Johnny Hallyday

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Johnny Hallyday a shekara 2014.

Johnny Hallyday (lafazi : [joni alidai] ; an haife shi a birnin Paris, Faransa, a ranar 15 ga watan Yuni 1943 - ya mutu a Marnes-la-Coquette, Faransa, a ranar 6 ga watan Disamba 2017) mawaƙin Faransa ne.

Shi ne ɗaya daga cikin shahararrun Faransa mawaƙa a karni na ashirin. Ya shirya waƙa kamar L'Idole des jeunes (Gumkin matasa, 1962), Noir c'est noir (Baƙi baƙi ne, 1966), Que je t'aime (Ina sonki sosai, 1969), Requiem pour un fou (Requiem domin mahaukaci, 1976) na Ma gueule (Fuskana, 1980).