Jump to content

Harshen Karai-Karai

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Karai-Karai (yare))
Harshen Karai-Karai
'Yan asalin magana
1,800,000
Baƙaƙen boko
Lamban rijistar harshe
ISO 639-3 kai
Glottolog kare1348[1]
Taton yaren kari karai
bikin karai kari

Karai-Karai (Ajami: كاراي-كاراي) daya ne daga harsunan al'ummun Najeriya wanda ke cikin rukunin iyalan harsunan Afroasiatic. Jihohin da aka fi yawan magana da shi sun hada da jihohin Bauchi, Borno, Yobe, Gombe da sauransu. Mafi yawan wuraren da aka fi samun al'ummar da ke magana da wannan harshe akasari suna zaune ne a garuruwan da suke cikin yankin da ake kira Ƙasar Karai-Karai ko Daular Karai-Karai wanda ya kasance gurbin wurin da ke tsakanin yammacin tsohuwar Daular Borno da kuma gabashin Kasar Hausa wanda Kuma a yanzu ya kuma shafi garuruwan da a cikin su suka hada da Kukar-Gadu, Dagare, Maje, Potiskum, Fika, Nangere, Dambam, Kalam, Jalam, Gulani, Daya, Damagum, Gujba, Ngelzarma, Deba, Janda da kuma Misau duk a cikin Najeriya. Daga cikin ire-iren karin harshen akwai Birkai, Jalalum, Ngwajum, da kuma Pakarau. [2][3][4]

Tarihin Harshe

[gyara sashe | gyara masomin]

Bayanin Asalin Suna

[gyara sashe | gyara masomin]

Alakar Harshe

[gyara sashe | gyara masomin]

Harufan Rubutu

[gyara sashe | gyara masomin]

Tsarin Sauti

[gyara sashe | gyara masomin]

Adabin Karai-Karai

[gyara sashe | gyara masomin]

Adabi shi ne abin da aka zayyana da ka ko a rubuce domin ya isar da sako ko bayar da labari. Ko ya kwaikwayi wani al'amari, ko ya bayyana halayen da zuciya take ciki, ko ya tattauna fasahohi da falsafofin rayuwa. Adabi tamkar madubi ne da ke nuna yadda rayuwa ke gudana, domin taimaka wa mutum ya karu da ilmin jiya domin gyaran yau da gobe, haka kuma adabi rumbu ne na ajiye ilmi da tarihi da sauran zamantakewar rayuwa domin amfanin al'umma. Har ila yau kuma, Adabi hoto ne da ke dauke da kwatankwacin rayuwa ta jiya da yau da kintatar gobe. Yana dauke da manufofinmu, yana tafe da matsalolinmu da fasalce-fasalcenmu da nuna mana rayuwa mai kyau da maras kyau. Wannan ne kuma ya sa wasu masanan ke nuni da cewa adabi shi ke gina Dan Adam, har ya zama mutum. Duk wasu ayyukan fasaha da suka shafi sarrafa harshe da kaifafa tunani daga cikin rayuwar al'umma ta yau da kullum, da akan shirya don koyarwa, nusarwa, tunatarwa, zaburarwa, nishadantarwa da wasa kwanya. Dalili ke nan adabi kan kunshi kusan duk wasu harkokin rayuwar al'umma da zamantakewarsu. Domin bayan labaru da wakoki da wasanni, ya shafi zantukan hikima da sarrafa harshe da ake amfani da su cikin maganganu da tadi na yau da kullum. Adabi, shi ne madubin ko hoton rayuwa na al'umma. Wannan, ya kunshi yadda al'adunsu, dabi'unsu, harshensu, halayyar rayuwarsu abincinsu, tufarsu, makwancinsu, huldodinsu, tunaninsu da ra'ayoyinsu da sauran abubuwan da suka shafi dabarun zaman duniya don ci gaba da rayuwa; kai har ma da abubuwan da suka shafi mutuwa. Rassan adabi na Bakarkarai sun hada da: Wak'a, Azanci, Tatsuniya, Almara, Hikaya, K'issa, Tarihi, Labari, Barkwanci da sauransu.

