Haruna Abubakar

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Haruna Abubakar
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

29 Mayu 1999 - 2003 - Emmanuel Okpede
District: Nasarawa South
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

29 Mayu 1999 - - Emmanuel Okpede
District: Nasarawa South
Rayuwa
Haihuwa Nasarawa, 6 ga Yuni, 1952
ƙasa Najeriya
Mutuwa Ingila, 27 ga Faburairu, 2005
Karatu
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Haruna Abubakar (an haifeshi a ranar 6 ga watan Yunin shekarar 1952). Ɗan siyasa ne kuma lauya. an zaɓe shi Sanata ne na mazabar Nasarawa ta Kudu ta Jihar Nasarawa a Najeriya a farkon Jamhuriya ta huɗu, yana aiki a kan dandalin Jam’iyyar PDP. Ya hau ofishi ranar 29 ga Mayun shekarar 1999.[1]

Farkon rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Abubakar ne a ranar 6 ga Yunin shekarata 1952. Ya kuma zama lauya kuma ɗan kasuwa, sannan ya kasance mai ba da shawara a fannin shari’a ga Jam’iyyar National Party of Nigeria (NPN) a lokacin Jamhuriya ta biyu ta Najeriya. Ya kuma kasance Manajan Darakta na Kamfanin Pip Pip da Kamfanin Tallata Kayayyakin Man Fetur a zamanin mulkin mulkin Janar Sani Abacha.

Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan ya ci kujerarsa a Majalisar Dattawa a watan Yuni na shekarar 1999, aka naɗa shi ga kwamitocin kan Zaɓe (Mataimakin shugaban kasa), Ayyukan Majalisar Dattawa, Man Fetur, Harkokin Shari’a, Harkokin tattalin arziƙi da basusuka na gida & na waje. An kuma naɗa shi Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa a shekarar 1999, amma daga baya aka tilasta shi yin murabus.

Mutuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Abubakar ya rasu a wani asibiti dake babban birnin ƙasar ingila a London bayan doguwar jinya a ranar 27 ga Fabrairun shekarar 2005. An kuma binne shi a Lafiya.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "FEDERAL REPUBLIC OF NIGERIA LEGISLATIVE ELECTION OF 20 FEBRUARY AND 7 MARCH 1999"