Jump to content

Filin jirgin saman Dubai

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Filin jirgin saman Dubai
مطار دبي الدولي
IATA: DXB • ICAO: OMDB More pictures
Wuri
Ƴantacciyar ƙasaTaraiyar larabawa
Haɗaɗɗiyar daular larabawaDubai
Mazaunin mutaneAl Garhoud (en) Fassara
Coordinates 25°15′10″N 55°21′52″E / 25.2528°N 55.3644°E / 25.2528; 55.3644
Map
Altitude (en) Fassara 62 ft, above sea level
History and use
Ƙaddamarwa1960
Mai-iko Dubai
Manager (en) Fassara Dubai Airports Company
Suna saboda Dubai (birni)
Karatun Gine-gine
Yawan fili 1,400 ha
Filin jirgin sama
Tracks
Runway (en) Fassara Material Tsawo Faɗi
12L/30Rrock asphalt (en) Fassara4351 m60 m
12R/30Lrock asphalt (en) Fassara4447 m60 m
City served Dubai (birni)
Flights
Parts airport terminal (en) Fassara: 3
Offical website

Filin jirgin saman Dubai (IATA: DXB, ICAO: OMDB) shi ne babban filin jirgin saman da ke birnin Dubai, a masarautar Dubai, a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE). kuma shine filin jirgin saman da yafi kowane filin jirgi sufurin mutane na tsakanin kasa da kasa a duniya.[1] kuma shine na hudu a hada-hadan jama'a a duniya.[2] kuma na bakwai a sufurin hajoji a duniya, sannan shine filin jirgin da yafi kowane a zurga-zurgan Airbus A380 da Boeing 777,[3] kuma jiragensa yafi kowane akasarin sufurin fasinjoji a duk tashi.[4] a shekara ta 2017, DXB sun daukin nauyin pasinjoji miliyan 88, da hajoji masu kimanin nauyin tonnes miliyan 2.6 kuma sunyi rijistan zurga-zurgan jirage na kimanin dubu 409,493.[5]

Babban filin jirgin sama na Dubai yana nan a gabacin Al Garhoud district, 2.5 nautical miles (4.6 km; 2.9 mi) dake Dubai kuma ya mamaye fili mai girman eka 7,200 (hekta 2,900).[6] Ginin Terminal 3 shine gini na biyu a girma a duniya a fadin kasa. kuma shine mafi girman terminal na filayen jirage a duniya.[7]A watan Julin shekara ta 2019, Filin Jirgin ta sanya mafi girman naurar wuta mai amfanmi da hasken rana a yankin filin jirgin a matsayin daya daga cikin burikan gwamnatin Dubai na rage shan wutan nepa a kasan zuwa sheakara ta 2030.[8]

Filin jirgin Emirates na da nata cibiyar a tashar filin jirgin sama a Filin jirgin sama na dubai (DXB) da kuma wani a Terminal 3 tare da wasu bangarori 3 da suke hadin gwiwa da Flydubai. Tashar Filin jirgin Emirates shi ne mafi girman tasha a Gabas-ta-tsakiya.

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

Flying boat

Tarihin fara hawan jiragen farar hula ta fara a watan Julin shekara ta 1937 a lokacin da aka kada yarjejeniyar tashin jirgi mai tashi a ruwa na Imperial Airways tare da aron tashar soja akan kudi Rupi 440 a duk wata - wannan ya hada da kasafin masu gadi. Jirgin Imperial ya fara aiki sau daya a duk sati suna tashi zuwa Karachi daga gabas sai kuma zuwa Southampton, Ingila daga yamma. Zuwa Febrerun shekara ta 1938, an samu karin jirage masu zuwa hudu.

A tsakanin shekara ta 1940, tashi daga Dubai yawanci ta jirgin ruwa mai tashi ne wanda kungiyar British Overseas Airways Corporation (BOAC) ke aiwatar da almuransu na yau da kullum, ta hanyoyin Horseshoe tsakanin Afirka ta Kudu ta Persia Gulf har zuwa Sydney.[9]

Gini[gyara sashe | gyara masomin]

Fayil:Sheikh saeed bin maktoum al maktoum.jpg
Shugaban Dubai Sheikh Rasheed Al Maktoum
Fayil:Sheikh Saeed with Queen Elizabeth II (1995).jpg
Sheikh Rasheed da Sarauniyar Ingila Elizabeth II a 1995
Wurin pakin jirage wato apron

Shugaban kasar Dubai Sheikh Rashid bin Saeed Al Maktoum, ya umurnin ginin filin jirgin na Dubai a shekara ta 1959. an kaddamar da bikin bude ta a shekara ta 1960 da filin gudun jirgin me daukan girman hanyar Douglas DC-3 akan tsawon metre 1,800 (5,900 ft) wanda aka gina da curarren turbaya.[10]Filin jirgin ya fara da hanyoyin juya jirage guda uku, da apron (wato filin da ake fakin jirage) guda, da kuma karamin tashar jirgin sama wanda kamfanin Costain suka ginata.[11]

Hotuna[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

 1. "Dubai remains world's busiest international airport – Emirates 24|7". Emirates247.com. 24 January 2017. Retrieved 2 June, 2021.
 2. "Year to date". Retrieved 2 July 2021.
 3. "Where to spot your favourite aircraft type". anna.aero. 14 December 2016. Retrieved 2 July 2021.
 4. Cannon, Marisa. "Dubai airport up 7 per cent in passenger traffic". Business Traveller.
 5. "Press Releases". Dubaiairports.ae. Retrieved 2 July 2021.
 6. "Dubai International Airport". World Airport Guide. Archived from the original on 8 November 2006. Retrieved 2 July 2021.
 7. "Fact sheets, Reports & Statistics". Dubaiairport.com. Archived from the original on 28 September 2013. Retrieved 4 July 2021.
 8. "Dubai Airport Terminal 2 installs 15,000 solar panels". gulfnews.com. Retrieved 2 July 2021.
 9. "Dubai's First International Airport". Dubaiasitusedtobe.com. Retrieved 07 July 2021.
 10. "Dubai's beautiful first airport opened in 1960 with a sand runway". Yahoo! Canada. Retrieved 3 February 2016
 11. Andy Sambidge (23 June 2012). "UK's Costain looks for Middle East expansion". Arabian Business. Retrieved 07 July, 2021.