Jump to content

Iya Abubakar

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Iya Abubakar
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

Mayu 2003 - Mayu 2007 - Mohammed Mana
District: Adamawa North
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

1999 -
District: Adamawa North
Ministan Tsaron Najeriya

1979 - 1981
Olusegun Obasanjo - Akanbi Oniyangi
Rayuwa
Haihuwa Jihar Adamawa, 14 Disamba 1934 (89 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta St Catharine's College, Cambridge (en) Fassara
Kwalejin Barewa
Jami'ar Ibadan
Harsuna Turanci
Hausa
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa, masanin lissafi da Farfesa
Employers University of Michigan (en) Fassara
Jami'ar Ahmadu Bello
Kyaututtuka
Mamba Makarantar Kimiyya ta Najeriya
Imani
Addini Musulunci
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Iya Abubakar (An haife shi a ranar 14 ga watan Disamba, shekarar alif 1934) ya kasance Dan Nijeriya ne, Dan siyasa kuma kwararren malamin lissafi ne farfesa ne me mafi karanci shekarun da aka yi, yana cikin tsofaffin shugaban jami'ar ABU Zaria, ya kuma rike mukaman gwamnati da dama (Ministan tsaron Nijeriya da Ministan Harkokin cikin gida) lokacin Tarayyar Nijeriya ta Biyu, ya kuma zama Senata mai wakiltar Adamawa ta Arewa daga watan Mayu, shekarar alif 1999, zuwa watan Mayun shekarar 2007.[1][2]

Haihuwa da Aikin Karatu[gyara sashe | gyara masomin]

An haife Abubakar a Ranar 14 ga watan Disamban shekarar 1934. Yayi karatu a Kwalejin Barewa, Jami'ar Kwalejin Ibadan (wanda tazama ayanzu Jami'ar Ibadan) ya samu yin Ph.D a Jami'ar Cambridge. Yayi aiki amatsayin ferfesa mai kai kawo a Jami'ar Michigan daga shekarar 1965 zuwa shekarar 1966, sannan aka naɗa shi farfesan lissafi a Jami'ar Ahmadu Bello yana da shekara 28, a shekarar 1967.[3] Yarike matsayin har shekarar 1975, da kuma farfesa mai kai kawo a City University of New York daga shekarar 1971 zuwa shekarar 1972. A shekarar 1975, an nada shi Vice-Chancellor na jami'ar Ahmadu Bello, mukamin ne yarike har shekarar 1978. Abubakar yazama darekta a Babban Bankin Nijeriya daga shekarar 1972 zuwa shekarar 1975.[4][2]

Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan karewar mulkin Lt-Gen. Olusẹgun Ọbasanjọ bayan ya mika mulki ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa na dimokradiyya a shekarar 1979, an naɗa Abubakar Ministan Tsaro na Tarayyar, inda yarike mukamin har shekarar 1982. Daga shekarar 1993 zuwa shekarar 2005, shine Pro-Chancellor kuma Chairman na Majalisar Jami'ar Ibadan. A karshen shekara ta 1990, ya rike mukamin darekta na National Mathematical Centre dake Abuja da kuma rike National Manpower Commission of Nigeria dana non-governmental Africa International Foundation for Science and Technology.[4][2]

Abubakar Iya yazama sanata mai wakiltar Adamawa ta Arewa a Jihar Adamawa, Nigeria a farkon dawowar Nigerian Fourth Republic, yanema a karkashin jam'iyyar People's Democratic Party (PDP). Ya shiga ofis a ranar 29 ga watan Mayu shekara ta 1999.[5] An sake zaɓen sa a watan Afrilu shekara ta 2003.[6] Bayan samun nasarar sa zuwa majalisar dattawa a watan Yuni shekarar 1999 an bashi rikon mukamai na kwamiti akan Public Accounts, da Banking & Currency (chairman), da Commerce and Finance & Approprition.[7] Abubakar ya kuma rike shugaban kwamiti na Finance and Appropriation[8] da kwamiti na Science and Technology.[9][2].

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://dailytrust.com/senator-iya-abubakar-at-84
  2. 2.0 2.1 2.2 2.3 Cite web|url=http://www.nigerianbiography.com/2015/11/biography-of-iya-abubakar.html%7Ctitle=Biography of Iya Abubakar|website=www.nigerianbiography.com|access-date=2017-10-20
  3. Cite web |url=http://www.math.buffalo.edu/mad/PEEPS/abubakar_iya.html |title=Iya Abubakar |work=Mathematicians of the African Diaspora |accessdate=2010-06-23
  4. 4.0 4.1 Cite book |title=Who's Who 2006 |publisher=Bloomsbury USA |year=2006 |isbn=1-59691-218-9
  5. cite web |url=http://psephos.adam-carr.net/countries/n/nigeria/nigerialeg2.txt |title=FEDERAL REPUBLIC OF NIGERIA LEGISLATIVE ELECTION OF 20 FEBRUARY AND 7 MARCH 1999 |work=Psephos |accessdate=2010-06-23
  6. cite web |url=http://www.dawodu.com/senator.htm |title=Senators |work=Dawodu |accessdate=2010-06-23
  7. Cite web |url=http://www.nigeriacongress.org/assembly/committees1.htm |title=Congressional Committees |publisher=Nigeria Congress |accessdate=2010-06-23 |deadurl=yes |archiveurl=https://web.archive.org/web/20091118151316/http://www.nigeriacongress.org/assembly/committees1.htm |archivedate=2009-11-18 |df=
  8. citation|url=http://allafrica.com/stories/200304160468.html%7Ctitle=Nigeria[permanent dead link]: Iya Abubakar Predicts Boom for Adamawa|newspaper=Daily Trust|first=Tashikalmah|last=Hallah|date=April 16, 2003.
  9. citation|url=http://allafrica.com/stories/200309100548.html%7Ctitle=Nigeria[permanent dead link]: Senate to Sign IT Policy Bill Soon - Prof. Abubakar|newspaper=Daily Trust|first=Hassan|last=Idris|date=September 10, 2003.

.