Jump to content

Ilojo Bar

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ilojo Bar
Wuri
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihohin Najeriyajahar Lagos
Ƙananan hukumumin a NijeriyaLagos Island
Coordinates 6°34′N 3°20′E / 6.57°N 3.33°E / 6.57; 3.33
Map
History and use
Opening1855
Heritage
Ilojo Bar & Restaurant
Wuri
Lagos Island, Lagos, Lagos State, Nigeria
Coordinates 6°34′N 3°20′E / 6.57°N 3.33°E / 6.57; 3.33
Map
History and use
Opening1855
Heritage
Fayil:Ilojo Bar advert, 1939.jpeg
Tallan sabis akan bugu na Daily Times na Najeriya a 1939

Ilojo Bar, wanda kuma ake kira Olaiya House ko Casa and Fernandez,wani gini ne mai tarihi irin na ƙasar Brazil wanda ke kusa da dandalin Tinubu a tsibirin Lagos Island, jihar Legas, Najeriya. [1][2] Asalin gidan Fernandez ne suka gina shi azaman mashaya da gidan abinci a shekara ta 1855 waɗanda suka yi aiki da tsoffin bayi waɗanda suka ƙware da fasahar gini yayin da suke Kudancin Amurka.[3] Daga baya aka sayar da Ilojo Bar ga Alfred Omolana Olaiya na dangin Olaiya a shekarar 1933 kuma Hukumar Kula da Gidajen tarihi da abubuwan tarihi ta kasa ta ayyana a matsayin abin tarihi na kasa a shekara ta 1956. [4]

Sunan "Ilojo Bar"

[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan da aka siyar da gidan ga Alfred Omolona Olaiya a shekarar 1933, ya sanyawa ginin suna “Ilojo Bar” da sunan garinsu na “Ilojo” da ke Ijesa Isu, jihar Ekiti. [5]

Ilojo Bar

An ruguje ginin ne a ranar Lahadi, 11 ga watan Satumba, shekara ta dubu biyu da sha shida 2016, bisa wasu shakku a lokacin bukukuwan Sallah a Legas.[6][7] Ana ci gaba da binciken lamarin. Yanzu haka dai filin yana karkashin gwamnatin jihar Legas. [8] [9][10]

  1. Edvige Jean-François; Chris Giles (19 July 2017). "Lagos' Afro-Brazilian architecture faces down the bulldozers". Cable News Network. Retrieved 5 August 2017.
  2. Empty citation (help) Hakeem B. Harunah (2000). Nigeria's defunct slave ports: their cultural legacies and touristic value. First Academic Publishers. ISBN 978-978-34902-3-9
  3. Alex Ikechukwu Okpoko; Pat Uche Okpoko (2002). Tourism in Nigeria. Afro-Orbis Publications. ISBN 978-978-35253-8-2
  4. Udemma Chukwuma (22 October 2014). " 'Bring Ilojo Bar back to life". The Nation Newspaper. Retrieved 5 September 2016.
  5. "A Tragedy of Confusing Interests". ktravula-a travelogue!. 2 October 2016. Retrieved 26 February 2017.
  6. "A Failure All Around". ktravula-a travelogue!. 3 October 2016. Retrieved 26 February 2017.
  7. "161-year-old Ilojo Bar demolished-The Nation Nigeria". 13 September 2016. Retrieved 18 September 2016.
  8. "Update on the Demolition of Ilojo Bar". 18 September 2016. Retrieved 19 September 2016.
  9. Joseph Jibueze (28 September 2016). "Why Ilojo Bar was demolished, by family". The Nation. Retrieved 30 September 2016.
  10. Sunday Onen (28 September 2016). "Africa: 161 year old Monument "Ilojo Bar" Demolished in Lagos". ATQ News. Retrieved 23 July 2019.