Fati Mariko
Fati Mariko | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 1964 (60/61 shekaru) |
ƙasa | Nijar |
Karatu | |
Harsuna |
Faransanci Hausa Zarma Fillanci |
Sana'a | |
Sana'a | mawaƙi, ɗan wasan kwaikwayo da mai rubuta kiɗa |
Kayan kida | murya |
IMDb | nm4786855 |
Fatimata Gandigui Mariko, wacce aka fi sani da Fati Mariko (an haife ta a shekara ta alif dari tara da sittin da hudu 1964), mawaƙiya ce ƴar kasar Nijar.
Ilimi da Sana'a
[gyara sashe | gyara masomin]Mariko ta yi karatunta a Yamai da Bougouni kuma ta bunƙasa fasahar buga rubutu kafin ta zama mawaƙiya. Waƙarta mai farin jini mai suna "Djana-Djana", wadda aka yi tare da ƙungiyar Marhaba kuma ta fito a alif dari tara da tamanin da shida 1986, ta kawo shahararta ta farko. Mariko ta ci gaba da aikinta a matsayin fitacciyar mawaƙiya sama da shekaru talatin, wani lokaci tana haɗin gwiwa tare da taurari maza da ƙungiyoyin hip-hop a cikin shirye-shiryenta. Waƙarta ta samo asali ne daga Zarma - al'adar Songhay da kiɗan jama'a.[1] Ta yi waƙa a cikin yaren Faransanci da kuma harsuna daban-daban na Nijar, ciki har da Hausa, Djerma, da Fula.[2] Albums ɗin ta sun haɗa da Issa Haro da Inch Allah.[3]