Salman bin Abdulaziz Al Saud
Appearance

Salman bin Abdulaziz Al Saud [1] an haife shi a ranar 31 ga watan Disamba shekara ta alif dubu daya da dari tara da talatin da biyar (1935)) shi ne Sarkin Saudiyya, Mai kula da Masallatai Masu Tsarki Guda Biyu tun daga shekarar 2015. Ya kasance Ministan Tsaro tun daga shekarar 2011, kuma ya kasance Gwamnan Lardin Riyadh daga alif dubu daya da dari tara da sittin da uku(1963) zuwa shekarar 2011.[2]



Salman ya zama sarki ne a ranar 23 ga watan Janairun shekara ta 2015 bayan mutuwar dan uwansa, Sarki Abdullah. A matsayin Sarki na Bakwai, cikakkun 'yan uwansa sun haɗa da sarki Fahd, da manyan sarakunan Sultan da Nayef.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Larabci: سلمان ابن عبد العزيز آل سعود, Salmān bin ʻAbd al-ʻAzīz Āl Saʻūd, Najdi Arabic pronunciation: [sælˈmæːn ben ˈʢæbd ælʢæˈziːz ʔæːl sæˈʢuːd]
- ↑ "9/11 Commission interview with Saudi Prince Bandar released".