Tatsuniyoyin Karai-Karai

[gyara sashe | gyara masomin]

Tatsuniya, ƙagaggun labarai ne waɗanda ba su faru a gaske ba, wanda Karai-Karai kan shirya don annashuwa da hira. Tatsuniya, tana da amfani, domin a lokacin da (zamanin da ya shude), lokacin da ilimi da karatu ba su samu ba a ƙasashen Karai-Karai, tatsuniyoyi da labaru, su ne makarantar ‘ya’yan Karai-Karai, inda suke koyon tarbiyya ko halayen kirki, hani kan miyagun halaye da kuma dabarun zaman duniya, kamar dabarun kare kai, samun abinci, da sauransu. Kuma tatsuniya, tana ba da nishaɗi da raha.

Tun zamanin iyaye da kakanni aka buɗi ido aka tarar da al'ummar Karai-Karai sun yi riko da tatsuniya a matsayin wata hanya ta rainon 'ya'yan su wajen koya musu jarumta, dabaru da sauran muhimman darussan rayuwa. Ga misalin daya daga tatsuniyoyin da al'ummar Karai-Karai suke yi wa yaran su a lokutan dare ƙarƙashin hasken farin wata mai suna Tatsuniyar Kura Da Dila.

Zanjai Ka Auyaku

[gyara sashe | gyara masomin]

Dindeno tiku! – Marza! Dindeno na la ɗina bai sai dayi a ka ta zanjai ka auyaku. To zanjai ka auyaku na tingenasu a fula wadi, na tingenasu a fula waɗi, ka ba hnna yakara manga bai, muttan yakarasu a fula waɗi kawai, ka ba damfara nga bai. Shikenan sai na biti na biti, sai zanjai barhnni da a ka ta hnni da na la wala a markau su walanka marka bi ye su gamati kasu mikesu ɗawe a fula wadi. To ndanekau, sai zanjai da doku ta zanjai men ma yanate na rere, ma auyaku kuwa ndibkau men hnni a ka ta sabun. To ganyatansunakau a gi markau. Ndankam sai zabnasu a benu. Zabanasuku a benu, dusu kuwa yananekau dokun su waɗi a bo sabun waɗi kuwa a zinci ta rere. Kuma doku ma zanjai na kumɓaci, doku ma auyaku kuwa na simeri. To ndenekau ransuku a benu, na gaɓu ta ifisu, na gaɓu ta ifisu, auyaku na meni ka ada kaɗinko bai, sai nayi shiri ma muna ɓai ma damfarasu ne, gi mandi sa ifiyi ye, sai cirɗi a zu ben ma ɗakai, saka ya sai cirɗaka ifi, ngayam kuwa na zu gugutu ta men hnni. To akau njamtakau, sai ndala kwaro ndetu da to dama su mayakasu ne. Ndenekau burane ganga ma dan-dan-kirin, ku mento men yutaka ka dan-dan kirin kuwa tanka ka tikau a ben, ka gi ta fate bai, sai mukau faɗeke. To dukwane ganga, dukwane ganga. Raneka a benu tanka kasu, sai auyaku badi bi mandi sa cirɗeke lim hnniíi. To eli caɓtakau, sai fate hnni gazal. Anya sai tilɗi dokuhnni ka ka ta sabun kulaɓ, sai ɗayi a bai doku niya, zanjai tanka ka hnni, reneka ɓuri ya ka hnni fateka bai. Na gubɗuhnni na ruru, na gubɗuhnni na ruru, fatene daka-daka hnni. Ndenekau a naka doku ka zu zinci, zinci