Jump to content

Haruna Manu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Haruna Manu
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

13 ga Yuni, 2023 -
Yusuf Abubakar Yusuf
District: Taraba Central
Deputy Governor of Taraba State (en) Fassara

29 Mayu 2015 - 29 Mayu 2023
Rayuwa
Haihuwa 23 ga Augusta, 1973 (51 shekaru)
ƙasa Najeriya
Mazauni Jalingo
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da injiniya
Imani
Jam'iyar siyasa People's Democratic Party (en) Fassara

Haruna Manu (an haife shi ranar 23 Ga watan Augusta shekarar alif 1973) dan siyasa ne a Najeriaya kuma mamba na jamiyyar PDP sannan kuma tsohon mamba a majalisar wakilai ta tattauna, ya wakilai Bali/Gassol Federal Constituency. Shine mataimakin gwamnan Jihar Taraba, yana mataimakin ne karkashin gwamna Darius Dickson Ishaku tun daga ranar 29 ga watan Mayu, shekarar 2015.[1][2][3][4]

Rayuwa da Ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Haruna a ranar 23 ga watan Agusta, shakarar 1973, a wani gari da ake kira da Mutum-Biyu, a karamar hukumar Gassol ta jihar Taraba. Ya yi digiri na farko a fannin harkokin kasuwanci (Business Administration) tare da samun kwarewa a fannin hada-hadar kudi daga babbar Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya a jihar Kaduna. Ya kuma yi digirin digirgir a fannin Kasuwancin Lantarki daga Jami’ar Carnegie Mellon da ke Amurka, kuma ya samu sheda a certified Microsoft System Engineer.

Yayi aiki da Nigerian Liquefied Natural Gas (NLNG) ya kuma yi aiki a kamfanin sadarwa na Nigeria Communication Limited (MTN) a takaice yayi aiki a kamfanoni dama.

  1. "Taraba seeks Senate intervention over N30b spent on FG roads". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). 2017-11-15. Archived from the original on 2022-02-22. Retrieved 2022-02-22.
  2. "Looters will be arrested, says Taraba deputy gov". Punch Newspapers (in Turanci). 2020-10-26. Retrieved 2022-03-12.
  3. "Office of the Deputy Governor". tarabastate.gov.ng. Archived from the original on October 8, 2020. Retrieved November 10, 2020.
  4. "Inec Declares Darius Ishaku winner of Taraba Governorship Election". Channels TV. April 26, 2015. Retrieved November 10, 2020.