Farida Jalal
Farida Jalal | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 2 Nuwamba, 1985 (38 shekaru) |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan wasan kwaikwayo |
Farida Jalal (An haife ta ranar 2 ga watan Nuwamba, shekara ta alif ɗari tara da tamanin da biyar1985) na Miladiyya. A birnin Katsina. Ƴar wasan fim ce a masana'antar fina-finan Arewacin Najeriya da aka fi sani da Kannywood.[1]
Rayuwar farko da ilimi[gyara sashe | gyara masomin]
An haifi Farida Jallal ne a ranar 2 ga watan Nuwamba, 1985 a birnin Katsina, Jihar Katsina. Farida ta taso ne kuma ta yi karatu a jiharta ta Katsina inda daga baya ta koma jihar Kano ta fara sana’ar fim a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood.[2]
Sana'a[gyara sashe | gyara masomin]
Farida ta shiga harkar fim ne a shekarar 2002 inda ta fito a manyan fina-finan masana’antu na lokacin kamar Yakana, Sansani da Madadi. An dakatar da Jaruma Farida Jallal daga yin fim na wasu lokuta saboda hana wasu jaruman fina-finai da gwamnatin jihar Kano ta yi.[3] A Shekarar 2019, Farida har ta sake fitowa a Kannywood.[4] A lokacin ta bayyana cewa ta dawo harkar fim har ma ta sanar da cewa nan ba da daɗewa ba za ta fitar da fina-finanta. A wata hira da ta yi da BBC Hausa, Farida ta bayyana cewa har yanzu ana cin moriyarta a masana'antar Kannywood.[5] A cikin wata hira da jaruma Farida Jallal ta bayyana cewa a halin yanzu tana mai da hankali kan waƙoƙin Bisharar Musulunci.[6][7][8]
Fina-finai[gyara sashe | gyara masomin]
Farida Jalal ta zayyano waɗansu finafinai da tayi. Sun haɗa da;
- Sansani
- Yakana
- Raga
- Jan Kunne
- Farashi
- Dan Zaki
- Lugga
- Tutarso
- Namshaza
- Gidauniya
- Kumbo.
Da sauransu da dama a cewar ta.[9]
Rayuwa ta sirri[gyara sashe | gyara masomin]
Farida tayi aure ta haifi ƴaƴa biyu, amma ɗaya daga cikin ‘ya’yanta ya rasu. Farida bata da aure a halin yanzu.[ana buƙatar hujja]
Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]
- ↑ "Opera News Detail". lucky-wap-ams.op-mobile.opera.com. Retrieved 2022-04-23.
- ↑ "Har yanzu ba a dena yayinmu ba, Tsohuwar jarumar Kannywood - Farida Jalal". HausalLoaded.Com (in Turanci). 2022-04-22. Retrieved 2022-04-23.
- ↑ "The 'second coming' of Kannywood". A Tunanina... (in Turanci). 2011-06-26. Retrieved 2022-04-23.
- ↑ "Farida Jalal Ta Dawo Fim Ne ?". HausalLoaded.Com (in Turanci). 2019-10-03. Retrieved 2022-04-23.
- ↑ "...Daga Bakin Mai Ita tare da Farida Jalal". BBC News Hausa. 2022-04-21. Retrieved 2022-04-23.
- ↑ "Har yanzu ba a dena yayinmu ba, Tsohuwar jarumar Kannywood, Farida Jalal". HausaDrop.com (in Turanci). 2022-04-21. Retrieved 2022-04-23.[permanent dead link]
- ↑ Blueprint (2021-12-24). "I have no regrets going into Islamic songs – FARIDA JALAL". Blueprint Newspapers Limited (in Turanci). Retrieved 2022-04-23.
- ↑ "Why I ventured into Islamic gospel – Farida Jalal". Daily Trust (in Turanci). 2021-09-11. Retrieved 2022-04-23.
- ↑ https://dailytrust.com/why-i-ventured-into-islamic-gospel-farida-jalal
- CS1 Turanci-language sources (en)
- All articles with dead external links
- Articles with dead external links from November 2022
- Articles with invalid date parameter in template
- Articles with permanently dead external links
- All articles with unsourced statements
- Articles with unsourced statements from July 2022
- Hausawa
- Rayayyun mutane
- Haihuwan 1985
- Mutane daga Jihar Katsina