Jami'ar Leipzig

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jami'ar Leipzig

Aus Tradition Grenzen überschreiten
Bayanai
Suna a hukumance
Universität Leipzig – Alma Mater Lipsiensis da Karl-Marx-Universität Leipzig
Iri public university (en) Fassara, open-access publisher (en) Fassara, comprehensive university (en) Fassara da university of applied sciences (en) Fassara
Ƙasa Jamus
Aiki
Mamba na Utrecht Network (en) Fassara, Verein zur Förderung eines Deutschen Forschungsnetzes (en) Fassara, German Rectors' Conference (en) Fassara, German University Sports Federation (en) Fassara, European University Association (en) Fassara, Informationsdienst Wissenschaft (en) Fassara, Franco-German University (en) Fassara, German National Research Data Infrastructure (NFDI) e.V. (en) Fassara da ORCID
Bangare na ELIXIR Germany (en) Fassara
Ƙaramar kamfani na
Ma'aikata 5,300 (2018)
Harshen amfani Jamusanci
Adadin ɗalibai 31,088 (2020)
Mulki
Rector (en) Fassara Eva Inés Obergfell (en) Fassara
Hedkwata Leipzig
Subdivisions
Mamallaki na
DBpedia (en) Fassara
Tarihi
Ƙirƙira 2 Disamba 1409
Wanda ya samar

uni-leipzig.de


Jami’ar Leipzig tana cikin garin Leipzig a gabacin Jamus a jihar Sachsen. Sunan latin Alma Mater Lipsiensis ne.

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

An kafa jami’ar Leipzig a shekara 1409. Tana daya daga tsaffofin jami’o’i a Turai, da kuma na biyu mafi tsufa a Jamus. Jami’ar ta yi aiki ba tare da katsewa ba. Frederick I, mai mulkin Sachsen da dan uwarsa William II, sun kafa jami’ar a ranar 2 ga Disemba 1409. Tun da kafuwarta, Jami’ar Leipzig ta gudanar da bincike da koyawa ba tare da katsewa ba fiye da shekaru 600. Har ila yau, jami’a ta kasance daya daga cikin jami’o’in Jamus na farko inda mata suke iya shiga jami’a a matsayin baƙi da kuma suke halartar laccoci. A cikin 1873 ƴar Rasha Anna Yevreinova ita ce mace na farko a Jamus don samun digiri a nazarin shari’a daga Jami’ar Leipzig. Duk da haka, Jami’ar Leipzig kuma ta fuskanci lokuta masu wahala. Yaƙin Duniya na biyu ya halaka birnin da jami’a da yawa. Ya lalata manyan sassan jami’ar, amma an ci gaba da karatu. An ce a karshen yaƙin kashi 60 na gineginen jami’o’i da kashi 70 na litattafai da dakunan karatu sun lalace. A cikin lokacin yaƙin duniya na biyu akwai Yahudawa da yawa waɗanda suke yi aiki a jami'ar Leipzig, suke rasa digirinsu jami'ar. Dalilin shi ne wariyan gurguzu na ƙasar Jamus (wato nazism) ga Yahudawa. A cikin shekaru 75 Jamus da birnin Leipzig suka canza gaba ɗaya. Yau, jami'ar Leipzig tana da wuri mai haƙuri da kuma tana ƙaddamad da daidaito tsakanin maza da mata cikin jami'ar. Jami'ar Leipzig tana kula da haɗin gwiwa tare da yawancin sauran jami'o'i a duk duniya kamar Brazil, Asturaliya, Japan, Afirka ta Kudu da Tanzaniya.

Ilimi da bincike[gyara sashe | gyara masomin]

Yau, Jami’ar Leipzig tana da gine-gine, dakunan karatu, kantuna da yawa a cikin birni. Halin yanzu dalibai kusan 31.000 suna karatu da malamai 465 a sashen jami’a guda 14. Akwai batutuwa na karatu 158 kamar nazarin Afirka, likitan hakora da karatun ilimi. Jami'ar tana da lambun tsirrai mafi dadewar a Jamus, da kuma gidajen tarihi uku da kungiyar makaɗa na jami’a. Jami’ar Leipzig tana da shahararsa da tana jan hankalin ɗalibai da yawa a cikin ƙasa, na Turai da na duniya.

Asibitin jami'a (Universitätsklinikum) ita ce babbar asibitin Leipzig kuma shi ne muhimmin bangaren jami'a. Yana da kusan ma'aikata 6000 da fiye da marasa lafiya 400.000 kowace shekara. Ɗalibai na likitanci, likitan hakora, ilimin harhada magunguna da, tun 2022, dalibin ungozoma su ne ake horar da su.

20 masanin wanɗanda suka lashe kyautar nobel suka da alaƙa da jami'a da kuma wasu mashahuran Jamusawa sun yi karatu a jami’a kamar Johann Wolfgang von Goethe, Erich Kästner da Richard Wagner da kuma tsohon shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel.

Lauya Eva Ines Obergfell tana shugaban jami’ar Leipzig tun da Afrilu 1 2022.