Jump to content

Jacob Gyang Buba

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jacob Gyang Buba
Rayuwa
Haihuwa 10 Oktoba 1951 (72 shekaru)
Sana'a
Sana'a Sarauta

Jacob Gyang Buba

(An haife shi a ranar 10 ga watan Oktoba a shekarar 1951), ya kasan ce tsohon jami'in kwastam ne da ya yi ritaya. San nan Ya yi aiki a matsayin Kwanturola-Janar na Kwastam din Najeriya daga shekara ta 2004 zuwa shekarar 2008. A ranar 1 ga watan Afrilu shekara ta 2009, aka rantsar da shi a matsayin Gbong Gwom Jos, babban basaraken masarautar Berom wanda ke matsayin sarki na 5 na ƙabilun bayan mutuwar da Victor Dung Pam. Shine Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jos kuma shugaban Majalisar Hadin Gwuiwar Jos. Yana aiki ne a matsayin Shugaban Jami'ar na 3 na Jami'ar Nnamdi Azikiwe tun daga watan Maris shekara ta 2016 a taron karo na 10 na makarantar.

Bayan Fage[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Gyang Buba a shekarar ta 1951 A Kauyen Madu na gundumar Du, Jos ta Kudu, Jihar Filato. Shine ɗan fari na Buba Dung Bot na Lo Du, Lo-Wet family da Ngo Kaneng Buba, ɗan ɗan gidan mai mulkin masarautar. Ya fara karatun sa na farko a makarantar SUM elementary Chwelnyap a shekarar ta 1960 zuwa shekara ta 1963, sannan ya tafi Baptist Day School Jos don kammala karatunsa na firamare, bayan ya kammala kuma daga shekarar 1966 zuwa shekera ta 1971, ya kamala makarantar sakandaren lardin, Kuru wanda yanzu ake kira makarantar sakandaren gwamnati, Kuru. kuma ya halarci Cibiyar Gudanarwa ta Jami’ar Ahmadu Bello ya kuma ya kammala karatun difloma a harkar Banki a shekarar ta 1975.

Ayyuka[gyara sashe | gyara masomin]

Ya fara aikin sa ne a matsayin magatakarda a Ofishin Ba da Lamuni na Tarayya a shekarar 1972 zuwa shekara ta 1974, kafin ya halarci Cibiyar Gudanarwa kuma ya shiga cikin Hukumar Kwastam ta Najeriya a shekara ta 1975 a matsayin mataimakin jami’in rigakafi. Ya zama CG a shekarata 2004 kuma ya kasance shugaban ƙaramin kwamiti na Tarayyar Afirka na daraktocin janar na Kwastam a tsakanin 2007 zuwa 2008, mukamin da ya gabata shi ne mataimakin CG na kwastam a babban ofishinta dake Abuja . A matsayinsa na CG na kwastam, ya aiwatar da sauye-sauye na Haraji na waje don ECOWAS da kuma gudanar da aikin ɗaukar hoto a kan iyakokin, yankunan filayen jirgin sama da tashar jiragen ruwa, ya gyara cikakken nazarin dokar Kwastam da Gudanar da Haraji a shekarar 1958 da kuma sanarwa kwastam daban-daban. Gyang yana halartar taron Kasuwanci daban-daban wanda daga cikinsu ya haɗa da taron karawa juna sani na ƴansandan ƙasa da ƙasa wato INTERPOL . Shi memba ne da aka nada a cikin Cocin Seventh Day Adventist, kuma an ba shi lambar girmamawa ta kasa ta Kwamandan Umarnin Nijar (CON) da Jami'in Tarayyar Tarayya (OFR), shi ma memba ne a Taron Kasa na 2014.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]


Kara karantawa[gyara sashe | gyara masomin]

 • Mehler, Andreas; Melber, Henning; Walraven, Klaas Van (2009-10-10). Africa Yearbook Volume 5: Politics, Economy and Society South of the Sahara In 2008. BRILL. ISBN 978-90-04-17811-3.
 • Mehler, Andreas; Melber, Henning; Walraven, Klaas van (2010-10-25). Africa Yearbook Volume 6: Politics, Economy and Society South of the Sahara in 2009. BRILL. ISBN 978-90-04-18560-9.
 • Corporate Nigeria. IMC--International Media Communications GmbH. 2006.

Hanyoyin haɗin waje[gyara sashe | gyara masomin]

 • Obisakin, Lawrence Olufemi (2007). Protocol for Life: Guidelines on Diplomatic, Official and Social Manners. Lawrence Olufemi Obisakin. ISBN 978-978-029-807-4.
 • Shittu, Sheriff (2018-03-09). "Jos monarch asks President Buhari to revisit state police". TODAY. Retrieved 2020-11-09.
 • "Plateau monarch: Governors don't have authority to redefine traditional boundaries". TheCable. 2019-05-18. Retrieved 2020-11-09.
 • "Gbong Gwom Jos tasks traditional rulers on cultism, drug abuse". The Sun Nigeria. 2018-05-15. Retrieved 2020-11-09.
 • "Gbong Gwon Jos kicks as Lalong moves to reduce his influence". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News. 2019-05-18. Retrieved 2020-11-09.
 • "Court restrains Lalong from demoting Gbong Gwom Jos". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News. 2019-05-25. Retrieved 2020-11-09.
 • "Jacob Buba Gyang And His Stalkers". www.gamji.com. Retrieved 2020-11-09.
 • Obisakin, Lawrence Olufemi (2007). Protocol for Life: Guidelines on Diplomatic, Official and Social Manners. Spectrum. ISBN 9789780298074.