Gooya
Gooya | |
---|---|
General information | |
Labarin ƙasa | |
Tsarin Daidaiton Labarin Kasa | 11°17′39″N 11°18′50″E / 11.294273°N 11.313971°E |
Kasa | Najeriya |
Territory | Jihar Yobe |
Gooya, Goya ko Gòoya wurin binciken tarihi ne, tsohon birni ne kuma wani kwari mai tsaunuka mai yawan ramuka, kogo da kwazazzabai wanda yake a ƙaramar hukumar Fika, jihar Yobe, Najeriya .[1] Ana la'akari da shi a matsayin ɗaya daga cikin wuraren da ake kai ziyarar yawon bude ido a Yobe kuma a kuma yi masa kallon wuri mafi zurfin kwazazzabo a Najeriya.[2] A halin yanzu wurin gida ne na namun daji daban-daban kamar kuraye da birrai. A baya wurin ya kasance mafaka ne dake amfani don yin kwanton ɓauna ga ƙabilar Karai-Karai a zamanin yaƙe-yaƙe. Tarihin baka ya nuna cewa wurin tsohon yankin al'ummar Karai-Karai ne kamar yadda aka nuna shaidar kasancewar dan Adam a yankin ts hanyar la'akari da kufayin tsohon ginin ganuwar birnin da kuma ragowar burbushin rusassun gidaje da ake gani. [3] [4]
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]Tarihin baka ya nuna cewa bayan mulkin Ayam da Dakau da sauran sarakuna da dama, labari ya iso wa Mai Idris Alooma (1580 - 1617) game da danginsa wato al'ummar Karai-karai. Sakamakon haka, ruwayar ta ce, Alooma ya yi tattaki zuwa ƙasar Karai-karai da ke yammacin Kanem Borno da nufin kai dukkan al'ummar Karai-karai zuwa wani wuri kusa da shi. Labarin tafiyarsa da niyyarsa ya isa ga al'ummar Karai-Karai. Sai su kuma suka yanke shawarar tashi zuwa Gooya (kwazazzabo mai zurfi) wanda al'ummar Karai-karai musamman waɗanda suka zo ta kwarin Gongola suka gano a matsayin katafaren wurin ja da baya a duk lokacin da suka ji ba su da isasshen lokaci don ankarar da sauran. 'yan uwansu da dake nesa game da zuwan kowane haɗari.
Mai Gireema shi ne sarkin da ya jagoranci al'ummar Karai-Karai zuwa Gooya.
Nassoshi
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://leadership.ng/inside-yobes-15-tourist-attractions-cultural-events-and-the-incredible-8000yrs-dufuna-canoe/
- ↑ https://thewillnews.com/state-of-state-yobe-state/
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-18. Retrieved 2023-07-19.
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-18. Retrieved 2023-07-19.