Gundumar Sanatan Adamawa ta Arewa
Appearance
Adamawa North senatorial district |
---|
Sanatan Adamawa ta Arewa a Jihar Adamawan Najeriya ta ƙunshi ƙananan hukumomin Madagali da Maiha da Michika da Mubi ta Arewa da kuma Mubi ta Kudu.[1][2]
Sanatan da ke wakiltar gundumar a halin yanzu shine Amos Yohanna na jam'iyyar PDP wanda aka zaɓa a shekarar 2023.[3]
Sanatocin da suka wakilta gundumar
[gyara sashe | gyara masomin]A ƙasa jerin sanatocin da suka wakilci gundumar ne tun daga ranar 5 ga watan Disamban 1992 zuwa yau.
Sanata | Jam'iyya | Shekarar | Majalisa ta | Tarihin zaɓen |
---|---|---|---|---|
An ƙirƙira Gundumar a ranar 5 ga watan Disamban shekarar 1992 | ||||
Paul Wampana | Disamba 5, 1992 - Nuwamba 17, 1993 | 3 | An zaɓe shi a shekarar 1992
Jamhoriya ta 3 ta watse | |
Iya Abubakar | PDP | Yuni 3, 1999 - Yuni 5, 2007 | 4 ta, 5 | An zaɓe shi a shekarar 1999
An sake zaɓenshi a shekarar 2003 |
Mohammed Mana | PDD | Yuni 5, 2007 - Yuni 6, 2011 | ta 6 | An zaɓeshi a shekarar 2007 |
Bindo Jibrilla | PDP | Yuni 6, 2011 - Yuni 6, 2015 | ta 7 | An zaɓeshi a shekarar 2011
Yayi ritaya |
Binta Masi Garba | APC | Yuni 6, 2015 - Yuni 11, 2019 | ta 8 | An zaɓeta a shekarar 2015
Zaɓen ya samu matsala |
Ishaku Abbo | PDP | Yuni 11, 2019 - Oktoba 16, 2023 | 9 ta, 10 | An Zaɓeshi a 2019
Ba'a zaɓe shi ba bayan ƙarewar wa'adinsa |
Amos Yohanna | PDP | Oktoba 16, 2023 - yanzu | ta 10 | An zaɓeshi a shekarar 2023 |
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]Adamawa North senatorial district |
---|
- ↑ "ShineYourEye". www.shineyoureye.org. Retrieved 2024-05-28.
- ↑ "Adamawa North Senatorial aspirant promises rebirth, excellent representation". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). 2022-04-19. Retrieved 2024-05-28.
- ↑ Adah, Glamour (2023-10-26). "Senate Swears In Amos Yohanna To Replace Elisha Abbo". Arise News (in Turanci). Retrieved 2024-05-28.