke da alhakin rayawa da gudanar da wuraren ibadar Musulunci na Masallacin Harami da Masallacin Nabawi, da sassa na addini, fasaha da gudanarwa. An kafa hukumar ne a ranar 8 ga watan Mayun shekarar, 2012 bisa umarnin sarki Abdullah na Saudiyya. Hukumar da ke da Shelkwata a Masallacin Harami na Makkah, Shugaban Hukumar ne ke kula da hukumar, shi kuma sarki ne yake naɗa shi.

Shugaban hukumar mai ci a yanzu Abdul-Rahman al-Sudais limamin masallacin al-Haram, wanda aka naɗa shi a matsayin shugaban hukumar a ranar da aka kafa hukumar, wanda Sarki Salman na Saudiyya ya sake sabunta wa'adinsa har sau biyu.

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

An kafa hukumar shugabancin ne a ranar 8 ga watan Mayu shekarar, 2012 bisa umarnin sarki Abdullah na Saudi Arabia, wanda kuma ya naɗa Abdul-Rahman al-Sudais a matsayin shugabanta. Sarki Salman na Saudiyya ya sake naɗa shi muƙamin har sau biyu, a shekarar, 2016 da kuma 2020 kamar yadda har yanzu shine shugaban ta.

Gudanarwa[gyara sashe | gyara masomin]

Hukumar tana kula da wasu sassa da dama da ke kula da wasu ɓangarori daban-daban na masallatan biyu, kamar Masana'antar Kiswah. Hukumar kula da harkokin masallacin Annabi ne ke gudanar da ayyukan masallacin Nabawi, ƙaramar hukumar ta Haramain.

Sarkin Saudiyya shine yake naɗa shugaban hukumar na tsawon shekaru 4 .