kuɗka dabe. Kafin baɗi doku hnni ma gubɗu tlanninki. Baɗene doku, doku na jo bai, karshaɓ-karshaɓ a zu yali. Zanjai dai tlaɗanehnni hande hnni sosai. Ndeneka a kwaro sai lamne baba auyaku a kwaro, sai da, “Na barne yasi a muni fa, na barne yasi a muni sosai, na gubɗenesunakau.” Kane gubɗa hnni. Ndenekau, sai auyaku wali a kwar ta Meto cirka kwitato. Cirne kwita ye waleneka ya na haɗu ta mento. Zanjai ikaye sai nayi boni ka aiku ma kwita, sai zanjai zaitu lewi hnni a asa yasi ka caɗ ta auyaku barahnni kwita. Lewi walikau, sai zabka kwita yi a bo hnni, sai zanjai limfati bo lewi sai da, “Ka waine menkayam kaye?” Da, “Ka caɗ ta baba auyaku.” Da, “To, ɗaci na la.” Ndeneka a gi baba auyaku, da, “To, gi bandi ka waika menkaíi, ka la alane a don mu wali.” Da, “Um, um! Na waikau ka kwar ta Meto fa!” Da, “A’a! Kwar ta Metai ma, hnno na lano.” Da, “To, yeti shiri mu wali, amma sai ka girawa.” Jaga baɗa bai sai zanjai alka yasi a zu gadlai hnni, sai zayi tabi a far ta baka hnni, sai dukwa tabi buk-buk-buk-buk, da sa kwakwayrako ma gaja da jagau baɗatakau. Ndenekau, sai auyaku da, “O’o, jaga baɗa bai!” Ndehnni sai da jagau baɗatakau, sai wali, to, bo kwarai. [Baba auyaku da],… “To, bo kwarai [ma Meto] kafuna ye, sai ka ɓalu caca ɓelu, waɗi ma afe, waɗi ma fate.” Saida ndenekau, auyaku na don, sai da, “Bo kwaro anana warai!” Sai bo kwarai afatau. Bo kwaro afatakau, sai gaɗasu, sai da, “Bo kwaro ngirki-ngiriɗ!” Sai bo kwaro fato a kasu. Ndankau yanekau ba ta ɓanasu, sai da, “To, fatoma tum.” Zanjai da sa fate bai se sa kumka gam. Ku mento ro, hnni ba mbamba, da se sa waine gam. Auyaku yetu cirot sai da, “Anana warai!”, sai bo kwaro afatau, sai fatahnni, sai da, “Bo kwaro ngirki ngiriɗ!”, sai yarata a ka ta zanjai. To fataka, zanjai ndenekau ka bo tame da, “Anana warai!”, sai da, “Ngirki ngiriɗ!”, bo kwaro sai na shaɗe a ka hnni, na tlaɗe a ka hnni. “Bo kwaro gitlki gitliɗ! Bo kwaro gitlki gitliɗ!” Ka bai. Sai Ama Meto nanna. Meto ndenekau, zanjai rahnni aka ta jigum ma indinto. Dama yeka indinto a aka ta jigum wadi. Sai zanjai rahnni akai, sai ndetu yeni indin a ka hnni, sai ale ruru aka ta jigum yi. Sai da, “Aka ta jigum hnno ka nga?!” Sai astu zanjai alese a mala sai lewai nguni a zuni ka jibo dadakese sosai. Walneka kwaro, kane auyaku na tingenonni a ka ta gunja na ɗimihnni, sai na gaɗe da, “Kawulele ma ka ta gunja, na gaɗi bi?” Sai da, “Sai ka bareno kwita.” Sai barni kine mandi na gi hnni. Sai auyaku kiye donni, kayahnni, ndai, tingi a donni, sai da tame, “Kawulele ma ka ta gunja, na gaɗi ko na gaɗi bai?”

