Fauziyya D Sulaiman

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Fauziyya D Sulaiman
Rayuwa
Haihuwa Fagge, 23 ga Maris, 1981 (42 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a marubuci

Fauziyya D Sulaiman wacce aka fi sani da (Matar Bello Q far Q), An haife ta a unguwar Fagge ta jihar Kano a Shekara ta alif dubu daya da dari daya da tamanin da daya (1981). Kuma ta kasance Marubuciyar litattafai ce sannan kuma marubuciyar labarin fina-finai. Haka nan Fauziyya na gabatar da shiri na talabijin a tashar Arewa24.[1][2]

Tarihinta da karatunta[gyara sashe | gyara masomin]

Fauziyya ta yi karatunta na Firamare a Makarantar Festival Primary School, daga nan ta wuce makarantar ‘yammata ta kwana Government Girls Secondary School ‘Yar gaya a shekara ta alif dubu ɗaya da dari tara da casa'in da uku 1993, bayan ta kammala karatunta na Jiniya ta koma Makarantar Government Girls College Dala ta karasa karatunta daga shekara ta alif 1995 zuwa shekara ta alif 1998. Daga nan ta yi aure a shekara ta alif 1999. A shekara ta 2003 ta koma karatu a Makarantar College of Health Sciences, School of Hygiene inda ta yi Diploma a kan Assistant Nutritionist. Daga nan ta yi karatun satifiket a Makarantar School of Management, a kan Hotel and Catering Services.

Ta'alifin ta[gyara sashe | gyara masomin]

A game da rubutu kuwa ta fara rubuta littafi a shekarar 2002, inda ta rubuta littafinta na farko mai suna Me na yi mata?. Daga nan ta ci gaba da rubuta littafi da suka hada da:

 • Kishin Banza
 • Guduna Ake yi
 • Rayuwar ‘Ya Mace
 • Mece ce Rayuwa
 • Burin Raina
 • Karshen Wahala
 • Labarin Zuciya
 • Matsalar Mace
 • Mijin Uwa
 • Auren Kudi
 • Duk Abinda Namiji Ya yi

Kungiyoyi[gyara sashe | gyara masomin]

Fauziyya mamba ce a Kungiyar Marubuta ta kasar Najeriya reshen jihar Kano kuma ta rike mukamin jami’a a majalisar gudanarwa ta Kungiyar tun daga watan Maris na shekara ta 2009 har zuwa shekara ta 2010. Daga nan aka sake zabenta a dai wannan mukami daga watan Maris na shekara ta 2010 har zuwa watan Maris na shekara ta 2012[3]

Sannan kuma Fauziyya ta kirkiri kungiyar ta mai suna Creative Helping Needy Foundation (CHNG) kungiya ce mai rajin tallafawa marayu da talakawa mabukata musamman a fannin ilimi da larura ta rashin lafiya.[4]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

 1. http://hausafilms.tv/writer/fauziya_d_sulaiman
 2. https://hausa.leadership.ng/2020/03/05/cikar-kungiyar-marubuta-mata-zalla-ta-mace-mutum-shekara-bakwai-da-kafuwa/
 3. https://www.pngline.com/i/fauziyya%20d%20sulaiman%20books/
 4. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2019-02-07. Retrieved 2020-04-29.