Farida Jalal

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Farida Jalal
Rayuwa
Haihuwa 2 Nuwamba, 1985 (38 shekaru)
Sana'a
Sana'a ɗan wasan kwaikwayo

Farida Jalal (An haife ta ranar 2 ga watan Nuwamba, shekara ta alif ɗari tara da tamanin da biyar1985) na Miladiyya. A birnin Katsina. Ƴar wasan fim ce a masana'antar fina-finan Arewacin Najeriya da aka fi sani da Kannywood.[1]

Rayuwar farko da ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Farida Jallal ne a ranar 2 ga watan Nuwamba, 1985 a birnin Katsina, Jihar Katsina. Farida ta taso ne kuma ta yi karatu a jiharta ta Katsina inda daga baya ta koma jihar Kano ta fara sana’ar fim a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood.[2]

Sana'a[gyara sashe | gyara masomin]

Farida ta shiga harkar fim ne a shekarar 2002 inda ta fito a manyan fina-finan masana’antu na lokacin kamar Yakana, Sansani da Madadi. An dakatar da Jaruma Farida Jallal daga yin fim na wasu lokuta saboda hana wasu jaruman fina-finai da gwamnatin jihar Kano ta yi.[3] A Shekarar 2019, Farida har ta sake fitowa a Kannywood.[4] A lokacin ta bayyana cewa ta dawo harkar fim har ma ta sanar da cewa nan ba da daɗewa ba za ta fitar da fina-finanta. A wata hira da ta yi da BBC Hausa, Farida ta bayyana cewa har yanzu ana cin moriyarta a masana'antar Kannywood.[5] A cikin wata hira da jaruma Farida Jallal ta bayyana cewa a halin yanzu tana mai da hankali kan waƙoƙin Bisharar Musulunci.[6][7][8]

Fina-finai[gyara sashe | gyara masomin]

Farida Jalal ta zayyano waɗansu finafinai da tayi. Sun haɗa da;

  • Sansani
  • Yakana
  • Raga
  • Jan Kunne
  • Farashi
  • Dan Zaki
  • Lugga
  • Tutarso
  • Namshaza
  • Gidauniya
  • Kumbo.

Da sauransu da dama a cewar ta.[9]

Rayuwa ta sirri[gyara sashe | gyara masomin]

Farida tayi aure ta haifi ƴaƴa biyu, amma ɗaya daga cikin ‘ya’yanta ya rasu. Farida bata da aure a halin yanzu.[ana buƙatar hujja]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Opera News Detail". lucky-wap-ams.op-mobile.opera.com. Retrieved 2022-04-23.
  2. "Har yanzu ba a dena yayinmu ba, Tsohuwar jarumar Kannywood - Farida Jalal". HausalLoaded.Com (in Turanci). 2022-04-22. Retrieved 2022-04-23.
  3. "The 'second coming' of Kannywood". A Tunanina... (in Turanci). 2011-06-26. Retrieved 2022-04-23.
  4. "Farida Jalal Ta Dawo Fim Ne ?". HausalLoaded.Com (in Turanci). 2019-10-03. Retrieved 2022-04-23.
  5. "...Daga Bakin Mai Ita tare da Farida Jalal". BBC News Hausa. 2022-04-21. Retrieved 2022-04-23.
  6. "Har yanzu ba a dena yayinmu ba, Tsohuwar jarumar Kannywood, Farida Jalal". HausaDrop.com (in Turanci). 2022-04-21. Retrieved 2022-04-23.[permanent dead link]
  7. Blueprint (2021-12-24). "I have no regrets going into Islamic songs – FARIDA JALAL". Blueprint Newspapers Limited (in Turanci). Retrieved 2022-04-23.
  8. "Why I ventured into Islamic gospel – Farida Jalal". Daily Trust (in Turanci). 2021-09-11. Retrieved 2022-04-23.
  9. https://dailytrust.com/why-i-ventured-into-islamic-gospel-farida-jalal