Da, “Sai ka barneno kwita.”  Sai ka gida ɓi, ka gida ɓi, sai da gutu kwita ma gi hnni kap, sai kayehnni a wale a kwaro ka jojo. 

Ndenekam, sai lamse da, “Kai, baba auyaku, ankun na yene gubɗu a Metom, dita ɓi, ankun na kine bai. Na taka ’yenetakau sosai, tati ka aguwa. Meton, ka kala labarto ye, kai, Metai, ami ditau wam bai!” Sai da, “To, har yene ishe!” Kane, gubɗanehnni har yene ishe ma. Sai auyaku da, “Ance, ishe ma Metai, kamatikau mu kastuka sorum a kayi.” Sai kume buto walanekau. Da, “Naye, isheyi?” Da, “Ayam.” Tima isheyi, da, “Yar na kase sorum akayi.” Da, “A’a, ka kase a ka ta ami bai. Ka ba ta muno cilis wadi!” Ndanka a bice, na la kasa ya, da, “A’a, ka kase a ka ta ami bai. Ka muno cilis wadi!” Sai da, “Kai! Menkai baya gubɗane dikau ka bi kuwa!” Daci. Dindeno wayatako.

Waƙoƙin Karai-Karai

[gyara sashe | gyara masomin]

Waka tana daya daga cikin dadaddun al’adu na al’ummar Karai-Karai wanda suka dauke ta da muhimmanci kwarai dagaske. Kamar dai yadda aka sani ita wakar baka zance ne sarrafaffe, aunanne wanda ake aiwatar da shi ta bin hawa da saukar murya, mai zuwa a gunduwoyin layuka da ake rerawa bisa wani daidaitaccen tsari, a wani lokacin ma har da kida. Irin waɗannan wakoki dai Karai-Karai sun fara yin su tun kafin ma shigarsu cikin addinin Musulunci. Wakoki ne wadanda suka haɗa da: Waƙoƙin Bukukuwa, Wakokin Mata da kuma Waƙoƙin Yara. Ga wasu misalan wakokin na Karai-Karai waɗanda suke yin su a bangarori dabam-daban tun zamanin kaka da kakanni:

WA TA AKWARO (WAKOKIN AURE)

[gyara sashe | gyara masomin]

BADINE NA LATO 1a Ayye yawo badine na lato, 1b Ayye yawo badine na lato. 2a Ayye yawo badine ndala bento, 2b Ayye yawo badine ndala bento. 3a Ayye yawo gajino na lato, 3b Ayye yawo gajino na lato. 4a Ayye yawo bano yeka zawa bai, 4b Ayye yawo bano yeka zawa bai. 5a Ayye yawo bano yeka zawa bai, 5b Ayye yawo bano yeka zawa bai. 6a Ayye yawo badine walika ma, 6b Ayye yawo badine walika ma. 7a Ayye yawo badine na lato, 7b Ayye yawo badine na lato. 8a Ayye yawo badine na lato, 8b Ayye yawo badine na lato.

WA TA ASA KA (WAKOKIN YABO)

[gyara sashe | gyara masomin]

ABU ARUFE ABU ARUFE (Irin Dawa) 1 Abu arufe na la netu bo goya, Abu arufe na la netu bo goya. 2X 2 Jarime malum teneka alwashi, Abu arufe na la netu bo goya. 2X 3 Jarime na Boza alwashi na Daya, Abu arufe na la netu bo goya. 4 Adir siba yalo, siye suba nyonyo, Abu arufe na la netu bo goya. 5 Su e suba yalo, su e suba nyonyo, Abu arufe na la netu bo goya. 6 Abu arufe na la netu bo goya, Abu arufe na la netu bo goya. 7 Abu arufe na la netu bo goya, Abu arufe na la netu bo goya. 8 Su e suba yalo, su e suba nyonyo, Abu arufe na la netu bo goya. 9 Abu arufe na la netu bo goya, Abu arufe na la netu bo goya. 10 Jarime malum teneka alwashi, Abu arufe na la netu bo goya.

Karin Maganar Karai-Karai

[gyara sashe | gyara masomin]

Karin magana salo ne na yin magana takaitacciya kuma dunkulalliya wacce ke dauke da ma’ana mai fadi dan isar da saƙo ta cikin hikima. Akan yi amfani da wannan salo wajen yin nuni, gargadi, yabo, ƙarfafa gwiwa, da sauransu duk a hikimance, ta yadda kusan in ba cikakken Bakarkarai ba, fahimar wannan zance yana da wahala. Don ba kowa ne zai iya gane ta ba tare da an yi masa cikakken bayani ba. Amma yau da gobe da kuma yawan amfani da ita, musamman a zamunan da suka shude, da ake yawan tsarma ta a cikin zance, sai ya zama shi Bakarkarai yana iya gane abinsa.

Misalan Karin Maganar Karai-Karai:

[gyara sashe | gyara masomin]

1) A dar ta yaɗi ma nanu, saka ma dike. A rashin nonon uwa, ake shan na Kaka. 2) Akata wada ma daci se biradaka gabi. Don tuwon gobe ake wanke tukunya. 3) Am ma ‘yasi mem ma kawa ma dindi bai. Ruwan zafi ba wajen was an kwado ba ne. 4) Ba darta jire, ko na amu na ina bikuru. Marar gaskiya ko a cikin ruwa sai ya yi gumi. 5) Ba haɗu simeri ye tu jojo. Kowa ya ci zomo, ya ci gudu. 6) Ba rabo ma sina jibo kaleka caca bai, se sako. Mai rabon shan duka, 7) Bilan ma zu adimo. Kyan dan maciji 8) Baranka sipa lo a zanjai. An bawa Kura rabon nama. 9) Bara ɗatu a bai akau. Da babu gar aba daɗi 10) Gam bai biɗanka ulai. Bar kirga kwan kazarka kafin ta kinkishe 11) Bai mala malɗa-maɗde> dindi ngataka am ma ‘yasi. Duniya juyi-juyi kwado ya fada a ruwan zafi. 12) Ba tom ma ido manzai ceka zawani kaɗe. Mai hawaye a nesa sai ya fara kukansa da wuri. 13) Tiɗa ka indi dane waike bai, dawadi ko a ‘yali se tiɗe. Ba kullum ake kwana a gado ba. 14) Sammana ma zimbilim, teɗi fiska. Labarin zuciya a tambayi fuska. 15) Saka isheni bai sai ka basa. Duk wanda ya sha zuma ya sha harbi. 16) Riya ma wadi kwar ta wadi. Gidan wani, Dajin wani. 17) Rai gidi goro, ndala futu. Rai kamar goro ne, yana bukatar shan iska. 18) Nguzumur ngusi a da. A bar Kaza a cikin gashin ta! 19) Ndirama ‘yai sorim a ka hnni ba! Idan boka na magani, ya yiwa kansa. 20) Ndagai gamatuka ido ka taɗu. Allah Ya hada ido da bacci.

