Inibehe Effiong
Inibehe Effiong | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Akwa Ibom, 21 Disamba 1988 (35 shekaru) |
Karatu | |
Makaranta | University of Uyo (en) |
Sana'a | |
Sana'a | Lauya da Mai kare ƴancin ɗan'adam |
Mamba | African Action Congress (en) |
Inibehe Effiong (an haife shi a ranar ashirin da daya ga watan Disamba na shekara ta alif dari tara da tamanin da takwas1988). Shi lauya ne na kare hakkin bil'adama a kasar Najeriya, mai fafutuka, mai sharhi kan zamantakewar al'umma, kuma lauya ne kan shari'a.[1][2][3] Shi ne mai ba da shawara kan shari'a na African Action Congress . [4]
Rayuwa ta farko
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Effiong a Jihar Akwa Ibom dake kasar Najeriya a shekarar 1988. Ya halarci Babban Makarantar Kimiyya ta Presbyterian kuma ya ci gaba da karatun gaba da sakandare a Jami'ar Uyo, inda ya sami digiri na farko a fannin shari'a kuma an kira shi zuwa lauyanci a shekarar 2015.[5]
Yunkurin fafutuka
[gyara sashe | gyara masomin]A watan Agustan 2020, Effiong ya shigar da tuhuma a kan Hukumar Watsa Labarai ta Kasa don yin gyare-gyare ga Dokar Watsa Labaran Najeriya da kuma kara akan maganganun ƙiyayya daga naira dubu dari biyar (NGN 500,000) zuwa naira miliyan biyar (NGN 5,000,000). [6]
Daga ranar 5 ga Yuni na shekarar 2021, zuwa ranar 13 ga watan Janairun 2022, Gwamnatin Tarayya ta kasar Najeriya ta haramta Twitter, wanda ya jawo dakatar da aikinta a kasar. Inibehe ya shigar da kara a babban kotun tarayya a kan Gwamnatin Tarayyar ta Najeriya, tsohon Ministan Bayanai da Al'adu, Lai Mohammed, da kuma Babban Lauyan da Ministan Shari'a na lokacin, Abubakar Malami, domin samun umarni da ke hana gwamnati hana Twitter.[7]
A watan Maris na shekara ta dubu biyu da ashirin da uku 2023, Effiong ya soki Hukumar Tsaro ta Jihar Najeriya saboda karɓar sunan Ma'aikatar Tsaro ta Jiha kuma ya dauke shi ba bisa ka'ida ba.[8]
A ranar 27 ga watan Yulin shekarar dubu biyu da ashirin da biyu 2022, Babban Alkalin Jihar Akwa Ibom, Ekaette Obot, ya ba da umarnin a kulle Effiong a kurkuku saboda raini.[9] Yayinda yake cikin gidan kurkuku, ya yi iƙirarin cewa jami'in gidan yarin ya azabtar da shi, amma Hukumar gyara hali ta Najeriya ta karyata iƙirarin.[10][11]
kulle Inibehe a Kurkuku da gwamnatin tayi ya haifar da rikice-rikice a kasar wanda ya hada da kungiyoyi da dama irin kungiyoyar kare hakkin dan adam, gami da Socio-Economic Rights and Accountability Project da Amnesty International, Majalisa ta Najeriya wato najeriyan labo kongres ta yi kira ga sakin Inibehe. Akalla kungiyoyi 26 na farar hula da ke kira ga sakin Inibehe sun gabatar da takarda ga Babban Kwamishinan Majalisar Dinkin Duniya na 'Yancin Dan Adam a Geneva.[12]
Kungiyar Lauyoyin Najeriya wato SAN ta yi barazanar gabatar da takarda tare da Majalisar Shari'a ta Kasar najeriya, kuma sanannun lauyoyin Najeriya da yawa wanda suka hada da Babban Lauyan Najeriya kamar Femi Falana da Kayode Ajulo, sun yi Allah wadai da tsare Effiong. Kayode Ajulo ya bayyana ɗaurin Effiong a matsayin "ci da ceto da ikon shari'a".[13]
Lauyan kare hakkin dan adam kuma marubuci, mai suna Farfesa Chidi Odinkalu, ya bayyana Inibehe Effiong a matsayin "mai ƙarfin zuciya, jarumi mai ƙarfi, kuma mai ba da shawara kuma dan fafutuka mai basira wanda aka ƙaddara da ya zama sabon abu anan gaba a cikin aikin lauyanci, fafutuka da kuma kare hakkin dan adam na kasar Najeriya".[14]
Bayanan da aka ambata
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Inibehe Effiong: Impunity in the land of promise". Punch Newspapers. 2022-08-12. Retrieved 2023-12-22.
- ↑ Ugwu, Francis (2024-01-25). "My father fled North, abandoned everything he worked for - Inibehe Effiong laments Plateau killings". Daily Post Nigeria (in Turanci). Retrieved 2024-01-26.
- ↑ Princewill, Nimi (2022-11-10). "TikTokers caned and ordered to wash toilets as court rules they defamed Nigerian governor". CNN. Retrieved 2023-12-22.
- ↑ Oloniniran, Gbenga (2022-07-27). "Imprisonment: Release lawyer now, AAC tells A'Ibom CJ". Punch Newspapers. Retrieved 2023-12-22.
- ↑ "Inibehe Effiong: Defender of the defenceless who was put behind bars". Skabash!. 2022-12-27. Retrieved 2023-12-22.
- ↑ Akinkuotu, Eniola (2020-08-18). "Lawyer sues Lai Mohammed, NBC for hiking hate speech fine to N5m". Punch Newspapers. Retrieved 2023-12-22.
- ↑ "Twitter ban: Lawyer, Inibehe Effiong sues FG, Malami, Lai Mohammed". Trending News -. 2021-06-16. Retrieved 2023-12-22.
- ↑ Ochuba, Ogechukwu (2023-03-07). "DSS vs SSS: Inibehe Effiong Questions Legality of Security Agency's Name Following Social Media Debut". The Metro Lawyer. Archived from the original on 2023-12-22. Retrieved 2023-12-22.
- ↑ Igwe, Ignatius (2022-07-27). "Court Remands Human Right Lawyer, Inibehe Effiong For Contempt". Channels Television. Retrieved 2023-12-22.
- ↑ "How I was tortured while in prison -Lawyer Inibehe Effiong". Punch Newspapers. 2022-09-05. Retrieved 2023-12-22.
- ↑ Udonquak, Aniefiok (2022-08-12). "NCS debunks torture of human rights lawyer in A/Ibom -". Businessday NG. Retrieved 2023-12-22.
- ↑ "CSOs petition UN over Inibehe Effiong's incarceration". Premium Times Nigeria (in Jamusanci). Retrieved 2023-12-22.
- ↑ "Falana, Ajulo Condemn Illegal Imprisonment Of AAC Legal Adviser, Inibehe Effiong By Akwa Ibom Chief Judge, Say Victim Committed No Offence". Sahara Reporters. 2022-07-31. Retrieved 2023-12-22.
- ↑ "Top 10 quotes on Inibehe Effiong's incarceration". Premium Times Nigeria (in Jamusanci). Retrieved 2023-12-22.