Jump to content

Idris Abubakar

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Idris Abubakar
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya

3 ga Yuni, 2003 - 2007
District: Funa District (en) Fassara
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

29 Mayu 1999 - 29 Mayu 2003
District: Gombe South
Rayuwa
Haihuwa Jihar Gombe, 13 Nuwamba, 1955
ƙasa Najeriya
Mutuwa 1 ga Janairu, 2002
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa All Nigeria Peoples Party

Idris Abubakar (1955-2002) Ya kasance tsohon Sanata ne a Mazaɓar Gombe ta kudu ta jihar Gombe dake Najeriya a farkon Jamhuriya ta huɗu, ya gudanar da dandalin All People’s Party (APP). Ya shiga ofishi ranar 29 ga Mayun shekarar 1999.[1]

Tarihin rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Abubakar ne a ranar 13 ga Nuwamban 1955 a jihar Gombe.

Ya zama lauya a fannin shari'a, sannan ya kuma kasance babban abokin tarayya na Idris Abubakar & Co tare da ofisoshin a jihohin Bauchi da Legas. Ya kasance wakili a Majalisar Wakilai a lokacin da aka soke Jamhuriyyar Najeriyar (1992-11993).

Bayan ya hau kujerar shugabancin majalisar dattijai a watan Yuni na shekarar 1999, an naɗa shi ga kwamitoci a kan Ka’idoji & Kaidoji, Ma'adanai mai Muni, Banki & Kudade, Albarkatun Ruwa, Tsabtacewa da kuma basussuka na cikin gida & na waje (shugaba). Ya koma domin maye gurbin Sanata Evans Enwerem a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa a watan Nuwamban shekarata 1999. Daga baya, Abubakar ya fara gabatar da kudirin tsige Shugaba Olusegun Obasanjo saboda rashin aiwatar da dokar ta kasa.

Abubakar ya kamu da cutar sankara a ranar 10 ga Disamban shekarar 2002 bayan wani doguwar rashin lafiya.

Idris Yusuf ya rasu a ranan 11 ga watan Desanba shekara ta 2002.[2]