Gladys Anoma

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Gladys Anoma
Member of the National Assembly of Cote d'Ivoire (en) Fassara

Rayuwa
Cikakken suna Gladys Rose Bonful
Haihuwa Grand-Bassam (en) Fassara, 28 ga Maris, 1930
ƙasa Ivory Coast
Mutuwa 15th arrondissement of Paris (en) Fassara, 26 Oktoba 2006
Karatu
Makaranta University of Paris (en) Fassara
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Gladys Anoma (1930 - Oktoba 26, 2006) farfesa ce mai ilimin kimiyya kuma 'yar siyasa ce daga Ivory Coast a Yammacin Afirka.[1]

Rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Anoma 'yar Joseph Anoma ce, kuma yayin da daga baya aka san ta da Gladys Anoma, an ba ta suna Bonful Gladys Rose Anoma lokacin haihuwar ta.[1] Ta kasance ɗaliba a Senegal na tsawon shekaru huɗu sannan a Faransa na tsawon shekaru biyu.[1] Ta sami digiri na uku a fannin tsirrai na wurare masu zafi[2] daga Sorbonne, a Paris, Faransa, sannan ta ziyarci Tunisiya, Jamus, Ingila, Habasha, Morocco da Ghana kafin ta kai shekaru 37.[3]

A cewar labarin ta, ta yi aure da HE Ambassador J. Georges Anoma. Kuma taana da ’yar’uwa mai suna Mrs. Aké.[3]

Rahoton wata jarida game da balaguron mako biyar da ta yi zuwa Kingston, New York a watan Agusta 1968, tare da wasu shugabannin mata 11 na Afirka, ta ce mijinta, a lokacin, shi ne Sakatare Janar na Ma’aikatar Harkokin Waje kuma ma’auratan suna 'ya 'ya huɗu. Makasudin tafiyar shi ne don gano "al'amurra masu tada hankali a Amurka da Afirka."[3]

Ta rasu a birnin Paris a shekara ta 2006 kuma an binne ta a Abidjan na ƙasar Ivory Coast.[4] An gudanar da bikin tunawa da ita a cocin Saint Jacques Two Plateaux for Anoma a cikin shekarar 2016, shekaru 10 bayan mutuwarta.[3]

Nasarorin da ta samu[gyara sashe | gyara masomin]

  • Dr. Anoma ta koyar a Jami'ar Abidjan, Ivory Coast.[3]
  • Ta kasance marubuciyar rubutun labarin kan flora na Ivory Coast wanda ya bayyana a cikin shekarar 1971.[5]
  • A siyasance, tare da Jeanne Gervais da Hortense Aka-Anghui, ta kasance ɗaya daga cikin mata uku da aka zaɓa a Majalisar Dokokin Ƙasar Ivory Coast nan da nan bayan samun 'yancin kai; Ta yi aiki a matsayin mataimakiyar shugaban kungiyar daga shekarun 1975 har zuwa 1989.[2]
  • Ta kasance sakatare-janar na Association des Femmes Ivoriennes (Ƙungiyar Matan Ivory Coast) na shekaru masu yawa.[2]

Wallafawa[gyara sashe | gyara masomin]

  • Kammacher, Paul, Adjanohoun, Edouard, Assi, L Ake, Anoma, Gladys. LA FLORE AGROSTOLOGIQUE DE COTE D'IVOIRE . Ma'anar Botanischen Staatssammlung Munchen. 10, 1971, shafi na 30-37. H. Merxmüller. Munchen.[5]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 1.2 "Mme Bonful Gladys Rose Anoma". www.necrologie.ci. Archived from the original on 2019-11-07. Retrieved 2020-05-04.
  2. 2.0 2.1 2.2 Kathleen E. Sheldon (2005). Historical Dictionary of Women in Sub-Saharan Africa. Scarecrow Press. ISBN 978-0-8108-5331-7.
  3. 3.0 3.1 3.2 3.3 3.4 "The Kingston Daily Freeman from Kingston, New York on August 19, 1968 · Page 17". Retrieved 29 September 2017.
  4. "Cote d'Ivoire: ASCAD - To a great lady, the grateful Nation". fr.allafrica.com (in Faransanci). Retrieved 2020-05-04.
  5. 5.0 5.1 "Anoma, Gladys – Biodiversity Heritage Library". www.biodiversitylibrary.org. Retrieved 29 September 2017.