Ibife Alufohai
|
| |
| Rayuwa | |
| Haihuwa | Calabar, 29 ga Augusta, 1986 (39 shekaru) |
| Sana'a | |
Ibife Eugene Alufohai (an haife ta ranar 29 ga watan Agusta, 1986) 'yar Nijeriya ce, 'yar kwalliya, mai aikin bada agaji, mai kuma riƙe da kambun sarauniyar kyau ta Miss Valentine International 2010.[1] Ita ce ta kirkiro Miss Polo International.[2][3]
Tarihin Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Alufohai ta fito ne daga garin Abonnema na, jihar Ribas. Sai dai an haife ta ne a Calabar, Jihar Kuros Riba kuma ita ce ta ƙarshe cikin yara bakwai na iyayenta. Iyalinta sun yi kaurace-kaurace sosai saboda yanayin aikin mahaifinta a matsayin jami'in soja, wanda aka yi ta yiwa sauyin wajen aikin daga jihar Kaduna suka koma Fatakwal, zuwa Jihar Ribas.
Karatu
[gyara sashe | gyara masomin]Daga shekarar 1993 zuwa 1997 ta yi karatunta na firamare, ta kuma fara na sakandare duk a makarantar Tantua International Group of Schools inda ta kammala a shekarar 2003. A kuma shekarar 2003 din ta tafi Jami'ar Madonna, Okija don karatun jami'a sannan ta wuce Jami'ar Fatakwal, Jihar Ribas a shekarar 2008, inda ta kammala a shekarar 2012 tare da digiri a fannin Clinical psychology . Bayan karatun ta na jami'a, ta yi bautar kasa a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Yenagoa, Jihar Bayelsa, inda ta yi aiki a matsayin masaniyar halayyar dan Adam da kuma aiki a ECG daga shekarun 2013 zuwa 2014.
Iyali
[gyara sashe | gyara masomin]Alufohai ta yi aure har da ɗiyar ta. A zaman wani bangare na ayyukan taimakon al'umma da take, ta kafa gidauniya mai suna Polo International Relief Foundation.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Abraham, Anthony (19 April 2019). "World Fashion Festival Awards Honours Director of Polo International". Leadership Newspaper. Archived from the original on 19 April 2019. Retrieved 18 November 2019.
- ↑ "Abuja hosts 2018 'Miss Polo International'". Vanguard Newspaper. 16 August 2018. Retrieved 18 November 2019.
- ↑ Oyeyemi, Tunji (28 August 2018). "Nigeria fast becoming destination of choice for tourists- Minister". Federal Ministry of Information and Culture. Retrieved 18 November 2019.