Fikayo Tomori
Fikayo Tomori | |||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||
Cikakken suna | Oluwafikayomi Oluwadamilola Tomori | ||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Calgary, 19 Disamba 1997 (26 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Birtaniya | ||||||||||||||||||||||||||||||
Harshen uwa | Turanci | ||||||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||||||
Makaranta | unknown value | ||||||||||||||||||||||||||||||
Harsuna | Turanci | ||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||
Mahalarcin
| |||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | centre-back (en) | ||||||||||||||||||||||||||||||
Lamban wasa | 23 | ||||||||||||||||||||||||||||||
Nauyi | 79 kg | ||||||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 185 cm |
Oluwafikayomi Oluwadamilola "Fikayo" Tomori (an Haife shi a 19 Disamba 1997) ya kasance kwararren ɗanwasan ƙwallon ƙafa ne,wanda ke buga wasa a ƙungiyar kulub din Chelsea.Ya wakilci ƙasar Canada da England a matakan wasan matasa.
Matakin wasa
[gyara sashe | gyara masomin]Chelsea
[gyara sashe | gyara masomin]2005–16: Matakin matasa
[gyara sashe | gyara masomin]Tomori ya fara wasa a Chelsea a matakin under-8 level inda ya kai ga har zuwa matakin akademy.[1] Ya kasance daga cikin matasan Chelsea waɗanda suka lashe gasar UEFA Youth League har sau biyu a jere kuma da lashe FA Youth Cup a 2015 da 2016.[1]
A 11 Mayu 2016, Tomori an sanya shi a cikin yan wasan na benci na Kulub din Chelsea tare da abokin wasansa, kamar Tammy Abraham da Kasey Palmer, a wasan da Chelsea ta buga 1–1 da Liverpool. Duk da haka, bai sami damar buga wasa na biyu ba a Anfield.[2] A 15 Mayu 2016, A wasan Chelsea na karshen kakar 2015/16, Tomori ya samu daman buga wasa da sukayi 1–1 da Premier League champions Leicester City, inda ya canji Branislav Ivanović a minti na 60th.[3] Tomori ya samu shiga cikin waɗanda suka je ƙasar Tarayyar Amurka dan yin wasannin gabanin kaka, amma bai samu ya buga wasa ko ɗaya ba Tamuri ya koma kungiyan AC Milan a matsayin aro inda har yanzu Yana buga Wasa a chan.[4] A 1 Augusta 2016, Tomori ya sanya hannu a kwantaragi na shekara huɗu a 2016–17.[5] A 12 Augusta 2016, Tomori ya sanya riga lamba 33 gabanin fara kakar shekarar wanda canji ne daga 43 da ya fara sawa da farko.[6]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 "Fikayo Tomori". TheChels.info.
- ↑ "Liverpool 1–1 Chelsea". BBC Sport. 11 May 2016.
- ↑ "Chelsea 1–1 Leicester City". BBC Sport. 15 May 2016.
- ↑ "Summary: International Champions Cup". Retrieved 15 September 2016.
- ↑ "Tomori new deal on tour". Chelsea F.C. 1 August 2016. Retrieved 1 August 2016.
- ↑ "Squad list announced". Chelsea F.C. Retrieved 12 August 2015.