Kacici-Kacicin Karai-Karai

[gyara sashe | gyara masomin]

Kacici-kacici, reshe ne na sarrafa harshe wanda yara kan yi ta hanyar tambaya da amsa. Wasu masanan na yi masa kallon shiryayyun tambayoyi ne da kan zo a gajarce na hikima masu daukar fasali ayyananne da ke bukatar bayar da amsoshi. Akasari yaran Karai-Karai na yin kacici-kacici ne a lokaci daya da tatsuniya wanda wasu kan buɗe hirar da shi, sannan kuma tatsuniyoyi su biyo baya, a wasu lokutan kuma yakan zo a karshe, wanda idan an dauki kacici-kacici mai kama da waka ne, ana zuwa karshensa kowa sai ya watse. Wannan nau’i na sarrafa harshe, yana da matukar muhimmaci ga yara. Saboda yana taimakawa yara wajen kaifafa tunaninsu. Sannan kuma yana koyawa yara iya magana ta fuskar bayar da amsar da ta dace ga kowace tambaya. Haka nan yana koya wa yara yin tunani kafin yanke hukunci, saboda a wasu lokutan sai an yi nazari kafin a iya bayar da amsar tambayar, inda kuma ba amsa sai a ce an ba da gari. Wato an sallama ba za a iya ba, a nan kuma sai shi mai tambayar ya fadi amsa, wanda wannan yana koyar da yara sanin duk abin da ya gagari mutum, to za a iya samun mai yi. Yaran Karai-Karai suna yin kacici-kacici ne ta hanyar tambaya da amsa. Mutane biyu, ko fiye da haka ne ke yinsa. Ɗaya na tambaya saura kuma suna amsawa. Misalan Kacici-Kacicin Bakarkarai 1. Kwam ma kwar timu waleka dawai ka rici na nnaye ka ‘yari. 2. Na la riya, riya na zirahnno. 3. Na je daji, daji na yi mini dariya. 4. Baba na ben, bagwaja na mala. 5. Baba na daka gemunsa na waje 6. Na biraɗu ɗayi na zaka bo pati amma bika bai. 7. Na wanke tukunyata, na shanya a rana amma taki bushewa. 8. Kwamai hnno dibu, zor ta yanda sine wadi. 9. Shanu na dubu madaurin su daya. 10. Na la riya na kaleka zawa ma beno Garabi. 11. Aya maiwa fataru birazato. 12. Ai gunja ai gunja sai simeri pati bik! 13. Men ta kwar timu gwani ‘yararai. 14. Kukkuruk ka rugde. 15. Lewai ma baba lauke ka hnni ka polo ka polo. 16. Na birku bai kwaro na kumtu insa ma kwakware. 17. Ben ma bazin ka bo bai. 18. Na biradu dayi na zaka bo pati amma bika bai. 19. Ndaru ngunak ngunadi. 20. Tara ma baba maiwa, tugum ma akata wadi tak.

  1. Hammarström, Harald; Forkel, Robert; Haspelmath, Martin, eds. (2017). "Harshen Karai-Karai". Glottolog 3.0. Jena, Germany: Max Planck Institute for the Science of Human History.
  2. "OLAC resources in and about the Karai-Karai language".
  3. Blench, Roger (2019). An Atlas of Nigerian Languages (4th ed.). Cambridge: Kay Williamson Educational Foundation.
  4. Russeel G. Schuch; Yobe State Languages Research Project: aflang.humanities.ucla.edu/language-materials/chadic-languages/yobe/Karai-Karai